‘Atiku Ne Zai Warware Matsalolin Tsaro A Nijeriya’

An bayyana a cikin ‘yan takarar da suka fito, domin neman shugabancin Nijeriya a zaben shekara ta 2019 da cewar babu wanda zai iya kawo karshen wadannan matsaloli, sai Wazirin Adamawa Alhaji Atiku Abubakar, in har ya sami nasarar a zaben shekara ta 2019.
Shugabar mata a tawagar yakin neman zaben Atiku Abubakar a karamar hukumar Zariya a jihar Kaduna, Hajiya Aisha Musa Gwargwaje ta bayyana haka ga wakilinmu, bayan ta kammala wani taro da mata a Zariya, kan yakin neman zaben Wazirin Adamawa a zaben shekara ta 2019, kamar yadda hukumar zabe mai zaman kanta a Nijeriya ta tsara.
Hajiya Aisha Musa ta ci gaba da cewar, duk wanda ya san halin da kasar nan ke ciki, musamman wasu jihohi, kamar arewa ma so yamma da kuma jihar Zamfara, daga lokacin da jam’iyyar A P C ta karbi mulkin kasar nan daga jam’iyyar P D P, sai jefa al’ummar wadannan jihohi cikin matsaloli daban – daban da suka shafi rasa rayuka dare da kuma rana.
‘Yar siyasar ta bayar da misali da jihar Zamfara, inda ta ce, babu wani dan asalin jihar da kuma mazaunin da ke yin walwala ko kuma barci da ido biyu ako wane lokaci.
Hajiya Aisha Gwargwaje ta kara da cewar, ko da a lokacin da Muhammadu Buhari yah au mulkin kasar nan, babu abin da bai fadi ba kan zargin jam’iyyar P D P kana bin da ya shafi tsaro da tsadar man fetur da kuma tsadar abinci, amma a yau,kamar yadda ta ce, duk abubuwan da ya bayyana, babu inda aka sami sauki, sai ma ci gaba mara ma’ana aka samu a matsalolin da ya ambata zuwa yau.
A tsaokacin da Hajiya Aisha ta yi kan yaki da cin hanci da karbar rashwa, ta ce, duk ‘yan Nijeriya sun fahimci yaki da cin hanci da rashawa da gwamnatin A P C ke yi, na damke wadanda ba A P C suke ba da kuma rufe ido ga ‘yan jam’iyyar A P C da aka same su da aikata cin hanci ko kuma karban rashawa.
A dai zantawar da wakilinmu ya yi da Hajiya Aisha Musa, ta nuna matukar damuwar ta yadda ke yi wa al’umma kisar kiyashi a garuruwa da dama a jihar Zamfara, amma banu wasu matakai na gamsuwa da gwamnatin tarayya ta yi, sai dai a kullun a furta cewar an sami nasara ga ma su hallaka al’umma ko kuma ma su garkuwa da jama’a, domin neman kudi.
Domin ganin wadannan matsaloli sun kawo karshe, Hajiya Aisha Musa Gwargwaje, ta yi kira ga al’ummar Nijeriya, da su cire siyasa a zukatansu, su zabi Alhaji Atiku Abubakar, Wazirin Adamawa, a matsayin shugaban kasa a zaben wannan shekarar ta 2019.

Exit mobile version