Daga Khalid Idris Doya,
Tsohon mataimakin shugaban kasa Atiku Abubakar ya nuna matukar kaduwarsa bisa mutuwar shugaban kungiyar dattawan Niger Delta wato ‘Pan Niger Delta Elders Forum’ (PANDEF), Air Commodore Idongesit Nkanga (mai ritaya).
Atiku a sakon ta’aziyyarsa da ya fitar na rashin Nkanga ya misaltasa a matsayin dan kishin kasa, mai hangen nesa wajen gudanar da lamura kuma fitaccen dan siyasa mai nagarta da ba za a iya mancewa da shi ba.
A cewar Atiku, “Marigayi Idongesit Nkanga ya himmatu sosai wajen hada kan jama’a, inganta zaman lafiya da cigaban shiyyar Niger Delta.
“Shi din ya kasance dattajo, mai cikakken tunani da amfani da tunaninsa, shugaba mai rikon gaskiya da amana, wanda kuma ya kasance shugaba mai kishin kasa,” inji Wazirin Adamawa.
Tsohon mataimakin shugaban kasar ya yi addu’ar fatan Allah albarkaci iyalan mamacin, kana ya basu hakurin rashi, ya kuma mika ta’aziyyarsa ga iyalan mamacin, gwamnati da al’ummar jihar Akwa Ibom da yankin Niger Delta bisa wannan babban rashin da suka yi.