Atiku Ne Ya Fi Cancanta Ya Zama Angon Nijeriya A 2019

Allah kada ya kawo ranar yabo; haka Bahaushe ya ce. Hakika mu ’yan Nigeria yau ido bude mu ke nema da rokon Wazirin Adamawa Alhaji Atiku Abubakar da ya amsa kira ya tsaya takarar shugabancin kasar Nan a Shekara ta 2019 a karkashin Jamiyyar PDP bisa tabbacin da mu ke da shi shine kawai mafita a Nigeria Muna ta Kira da babbar murya da ka fito ka amsa kiranmu ka zama Dan takarar shugaban kasarmu saboda kyawawan halayensa da iya mu’amala da taimako da kishin kasa.

Kowa ya na da shaidar da ya ke bayarwa ta Alhaji Atiku Abubakar mutum ne Mai hakuri, hadari ne in har yasa gabansa gabas na Alkhairi baya juyawa. Wasu  sukace kishinsa da addinin Musulunci da San zama lafiya da kishin arewa shine jigonmu na rokonsa da ya fito. kasancewar shi haifaffen Kano ne, ya taso da tarbiyya da Jin Kai,Kuma da tausayi da rikon Amana irin na kanawa da dogaro da kansa,a kananan shekarunsa saida ya mallakawa kakarsa gida sukutum da Jin kai da zafin Nema. Mutum ne da take Jin korafin jama’a a duk inda suka tareshi ba hantara baya guduwa ya bar kasarsa  Sabanin manyanmu saidai suyi masanaantarsu akasashen ketare kada Yan asalin kasarsu su amfana . Duba da Alhaji Atiku Abubakar Wanda duk wata harkarsa ta kasuwanci a kasarsa Yake Dan Yan kasarsa su amfana ,Kuma ya rage Zaman banza. A kaf fadin Nigeria Bayan Alhaji Aliko Dangote babu Wanda Yake Samar da aikin yi sama da wazirin Adamawa.

Kadan daga cikin abinda Yan Nigeria suke amfana da shi na masana’antar ruwa da ya bude wato faro. wato a kalla wadanda suke cin abinci masana’antar ba zasu lissafu fa ,ga Kuma property debelopment company,Intels, ga Kuma noma Wanda Yake sawa ake masa kuma ya bawa mabukata abinda Yake nomawa Yafi hekta 2500. Wannan duk Muna Jin labari Kuma Muna gani bamu Kara tabbatar da Haka ba da gamsuwa saida mace Mai kamar maza Mai son talakawa wacce kwamishiniya tayi na Dan wani lokaci ta kawo cigaban da ba a taba kawowa ba a jihar Kano wajen tallafin noma,samarwa da Matasa aikin yi, taimakon gina makarantu na islamiyya, samarwa da Mata Abinyi, har ake Mata kirari da garkuwar matan Nigeria da wayarwa da Matasa Kai a wajen Neman na Kai wato Sanata Dr baraka Umar( senator baraka) tsohuwar kwamishiniya ta noma. mun santa,mun San halinta da kishinta a Kan kasarmu mun san tana son ta ga Nigeria ta fi Haka, da muka ganta a tafiyar mun San kyakkyawan zaton da mukewa wazirin Adamawa ya wuce haka Tunda muka ga itama  tana cikin tafiyar sosai. Sannan Kuma kawo maganar Karatu Wanda har makarantu yake da su Dan ilimantar da Yan Nigeria a Basu ilimi ingantacce shiyasa a jami’ar Nigeria babu kamar ta sa Wanda duk malamai Yan Nigeria suke koyarwa Kuma Yana bada gurbin Karatu kyauta ga maraya, ga Wanda  bai da Hali ko Kuma Wanda ya Zama haziki . Nigeria Muna cikin wani yanayi marar misaltuwa inda muke kuka wiwi har wani baya iya rarrashin wani saboda halin da muka tsinci kanmu Wanda bangarori mafi tsada a gun kowanne Dan Adam Mika rasasu.    muhimman bangaren da ayau muke Dora hannu a ka ,shine ilimi duk Wanda ya Kwana ya tashi a Nigeria yasan ilimin Yan kasar Yana Kara tabarbarewa ga harkar lafiya,tsaro, duk wani Jin dadi da ya kamata Dan Nigeria ya huta an gaza Samar Masa da Haka shine muke rokon Dr sanata baraka Umar da ta ja jama’ arta na fadin Nigeria zuwa ga wazirin Adamawa Alhaji Atiku Abubakar da Ya amsa  kiranmu, ya fito takarar shugaban kasa ,ko ma Zama yantattu mu fita daga halin bauta da fargaba da yunwar da muke ciki  mu Yan Nigeria dan min gwada da yawa amma da sun hau kujerar Sai su manta da mu ,mun gaji da tura mota tana bade mu da hayaki . Shiyasa muka hada Kai muke da tabbacin Alhaji  Atiku Abubakar shine amsar Nigeria.

 

Munzir, shugaban kungiyar Nigeria Ina Mafita, ya rubuto ne daga Kano

 

Exit mobile version