Daga Rabiu Ali Indabawa,
Babban Hafsan Sojin Kasa (COAS), Manjo Janar Ibrahim Attahiru, ya bayar da wa’adin awanni 48 ga sojojin ‘Operation Lafiya Dole’ don kwato Marte daga ‘yan ta’addar Boko Haram da kuma kawar da sauran kauyukan da ke kusa da su, da suka hada da Kirenowa, kirta, Wulgo, Chikingudo al’ummomin kananan hukumomin Marte da Ngala a jihar Borno.
Attahiru ya bayar da wannan umarnin ne a ranar Lahadi yayin da yake yi wa sojojin na Super Army 9, Dikwa jawabi. Ya ba sojojin tabbacin goyon bayan da ake bukata don gudanar da aikin, wanda ya ce dole ne a yi shi cikin awanni 48. “Wajibi ne a kwato Marte, Chikingudu, Wulgo Kirenowa da Kirta a cikin awanni 48 masu zuwa. Ya kamata ku kasance da tabbacin duk goyon bayan da kuke bukata a cikin wannan aiki mai wahala.
“Yanzu haka na zanta da kwamandan gidan wasu sansanoni, da kuma babban jami’in dake ba da umurni ga runduna ta 7, ba za ku bari wannan al’ummar ta fadi warwas ba. Koma ka yi abin da ake bukata kuma zan kasance a bayanka,” inji Attahiru.