Abdulazeez Kabir Muhammad" />

ASUU Reshen Jami’ar Jihar Taraba Ta Janye Yajin Aiki Bayan Wata Biyu

Kungiyar malaman jami’o’i (ASUU) reshen jihar Taraba ta janye yajin aikin da ta kwashe watanni biyu tana yi bayan cimma yarjejeniya tsakanin kungiyar da gwamnatin jihar.

Dr Samuel Shikaa, shugaban ASUU reshen jihar, ne ya bayyana hakan bayan sun kammala tattaunawa da kungiyar a Jalingo ranar Juma’a.

Shugaban ASUU ya kara da cewa gwamnatin jihar ta fara gudanar da wani sashe daga cikin yarjejeniyar da muka yi.

Kungiyar ta yi kira ga yayanta cewa su dawo bakin aiki cikin gaggawa sannan tayi kira ga daliban makarantar su dawo makaranta don soma karbar darasi.

Shikaa ya na fatan gwamnatin ta gabatar da dukkan yarjejeniyar da suka yi don tabbatar da cewa ba’a sake samu wani dalilin da zai sa a taba jadawalin makarantar ba nan gaba. Idan ba’a manta ba ASUU reshen jihar sun tsunduma yajin aiki ranar 3ga watan Afrilu sakamakon rashin biya musu wasu bukatun su

Exit mobile version