Watakila kungiyar kwallon kafa ta Atletico Madrid ta gabatar da sabon dan was anta, Diego Costa a gaban yan kallonta a wasan da kungiyar za ta fafata ta Chelsea a ranar laraba a wasan da zasu fafata na rukuni-rukuni a gasar zakarun turai.
Costa, dan shekara 32 ya koma tsohuwar kungiyarsa ne ta A.madrid a satin da ya gabata bayan kungiyoyin biyu suka amince da cinikin akan kudi kusan fam miliyan 52.
Duk da cewa dan wasan bazai fara wasa a kungiyar ba har sai a watan janairu sakamakon dakatarwar da akayiwa kungiyar na hanata siyan sababbin yan wasa bayan an kamata da siyan yan was aba bisa ka’ida ba.
Kungiyar Atletico Madrid dai ta yi niyyar gabatar da dan wasanne a gaban magoya bayanta domin ta farantawa yan wasan a sabon filin wasan kungiyar data fara wasa a ciki a wannan kakar mai suna Wanda Metropolitano dake garin na Madrid.
Costa dai ya koma Chelsea ne a shekarar 2014 inda yazura kwallaye 52 cikin wasanni 120 kuma ya taimakawa kungiyar ta lashe gasar firimiya sau biyu cikin shekaru uku.