Kungiyar Malaman jami’o’i ta kasa (ASUU) reshen Jami’ar Nsukka (UNN) ta yi barazanar maka hukumar shirya jarabawar shiga makarantun gaba da sakandire ta Kasa (JAMB) a gaban kotu saboda mummunar faduwar da Dalibai suka yi a a jarabawar shiga jami’a (UTME) ta shekarar 2025.
Shugaban kungiyar ASUU-UNN, Kwamared Óyibo Eze ne ya bayyana haka a lokacin da yake zantawa da manema labarai a garin Nsukka na jihar Enugu a ranar Laraba.
- Tinubu Ya Yaba Wa Sule Lamiɗo A Taron Ƙaddamar Da Littafin Tarihin Rayuwasa
- Yadda Kasar Sin Ke Kokarin Gina Tashar Bincike A Sama Da Tubalin Kasar Duniyar Wata
Oyibo ya ce, shiyyar da tafi samun mummunan sakamakon jarabawar itace Kudu-maso-Gabas. Lallai wannan zagon kasa ne da JAMB ta shirya da gangan na hana yaran shiyyar shiga manyan makarantu.
“Ofishina ya cika da tarin jama’a suna ta kiraye-kiraye kan wannan mummunan sakamakon da aka samu a jarabawar JAMB ta 2025.
“ASUU za ta kalubalanci wannan sakamakon a gaban babbar kotu idan JAMB ta gaza sake duba sakamakon da kuma bai wa dalibai makin da suka cancanta.” In ji shi
Ya yi kira ga gwamnonin jihohin Kudu-maso-Gabas da su tashi su kalubalanci abin da ya kira da rashin adalci domin hana dalibai daga shiyyar samun shiga manyan makarantu a kasar nan.
LEADERSHIP ta ruwaito cewa, shugaban JAMB, Farfesa Ishaq Oloyede, a ranar Laraba ya bayyana shirin sake gudanar da jarabawar ga dalibai da suka fito daga jihohin Kudu maso Gabas da Legas.