Aubameyang Ya Koma Arsenal Domin A Duba Lafiyarsa

Aubameyang

Tawagar ‘yan wasan kasar Gabon ta bai wa kaftin din kasar, Pierre-Emerick Aubameyang izinin komawa kungiyarsa ta Arsenal daga gasar kofin Afirka a Kamaru, domin a duba koshin lafiyarsa kamar yadda hukumar kwallon kasar ta bayyana.

Mai shekara 32 a duniya, bai yi wa Gabon wasan da ta yi canjaras da Ghana ba ranar Juma’a, sakamakon kamuwa da cutar korona kuma Aubameyang ya kamu da annobar da saukarsa a Kamaru ranar 6 ga watan Janairu sai dai yanzu zai je likitoci su duba koshin lafiyarsa da zarar ya isa Arsenal.

Haka kuma Gabon ta umarci dan wasanta da ke buga wasa a Nice, Mario Lemina ya koma gida, sakamakon rashin koshin lafiya wanda hakan ba karamin nakasu tawagar tasu za ta samu ba. Aubameyang wanda ya kamu da annobar a cikin watan Agusta, bai buga wa Arsenal wasa ba, tun bayan da ta karbe mukamin kyaftin daga wajensa kan halin rashin da’a da ya yi sannan Gabon ta sanar da cewar an kara samun wasu ‘yan wasanta dauke da cutar Korona ranar Litinin din da ta wuce.

‘Yan kwallon sun hada da Denis Bouanga da Noubi Fotso da David Sambissa da Serge Ngouali da kuma Ulrick Eneme Ella da ba za su buga mata karawa da Morocco ranar Talata ba.

Exit mobile version