Attajiri Da Rocha: Ƙasar Ingila Kakana Yake Kai Wanki -Jikarsa

A wannan tattaunawar wadda wakilinmu BELLO HAMZA ya naƙalto mana hirar da ANGELICA OYEDIRAN tsohuwa ‘yar shekaru 89 da haihuwa, kuma jika a wurin shahararren attajirin nan Candido Da Rocha, wanda alƙalumma suka tafi akan cewa shi ne ɗan Nijeriya na farko da ya fara zama miloniya. jikar tasa ta yi cikakken bayani dangane da kakanta. Ga yadda hirar ta kasance:

Za mu so ki yi mana bayanin rayuwar ki da na iyayen ki.

An haife ni ne a ranar 1 ga watan Disamba na shekarar 1927, sunan mahaifi na Christopher Akinsola Thomas “Architect” a ƙaramar Hukumar Legas, iyayensa sun rasu tun yana da shekara 7 a duniya, wani abokin mahaifinshi mai suna Papa Ɓaughn ya ɗauki renonsa, a lokacin bai daɗe na yin aure ba kuma ba shi da ‘ya’ya, sai ya mayar da shi a matsayin ɗansa na farko, duk da daga baya ya samu na sa yaran, maza 3 mace 1, mahaifin nawa ya rasu shekara 50 da suka wuce, 27 ga watan Oktoba yana da shekara 71 a duniya. Candido Da Rocha bai goyi bayan auren iyayena ba, yana son dukka ‘ya’yansa su auri ‘yan ƙasar Birazil, dukkan su kuma ba su yadda da haka ba, ɗan farko na iyaye na ya rasu yana ɗan yaro, na biyu mai suna Cyril Akin Thomas ya yi karatu  CMS Grammer School, ya girma har ya zama “Architect” kamar mahaifin mu sai ya rasu yana da shekara 41 bayan ya yi aure har ya haihu, na uku mai suna Ademola Thomas Injinian ginegine ne, ya yi karatunsa a ƙasar Ingila bayan kammalawa ya zama Minista a zamanin mulkin Shehu Shagari ya rasu shekara 4 da suka wuce yana da shekara 86., ni ne a ka haifa bayan shi.

Ko akwai wani abin da ya banbanta ki da sauran ‘yan’uwanki?

Ni kaɗai mahaifiya tat a Haifa ba tare da wani taimako ba, a ranar, ita kaɗai ne a gida tana girka abinci, mahaifina ya tafi buga ƙwallon “Lawn Tenis” a Yourba Kulub, yayyina kuma na wajen kakanmu don taya shi hira, sai ta ji alamun naƙuda, nan da nan ta kamala abinci, ta shiya a kan tebur, ta shiga ɗaki ta haifeni ba tare da taimakon wani ba, haihuwa na ikon Allah, ta shaida mani cewa, ni ne kaɗai cikin ‘ya’yanta ya zo duniya da cikakken ƙoshin lafiya.

Yi mana bayanin karatunki da ayyukanki.

Na halarci Methodist Girls High School, in da na samu ilimin Nursery da Primary daga nan na wuce CMS Grammar School na kuma yi makarantar Baptist Academy, ina cikin ɗaliban farko na Ƙueen’s College, Lagos. Sai da ban samu nasarar cin jarabawar ƙarshe ba, a wancan lokacin in mutum ya faɗi darasin Ingilishi to ya faɗi komai, amma wani malamin mu mai suna Dakta Whittaker ya ba da shawarar in sake zana jarabawar amma kuma na sake faɗuwa. A shekara ta biyu ina shirin sake zana jarabawan a Ƙueens College sai ga Farfesa Oladele Ajose ɗan Sarkin Legas Ologun Kutere Ajose sun zo makarantanmu mu tare da matarsa Baturiya, suna neman wayenda za su yi aiki da su a ƙungiyar “Birtish Red Cross” da suka kafa a Nijeriya, bayan tantancewar da aka yi wa da yawa daga cikinmu, matan ta amince da ɗauka ta aikin Red Cross duk da faɗuwa jarabawa da na yi tan a mai mamakin yadda na faɗi darasin Ingilish.a shekarar 1951 sun tura ni ƙasar Ingila in da yi karatun gudanar da mulki (administratiɓe roles) daga dawowa na a ka tura ni aiki a Kudanci da Gabashi da Arewacin kasar nan, na yi aiki da su har tsawon shekara 15 kafin in yi aure.

Ta ya ya kika haɗu da mijin na ki?

Mijina dattijo ne, na aure shi bayan shekara 5 da rasuwar matarsa. Shi ne jakadan Nijeriya na farko a birnin Washington DC, a nan muka yi aure. Daga nan aka tura shi ƙasar Sierra Leone nan ma ya zama jakadan ƙasar nan na farko, a lokacin ni na shugabanci matan jakadun ƙasashen waje a ƙasar, na yi aiki tuƙuru domin ganin miji ya yi nasara a dukkan ayyukansa. Shekarar da ya wuce, lokacin da Sarauniyar Ingila (Ƙueen Elizabeth 11) ta yi bukin cika shekara 90 a kan karagar mulki na aika mata da wasika in da na tuna mata da ziyarar da ta kawo ƙasar Sierra Leone an gabatar da ni ga ita a lokacin cin abincin rana, sannan mijina ya yi rawa da ita ni kuma na yi rawa da mijinta Yarima Philip, ta aiko mani ta kati, tana godiya (a thank you card).

Me kika shiga yi bayan kin bar “Red Cross”

Bayan rasuwar mijina na yi aikin da gwamnatin Nijeriya ƙarƙashin jagorancin Janar Yakubu Gawan kafin nan na yi aiki da “Christian Council” a matsayin Jakadiya tsakanin Nijeriya da ƙasashen waje a lokacin yaƙin basasa. Ni ne na jagoranci kwamitin bayar da kayan jinƙai da tsugunar da jama’a, ni ke ƙarɓo taimako daga ƙasashen waje, haka kuma, ni ke shiga garuruwan da dojojin Nijeriya suka ƙwato lokacin yaƙi domin zaƙulo mutanen da ke buƙatar taimako. An samu taimako daga Majalisar Ɗinkin Duniya da ƙungiyoyi irin su “Gaeman Cartas” da Roman Cartas”, ƙarshen yaƙin ya same ni ne a gartin Asaba ta jihar Delta. Ni kuma na jagoranci kai yara 5,000 daga ɓangaren Biyafira zuwa ƙashen Côte d’iɓoire da na, ni kuma na sake jagorantar dawowa da waɗannan yaran zuwa iyayensu bayan ko mai ya lafa, Allah Ya kare lokacin yaƙin. Me nene ya fi ba ki tsoro a lokacin yaƙin?

So da yawa yaƙi kan rutsa da ni a waje cikin mota ta (Land Roɓer), akwai lokacin da muke jirgin saman yaƙi DC6 tare da shugaban sojojin sama Alao, babu ko “seat belt” ashe ‘yan Biyafira na sane cewa, shi ne a ciki, su ka yi ta harbin jirgin amma cikin ikon Allah ba su sami nasarar harbo mu ba, mun sauka Port Harcourt lafiya ƙalau a wannan ranar, bayan ‘yan kwanaki Alao ya fita rangadi cikin jigin aka harbo shi nan take ya mutu, Allah Ya kare a irin waɗannan tafiye-tafiye da dama.

Akwai kuma lokacin da wasu baƙi suka zo daga Legas sun haɗa da Archdeacon Kale da Marigayya Steɓe Rhodes da kuma Gloria Rose da nufin za su tamaka mani ba da agaji a garin Kalaba, muna cikin shirye-shirye sai jiki ya ba ni cewa wannan tafiyar babu alhairi, har shirya hawa jigi mai sai sauka ungulu sai na gaya ma abokoan tafiyar ta wa cewa, na fasa tafiyar, abin bai yi masu daɗi ba, suna takaincin cewa sun zo tun daga Legas amma na ƙi basu daman taimakawa. Jirgin bai daɗe da tashi bay a faɗo, “Pilot” ɗin ya samu rauni mai tsanani da sai da a ka kai shi ƙasar Canada domin yi mashi magani. Da na shiga jirgin nan wataƙila da na mutu amma Allah na so in yi fiye da shekara 90 a duniya.

Wane labari mai kaɗa zuciya za ki ƙara mana dangane da yaƙin basasan`?

An yi yunwa kwarai a lokacin yaƙin, ɓangren Biyafira da na Gwamnatin tarayya,yaƙin ya kuma tarwatsa iyalai da dama, akwai wani yaro da Marigayyi Birgedia Benjamin Adekunle (Black Scorpion) ya kawo asibiti a Legas, yaron ya rasa idanuwarsa a misayar wuta tsakanin sojojin gwannati da na ‘yan tawaye an kuma kasha iyayensa gaba ɗaya, ba wanda ya san ‘yanuwa, ni kuma na zo asibitin ne a yi mani aiki a ido na hagu, lamarin yaron ya bani tausayi matuƙa saboda haka, sai na ɗauke a matsayin ɗa, na sa shi makaratar makafi daga nan na kai shi makaranta kwana na King’s College Legas bayan ya gama ya wuce Jami’a Jos in da ya yi karatunLauya, yanzu kwararren lauya ne, ya yi aure har ‘ya’ya.

Ya dangartakar ki da Candido Da Racha, Miloniya na farko a Nijeriya?

Mahaifiyata ce ‘ya ta uku a waje kaka na, Papa Candido Da Rocha. Wato ni jikan sat a ta biyu ce, a na kiransa da  Da Rocha of Casa d’Agua – Water House, sunan mahifinsa Esan daga Idifi, Ilesa ta jihar Osun. A lokacin da ƙasar Birtaniya ke ma ƙasarmu mulkin mallaka, sun fito da tsarin kai yara garin Legas domin karatun book ta hannun Sarauniya Ɓictoria, tsarin ya tanadi shiga lungu-lungu domin zaƙulo yara, a irin haka ne Kaka ya samu shiga cikin yaran da suka je Legas karatu, tarihi ya nuna cewa ana yawan sace mutane domin sayar da su ga masu fataucin bayi a lokacin da suke zirga-zirga daga makaranta zuwa gida. Turanwa ƙasar Portuguese masu safara a gaɓar West Coast na Afrika tare da ‘yan kasuwa Ijebu suka fi shahara a wannan sana’ar. Esan na daga cikin waɗanda aka sace, duk da mace-macen da ake yi a hannun ɓarayin mutanen Allah ya kare shi har aka kawo shi Badagry daga nan aka wuce da su Brazil, Bahia, Salɓador, wani attajiri mai safarar yadiddika ya ɗauke shi aiki ya kuma canza masa suna zuwa  Da Rocha. Hankalin shi bai natsu a rayuwar cikin bauta ba, saboda haka sai ya haɗu da wasu ‘yan Nijeriya da ke cikin ƙangin bauta a na Brazil su ka kafa ƙungiya da suka yi ƙarfi sai suka tunkari gwamnan Brazil na wancan lokacin sun a neman a basu ‘yancinsu.

An ba su ‘yancin nasu kamar yadda suka buƙata?

Daga ƙarshe sun samu ‘yanci, sun kuma ɗauki wata 13 kafin su iso Nijeriya, Esan Da Rocha ya jagoranci sauran jama’ar da suka dawo zuwa wajen Wakilin Sarauniya Ɓictoria suna buƙatar matsuguni, sarauniya ta basu wuri a tsakanin “Central bank” da “Broad Street” har zuwa Kam Salem a yankin Obalende.

A nan ya gina “The Water House” a ɓangaren da aka ba shi, ya samu kaso biyu ne saboda ya dawo da matarsa ‘yar asalin ƙasar nan da ‘ya’uyansa uɗu biyu maza biyu mata, ya kuma samu wani kason a unguwar Tinubu. Gidan day a gina ya yi daidai da gidan da ya zauna a ƙasar Brazil.

In  da nake zaune ba Esan da Candido suka gina ba kuma bai zauna a wannan ɓangaren ba, ya rasu a shekarar 1959, an raba dukiyarsa tsakanin ‘ya’yansa Aleɗander da Louisa Ebun Turton da Angelica Folashade Thomas (mahaifiyata) da kuma Candida Adenike Afodu. Mahaifiya ta ce gaji wannan ɓangaren, lokacin da Esan ya yi gininsa shekara 152 da suka wuce ana wahalar tsaftatacen  ruwan sha a Legas to ya wani babban rijiya da yake sayar da ruwan, ya na kuma rabawa kyauta, dalilin haka ne ya sanya wa gidan suna “water house” Casa d’Agua a yaren Brazil.

Bayan rasuwarsa ya yi wasiyar a ba Candido da Josephina ‘ɗar autansa wannan gidan, wanda ya yi karatun magani a ƙasar Sukotilan. Kuma ɗan jarida ne, wanda suka zauna tare da Anti Joana har lokacin da suka mutu. Bayn mutuwar ta su sai aka miƙa kayan na su ga Candido da Josephina. Daga baya sai suka raba kayan inda Josephina ta sake samun wani kayan shi kuma Candido ya riƙe  wannan gidan a matsayin gadon da ya samu daga Esan.

Kin taɓa zuwa Barazil don ki ga inda kakanki ya taɓa yin bauta?

  1. Na taba zuwa a shekara ta 1983 kuma na ziyarci gidan da ya zauna a Tororo, da ke Salɓador. Na kuma je Brazil na ga sakatariyar da ya zauna tare da wasu ‘yan Nijeriya. A sakatariyar akwai rubuce-rubuce da yawa na yadda aka sato su daga Nijeriya har zuwan su Brazil da wuraren da su ka yi bauta, kakan nawa na da wasu yaran da wata mata ‘yar Indiya, ba ta biyo shi gida ba, Esan ya rasu tana da shekara 88 an birne shi a makarbartar Ikoyi a nan Legas. Ya yi suna a ƙasar nan wajen bada tallafin kuɗi ga jama’a ya kuma shahara a sana’ar tufafi da goro da kayan gwari da sauransu.

Ya girman arziƙin Kakan ki Da Rocha?

Candido Da Rocha na da alaƙa na ƙut da ƙut da ƙasar Birtaniya da sauran ƙasashen Turai suna matuƙar mutunta shi ƙwarai da gaske, baya son rashin gaskiya, na yi zama a wannan gidan na tsawon shekara 3 lokacin da mahaifiyata ke jinyarsa, yana so na sosai mun shaƙu da juna ƙwarai. A lokacin yaƙin duniya na 2 ya bai wa gwamnatin Birtaniya wani katafaren gini in da suka zaunar da ɗaliban King’s College, da farko an ajiye su ne a filin Polo.

Cikin abokansa na kut da kut a kwai Herbert Macaulay. Da Rocha ya ƙi shiga harkar siyasa, ko da wasu suka nemi ya tsaya takara an ta zuwa wajensa neman kuɗi amma abin da yake ce musu  shi ne “in kuna son Da Rocha to ku zaɓe ni amma in kuɗi na ku ke so to kar ku zaɓe ni”. Sau biyu lokacin da gwamnatin Birtaniya ta kama shi saboda harkokinsa na siyasa, Da Rocha ne ke biyan tarar, abin da ya hana Macaulay shiga gidan yari tun lokacin. Daga ƙarshe ya yi gargaɗin cewa, ba zai sake biyan kuɗin tara a kansa ba. Da Rocha ɗan ɗariƙar Katolika ne na gaske. Attajiri ne gaske, Miloniya ne tun a wancan lokacin, ya na kuma da kyauta da taimakon jama’a. Masu kuɗi a wanncan lokacin Ingila suke kai wanki da gugan kayansu, Da Rochas da Johnsons da Doherty da su Olowu su ne attajirai Miloniya a wancan lokacin, ba sa wankin kayansu a Nijeriya sai ƙasar Birtaniya, ya wancinsu na da riguna da wanduna da singileti da sauran su barkatai.

 

Exit mobile version