Attajiri Arthur Eze Zai Zuba Jari A Kano

A kokarinsa na ciyar da Jihar Kano gaba tare da cigaba da habaka tattalin arzikinta, Gwamnan Jihar Kano, Dakta Abdullahi Umar Ganduje, ya ziyarci gidan hamshakin attajirin nan, Prince Arthur Eze, a ranar Alhamis din da ta gabata, domin gabatar masa da bukatarsa na neman ya zo ya zuba hannun jari a sabuwar kasauwar duniya da ake shirin budewa a Jihar Kano.

“Na zo wajenka ne, a madadin sauran al’ummar Jihar Kano, domin gabatar da bukatar da ake da ita; na zuwa wannan Jihar domin  zuba naka hannun jarin a sabuwar kasuwar duniya irin ta zamani wadda aka tsara ta daidai da yadda cigaban da duniya ke tafiya tare da samar da dukkanin abubuwan da ake bukata, musamman na tsaro,” a cewar Ganduje.

Eze, ya tabbatar wa da Gwamna Ganduje cewa, zai zo Kano domin zuba gagarumin jari a kasuwar, kasancewar Jihar Kano, Jiha ce da ta shahara ta fuskar zaman lafiya, musamman yadda ta samu Gwamna wanda ya bayyana shi da cewa, Dattijon arziki ne wanda ya damu da cigaban al’ummarsa.

Haka zalika, ya cigaba da bayyana cewa, tarihin shahararsa a harkokin kasuwanci, ba zai taba kammala ba, ba tare da ya ambaci Jihar Kano ba, “ina Kano lokacin mulkin Marigayi Gwamnan farar hula na farko, Alhaji Muhammadu Abubakar Rimi, ina cikin  wadanda muka jagoranci kafa Hukumar Gidan Talbijin na CTB.

“Don haka, zuwa Kano domin zuba jari daidai ya ke da a ce na koma gidana ne. Saboda haka zuba jarina zai zama na musamman, musamman idan na tuna zamana a Kano a wadancan shekaru da suka gabata, in ji Eze.

Haka zalika, ya kara da cewa, wani bangare na farkon shekaruna a harkokin kasuwanci, a Jihar Kano na tafiyar da su, a lokacin Unguwar Noman Salan (Noman’s Land) duk Daji ne. Kazalika, ina so na bayyana maka cewa, na zauna a Kano, sannan Mai Martaba Marigayi Sarkin Kano, Alhaji Ado Bayero, Abokina ne na gaske.

“Ko shakka babu, wannan ya tuna min kyakkyawan cigaban da kake kokarin samarwa wanda kuma ya zo a lokacin da ake bukatarsa, Musamman samar da karin Masarautu hudu masu daraja ta daya a Jihar ta Kano, don haka ina jinjina maka, ina kuma taya ka murna bisa wannan kyakkyawan cigaba da bijiro da shi, wannan abin a yaba maka ne kwarai da gaske”, a cewar Attajirin.

Kazalika, bayan taya Gwamna Ganduje murnar samar da karin Masarautun guda hudu ne kuma ya sake yaba masa, bisa nada guda cikin ‘ya’yan Marigayi Ado Bayero, a matsayin Sarkin Bichi, Sarki mai daraja ta daya, ko shakka babu wannnan babban cigaba ne, don kuwa hakan sai ya tuna  min mahaifinsa, wanda cikakken Dattijon ariziki ne, in ji shi.

Har ila yau, ya yi amfani da wannan dama wajen yin kira ga Sarkin na Bichi, wato dan

marigayi Sarki Ado Bayero,  da cewa ya dauka wannan wata kyauta ce daga Allah, sanna ya yi kokarin yin koyi da mahaifin nasa, musamman a bangaren kyawawan halaye.

Prince Arthur, ya ci gaba da cewa, “muna fatan Sarkin na Bichi ya zama koda yaushe mai hakuri da mutunta juna da kuma zama nagartaccen mutum kamar yadda mahaifinsa yake da kyakkyawan halaye. Haka nan, “Mai girma Gwamna, ina sake sanar da kai cewa, wannan kirkirar karin Masurautu, wata ingantacciyar hanya ce ta kara shigar da Sarakunan Gargajiya cikin harkokin Gwamnati kai tsaye.”

Da yake gabatar da nasa jawabin, Gwaman Ganduje, ya jinjinawa Eze tare da bayyana shi a matsayi guda cikin iyaye ga ‘Yan kabilar Ibo da ke fadin kasar nan, wanda yake yin abubuwa masu yawa domin inganta zaman lafiya da hadin kan kasa tsakanin kabilar ta Ibo da kuma sauran kabilun kasar nan baki daya.

“Na zo nan wurin ne, domin kara jinjina maka bisa abubuwan kirki da kake aiwatarwa na inganta alaka tsakanin al’umma Kano da kuma ‘Yan kabilar Ibo da ke zaune a Jihar Kano. Ina da tabbacin ka samu labarin kyakkyawan shirin da zai kara samar da ingantaccen hadin kai tsakanin al’ummarmu ta Hausa da kuma ‘Yan kabilar taku ta Ibo. Sannan muna kara jinjina maka bisa abubuwan alhairin da ake aiwatarwa”, in ji Gwamnan. Kamar yadda Babban Daraktan Yada Labaran Gwamna Gwamnan Kanon, Abba Anwar ya shaida wa Jaridar Leadership A Yau.

Exit mobile version