Aubameyang Ya Amince Da Albashin Da Arsenal Za Ta Bashi

Dortmund's Pierre-Emerick Aubameyang celebrates scoring the opening goal during the German Bundesliga soccer match between Borussia Dortmund and FC Schalke 04 in Dortmund, Germany, Saturday, Nov. 25, 2017. (AP Photo/Martin Meissner)

Rahotanni daga kasar Jamus ya bayyana cewa dan wasan kungiyar kwallon kafa ta Borussia Dortmund ya amince da albashin da kungiyar Arsenal za ta bashi idan har Arsenal din ta daidaita da Dortmund din.

Dan wasan, dan kasar Gabon yana samun matsala da kungiyar tasa inda a kwanakin baya kungiyar ta dakatar dashi bias nuna halin rashin da’a da yake yawan nunawa a kungiyar.

A kwanakin baya aka bayyana cewa dan wasan ya fara tattaunawa da wata kungiya a kasar China domin komawa kasar da buga wasa sai dai kungiyar ta Dormund tace baza ta rabu da dan wasan nata ba a wannan watan na Janairu.

Kungiyar kwallon kafa ta Arsenal dai tana zawarcin yan wasan da zasu maye mata gurbin Mesut Ozil da Aledis Sanches wadanda suke shirin barin kungiyar a wannan watan bayan sunki sake amincewa da sabon kwantaragin da kungiyar tayi musu tayi.

Kungiyar kwallon kafa ta Liberpool ma tana zawarcin dan wasan wanda take ganin zai maye mata gurbin Daniel Sturidge wanda shima zai bar kungiyar a karshen kakar da ake bugawa.

Arsenal tana mataki na 8 maki takwas tsakaninta da wadda take mataki na hudu sannan kuma bata buga gasar zakarun turai wanda hakan yasa yan wasan biyu suke ganin bazasu iya zaman kungiyar ba.

Duk da cewa Aubameyang yana fama da rashin tarbiyya amma Arsenal tana ganin za ta iya jure halayensa kuma tuni kungiyar ta shirya tunkarar Dortmund akan dan wasan.

 

Exit mobile version