Auratayya

Tare da

Fauziyya D Sulaiman

A wannan karon za mu taɓo ɓangaran da ya fi komai muhimmaci ga rayuwar Ɗan’adam kowacce ƙabila ne shi ko wanne addini ya ke bi aure, musamman ta ɓangaran mace, domin duk cikar mace da kamalarta da kyanta da iliminta da nasabarta, idan ba ta sami auratayya mai kyau ba ta kan zamto abar tausayi, akwai wani Karin magana da hausawa ke faɗa, wato fini da gidan uba na fiki da gidan miji, wannan shi ne bayani a taƙaice akan muhaccin samun aure mai nagarta ga mace.

Sai dai akwai wasu matakai da ya kamata ace kowacce mace ta bi, domin zaɓar mutumin da zai zamto abokin rayuwarta kafin ta san abin da ya kamata ta yi akanta da kuma matsayinta na mace.

Matakakan sun haɗa da.

  1. Dole kafin ta faɗa soyayya ta kula da wanda za ta so, duk da akan ce soyayya tana shigar mutum ba tare da ya shirya ba, amma a wani lokacin ana ƙoƙarin kaucewa faɗawa kowacce irin soyayya ta hanyar tsare mutunci kai, girmama kai da kuma neman zaɓin Allah.
  2. Kar ta yadda ta yi soyayya domin kyau ko domin kuɗi, duk da mun san addini bai haramta aure domin waɗannan abubunwa ba, amma yin aure dominsu yana cikin abubunwa da ke taka rawa gurin yawaita mace-macen aure a wannan zamanin, ko kuma lalata za mantakewa a kasa jin daɗin zaman auran, don haka duk sanda za ta fara soyayya da wani ko ta amincewa auren sa ta tabbatar ta yi ƙoƙarin kaucewa wancan abubuwan na farko, sai dai samun su a mataki na biyu ko na uku ba zai zamto laifi ba. Misali ta samu nagartaccen mutumin da ta ke ƙauna saboda halayensa, sai kuma aka yi sa’a yana da kyau ko kuma yana da kuɗi, to sai ta godewa Allah.
  3. Ƙoƙarin kame kai ga barin kusanta kai ga juna. A wannan zamanin ‘yan mata suna ganin kamar idan suka fara soyayya da namiji idan ba su haɗa jiki da shi ba kamar ba su burge ba, musamman wanda su ke da wayewa da ilimin zamani, sai dai wannan shi ne babban kuskure da mata ke aikatawa a rayuwarsu, domin da zarar kin yadda kin fara haɗa jikinki da wanda ki ke fatan ya aure ki to tabbas abu ɗaya dole zai faru cikin biyu. Ko ya fasa auranki har abada domin ya sami abin da ya ke buƙata daga gareki, ko kuma ya aureki saboda Allah ya ƙaddara sai kun yi auran, amma zai dinga zarginki har abada cikin auranku, wani yakan furta ko ya nuna bayan auran, wani kuma ba zai furta ba sai dai za a yi ta samun saɓanin da za a kasa gane kansa, shi ne da an yi satika a auran sai a fara rigimar da za a kasa gane kanta, ko kuma miji ya fara ƙoƙarin neman ƙarin auren babu gaira babu dalili a kasa gane menene matsalar.
  4. Shire-shirye kafin aure. Akwai matsaloli da yawa da ake samu a wannan lokacin, wani daga ɓangaran ma’auratan, wasu daga ɓangaran iyaye da sukan nuna ƙaranta akan komai na auran, kama daga gurin kawo kayan al’adar aure da ake yi, ko gurin kama gidan zama ko wasu abubuwa da suka shafi auran. Sai dai wanda akan samu daga ɓangaran ma’auranta ya fi muni matuƙa. Akwai wani hoto da ake ɗauka kafin aure yanzu wanda ake kiransa da (free weeding pictures) wannan hoto yana cikin manyan masifun da ke bibiyar aure a yanzu, za ka ga mace ta kwanta a kirjin namiji, ko ta rungume shi ko sun haɗa baki ko hannu, ko ya ɗauketa, da sauran abubuwa munana. Babban abin mamakin kuma wani lokaci har iyaye sukan yi ƙoƙarin nuna wannan hotunan. Akwai wani aure da aka sami matsala ta dalilin wannan ɗaukar hoto, lokacin da ya rage sauran wata guda bikin, saurayin ya ɗauki budurwar a mota suka tafi ɗauƙar wannan hotunan, to irin yanda suka dinga haɗa jikinsu da yanda suka dinga maƙale juna yasa suka shiga wani hali, don haka daga nan gurin ɗaukar hoton suka wuce wani guri suka biya buƙatar zuciyarsu.

Daga nan kuma aka fara nuna hotunan ga duniya kowa ya gani ya san za su yi aure, sai dai cikin rashin saa mahaifin yarinyar ya faɗa rashin lafiyar da ya sa aka ɗaga bikin zuwa wani lokaci da har ya kai watanni uku, a cikin lokacin ciki ya bayyana a jikin amarya, hankalin mahaifiyarta da angon ya tashi matuƙa, domin su kaɗai suka sani, daga ƙarshe suka shiga suka fita har suka zubar da cikin babu wanda ya sani. Sai dai bayan wannan lokacin sai angon ya janye ƙafarsa, tun suna ganin abin kamar wasa har suka tabbatar da ya tafi kenan, daga ƙarshe sai ji suka yi an ɗaura masa aure da wata ƙawar yarinyar, ya barsu da kayan auransu, daga wannan lokacin yarinyar ta shiga matuƙar tashin hankali. To da an yi auran a wannan lokacin me ka ke tsammanin zai biyo bayan auran?

 

Exit mobile version