Ibrahim Muhammad" />

Aure Abu Ne Na Juriya Da Hakuri – Abdussamad Isyaka Rabiu

Abdussamad Isyaka Rabiu

An bayyana zamantakewa na aure da cewa muhimmin al’amari ne da yake bukatar kyautatawa, girmamawa da kuma hakuri da juriya.

Shugaban rukunin kamfanonin BUA, Alhaji Abdussamad Isyaka Rabiu ya yi wannan Jan hankali a yayin liyafa bayan daurin auren yarsa Maryam Rabiu Isyaka Rabiu da angonta Muhammad Abdurrahman Umar da aka yi a gidan marigayi Khalifah Sheik Isyaka Rabiu.

Daurin auren ya da aka yi karkashin jagorancin Khalifah Nafiu Isyaka Rabiu ya sami  halartar Gwamnan jihar Kano Dokta Abdullahi Umar Ganduje da takwararsa na Jigawa Badaru Abubakar da tsofaffin Gwamnonin Zamfara Sani Yarima Bakura dana Gwambe Dakwabo da tsohon Gwamnan Imo Rocha’s -Okorocha da wasu  daga Sanatoci da ‘yan majalisar wakilai da ‘yan kasuwa da Malaman addini da shugabanin ma’aikatun Gwamnati da masu zaman kansu da dinbin jama’a a ranar Asabar.

Shugaban na BUA ya yi fatan Allah ya zaunar da ma’auratan lafiya tare kuma da gode wa dinbin al’umma da suka halarci daurin auren da suka baron abinda suke suka karrama gidan khalifa daga ciki daga sassa daban-daban na ciki da wajen jihar Kano.

Shima a nasa bangaren daya daga cikin manyan malamai da suka halarci daurin auren Shugaban kungiyar Izala ta kasa Sheik Bala Lau ya ce zuwansa daurin auren ta jaddada zumunci ne da suka saba suna yi run lokacin marigayi Khalifah Isyaka Rabiu.

Sannan ya yi kira ga iyaye da ma’aurata akan su kiyaye dokokin Ubangiji a duk lokacinda za’a yi shagalin bukin aure kar ayi abinda ya sabawa koyarwar Annabi.

Sheik Bala Lau ya koka da yanda yawanci yanzu zakaga anyi daurin auren bisa koyarwa addinin musulunci amma abin takaici sai a ware gefe guda da sunan.biki ana kwaikwayon Yahudawa da nasara da maguzanci yin haka babban kuskure ne da yake dauke albarkar auren ya kuma kawo masifa a cikin al’umma.

Ya ce aure wata hikima ce ta Ubangiji da make haduwa a kulla zumunci na zuriya da make bukatar hakuri da juna da sauke hakkin juna dan.gink zuriya ta gari.

Cikin wadanda suka yi jawabai a wajen sun hada da tsohon kakakin majalisar wakilai Hon. Ghali Na’abba da dangi daga bangaren ango da amarya.

Shima a nasa bangaren mahaifin amarya wanda dan’uwane ga Shugaban BUA Abdussamad Isyaka Rabiu. Alhaji Rabiu Isyaka Rabiu da akafi sani da Alhaji Karami ya gode wa dukkan al’umma da suka zo don shaida wannan abin.alkhairi.

Exit mobile version