Aubameyang Zai Maye Gurbin Lukaku A Manchester United

Kungiyar kwallon kafa ta Manchester United ta bayyana sunan dan wasan gaba na Arsenal, Peirre Emeric-Aubameyang a matsayin wanda take fatan zai maye mata gurbin dan wasa Rumelu Lukaku wanda yake kokarin komawa Inter Milan.

Tun karshen kakar wasan data gabata dan wasa Lukaku ya bayyana cewa bazai cigaba da zaman Manchester United ba kuma kociyan kungiyar ya amince da bukatar dan wasan sai dai ya bayyana dan wasan gaban Arsenal, Aubameyamg, a matsayin wanda ya dace ya maye gurbin na Lukaku, mai shekara 26 a duniya.

Dan wasa Lukaku dai har yanzu bai bugawa Manchester United wasa ko daya ba a wasannin da kungiyar take bugawa na share fage domin fara kakar wasa ta gaba kuma kawo yanzu United din zata buga wasa na uku a yau da kungiyar Inter Milan, kungiyar da Lukakun yake son komawa.

Kamar yadda wasu rahotanni suka bayyana daga kasar Italiya, kungiyar kwallon kafa ta Inter Milan ta tattauna da Manchester United akan farashin dan wasan kuma ta shirya biyan kudi fam miliyan 70 domin ganin ta raba United da dan wasan.

Tuni dai Manchester United ta gama shirya taya dan wasan fam miliyan 62 idan har Lukaku yatafi kuma farashin ana ganin Arsenal zata hakura ta karba duba da halin da kungiyar take ciki na bukatar kudi domin sayan ‘yan wasa.

Wasu rahotanni daga birnin Landan kuma sun bayyana cewa shugabannin kungiyar Arsenal basa son sayar da dan wasan ga babbar abokiyar hamayyarsu kuma za suyi fatali da tayin dan wasan idan Manchester United din ta yi.

Exit mobile version