Bello Hamza" />

Atiku Ya Lashe Jihar Inugu

Jami’iyyar PDP ta lashe zaben shugaban kasa da aka gudanar ranar 23 ga watan Fabrairu 2019. Jam’iyyar ta PDP ta samu kuri’a 355, 553 inda ta kayar da abokiyar takararta na Jam’iyyar APC wadda ta samu kuri’a 54423.

Da yake sanar da sakamakon zaben jiya a babban ofishin INEC dake garin Inugu, jami’i mai tattara sakamakon zaben na zaben shugaban kasa da aka gudunar 2019,  Farfesa Joseph Ahaneku ya ce, an tattara sakamakin zabe da suka fito daga kananan hukumomi 17 a garin Inugu ya kuma gode wa dukkan wadanda suka taimaka wajen samun nasara aikin.

Ya bayyana cewa, an jefa kuri’a 451063 yayin da kuri’a 30049 suka lalace.

A matakin Sanata, mataumakin shugaban majalisar dattijai Sanata Ike Ekweremadu, na jam’iyyar PDP ya samu gaggarumin nasara a mazabar Inugu ta Yamma.

Shugaban tattara sakamakon, Farfesa Douglas Nwabueze, wanda ya bayyana sakamakom ya kuma kara da cewa, Sanatan ya samu kuri’a 86,088 inda ya kayar da dan takara na kusa da shi, Misis Juliet Ibekaku-Nwagwu, na jami’iyyar APC.

A martaninsa, Ekweremadu, ya mika godiyarsa ga al’umar mazabarsa a zabarsa da suka sake zabarsa a karo na biyar zuwa majalsar dattijai.

“Ina daukan wannna cin zaben da matukar mahimmanci, don kuwa wannan shi ne karo na farko a tarihin Nijeriya da wani zai ci zabe zuwa majalisar dattijai har karo na biyar, hakan bai taba faruwa ba kuma ina daukan wannan da matukar mahimmanci kwarai da gaske, ina kuma mika godiya ta ga Allah madaukakin sarki da ya bani wannan ni’imar.

“Dole kuma in godewa abokai na da dukkan al’ummar jihar Inugu, lallai su nuna cewa, al’umma ne da suke a wayewa, wannan duk da cewa, ni wani karamin yaro ne daga kauyen Mpu amma suka bani wannnan daman, ina kuma godiya gare su musamman mutane mazaba ta ta yammancin Inugu.

“Idan za ku iya tunawa, mun shiga dambarwar siyasa a shekarar da ta wuce, a bin ya yi kamari a shekarar 2018 ta yadda babu wanda ya yi tunanin za  a samu wata rana kamar wannna, ranar da za a sanar da lashe zabe na da gaggarumin rinjiyaye, llai Allah ne kawai zai iya tabbatar da irin wannan nasarar.

A mazabar Inugu ta gabas kuma, ChimarokeNnamani na jam’iyyar PDP ya lashe zaben kujerar Sanata.

Sanata Nnamani ya samu kuri’u 128,843 in da samu nasara a kan Prince Lawrence Ozoemena Eze na jam’iyyar APC.

Farfesa Aloysius Okorie jami’i mai sanar da sakamakon zaben ya sanar da sakamakon.

Exit mobile version