Atiku Ba Asalin Dan Nijeriya Ba Ne, Dan Kamaru Ne –APC Ga Kotun Zabe

Jam’iyyar APC mai mulki ta bayyanawa kotun sauraron kararrakin zaben Shugaban Kasa, da ke zama a birnin tarayya Abuja, cewar dan takarar shugabancin kasa a karkashin inuwar jam’iyyar PDP, kuma tsohon mataimakin Shugaban Kasa, Alhaji Atiku Abubakar ba asalin dan Nijeriya bane.

Saboda haka jam’iyyar APC ta ce bai ma halarta Atikun ya tsaya neman takarar shugabancin kasa ba kwata-kwata.

APC ta yi ikirarin cewa Atiku dan asalin kasar Kamaru ne, ba kamar yadda aka dauka dan Nijeriya bane, a cewar jam’iyyar APC sam bai ma kamata a saurarin koken da ya shigarwa kotun ba, tunda shi ba dan kasa bane.

Wannan shine amsar da APC mai mulki ta bayar ga kokarin Atiku da jam’iyyar PDP na shigar da korafin zabe a gaban kotun kararrakin zaben, sannan APC ta bukaci kotu ta ayyana kuri’a miliyan 11.1 da Atiku ya samu a matsayin aikin banza.

APC ta ce an haifi Atikun ne a ranar 25 ga watan Nuwamban shekarar 1946, a garin Jada dake Adamawa arewacin Jamhuriyar Kamaru, don haka shi ba cikakken dan Nijeriya bane ma.

Exit mobile version