Ranar Asabar kungiyar kwallon kafa ta Atletico Madrid ta koma mataki ta daya a kan teburin La Liga, bayan da ta doke kungiyar kwallon kafa ta Real Balladolid da ci 2-0 a karawar mako na 11 a gidanta.
Atletico Madrid ta ci kwallayen biyu ta hannun Thomas Lemar da kuma Marcos Llorente a karawar da ta yi a gida a karshen mako kuma da wannan nasarar Atletico Madrid ta ci wasan La Liga na shida a jere da hakan ya sa ta hau kan teburin gasar bana da maki 26, bayan wasanni 10 da ta yi hakan kuma ya sa kungiyar ta garin Madrid ta bai wa Real Sociedad tazarar maki biyu wadda take ta biyu a teburi, bayan wasa 11 da ta kara a La Liga
Ga jerin wasanni bakwai da Atletco Madrid ta yi nasara a jere a La Liga da kuma na Champions League da ta buga:
Asabar 24 ga watan Oktoba La Liga
Asabar 31 ga watan Oktoba La Liga
Osasuna 1 – 3 Atl Madrid
Asabar 7 ga watan Nuwamba La Liga
Atl Madrid 4 – 0 Cadiz
Asabar 21 ga watan Nuwamba La Liga
Atl Madrid 1 – 0 Barcelona
Asabar 28 ga watan Nuwamba La Liga
Asabar 5 ga watan Disamba La Liga
Atl Madrid 2 – 0 Balladolid
Wasannin Champions League da Atletico ta buga a bana:
Talata 3 ga watan Oktoba Champions League
Lok. Moscow 1 – 1 Atl Madrid
Taalata 27 ga watan Oktoba Champions League
Atl Madrid 3 – 2 RB Salzburg
Laraba 25 ga watan Nuwamba Champions League
Atl Madrid 0 – 0 Lok. Moscow
Talata 1 ga watan Disamba hampions League
Atl Madrid 1 – 1 B Munich