Asusun TSA Ya Ba Gwamnati Damar Tsimin Naira Biliyan 45 Duk Wata – AGF

Gwamnatin Tarayya ta samu sama da tiriliyan 10 bayan aiwatar da asusun bai-daya (TSA) da ta amince da shi daga rukunin Manya da kananan Ma’aikatunta da kuma sauran Hukumomin da ke karkashin ikonta da yawansu ya kai guda 1,674.

Wannan sanarwa ta fito ne kai tsaye daga Ofishin Babban Akanta Janar na Tarayyar Nijeriya, a jiya Alhamis bayan tantancewa tare da sake duba kafatanin Ma’aikatun Gwamnati tare da manya da kuma kananan Hukumomin Gwamnati a wannan shekara ta 2019 ga Shugaban Ma’aikatan Tarayyar Nijeriya baki daya.   

A yayin gabatar da wannan kudiri, Ofishin Akanta Janar na Kasar ya bayyana cewa, a karkashin wannan asusu na bai-daya (TSA), Gwamnati na samun damar tsimin sama da Naira bilyan 45 a duk watan duniya tun kafin ma a fara yin amfani da tsarin asusun bai-dayan yadda ya kamata.    

Haka nan, Ofishin ya sake bayyana cewa, harajin Naira bilyan 50 da ake samu daga cikin kudaden da ake fitarwa sun daina shiga kai tsaye sauran bankuna saboda aiwatar da asusun bai-dayan da Gwamnatin Tarayya ta yi.

Sannan akwai wadansu ci gaban da dama da aka samu sakamakon bijiro da asusun TSA da Gwamnatin Tarayya ta yi da ya hada da: daina ta’ammali da kudi a hannu ta hanyar cinikayya  da Gwamnati, damar sanin dukkanin wani shiga ko fitar kudi da ya shafi Gwamnati, rage yawan asusun ajiya da wasu Ma’aikatun Gwamnati ke da su, karin samun kudaden shiga ta hanyar bankuna ba hannu da hannu ba, karin sanya idanu ga Gwamnati a kan harkokin da suka shafi kudi, rage yawan shige da fice na kudi sannan yanzu asusun TSA ya fara gudana yadda ya kamata har a kan kudaden waje da ake amfani da su a baya ga na gida.

Har ila yau, Ofishin ya bayyyana cewa, “kamar yadda labari ya iske su, an aiwatar da kasafin kudin shekarar 2017 da kaso 67 cikin 100”, kamar yadda majiyar ta bayyana.

Exit mobile version