Auren Da Nake Buri

Fili na musamman domin Matasa, inda ‘Yan mata da samari ke fayyace ra’ayoyinsu game da irin mazaje da ‘yan matan da suke son aura tare da irin zaman auren da suke son yi gami da shagalgulan bikin da suke so, bari dai muje ga sakonnin masu karatu miji yadda sakonnin za su kasance:

Namiji mai saje nake son aura
Ina son na auri miji baki dan dai-dai mai saje wanda ya iya soyayya. Auren da nake so a gaskiya za a yi shagali wanda ba zai iya musultuwa ba. Ina son mu yi zama na amana da soyayya sosai.
Daga Hajiya Sadiya Umar Garin Kaduna

Burina Na miji wankan tarwada
Wallahi ina son Allah ya bani Soja, na gari, dogo, wankan tarwada, da son samu ne ma fari kamar ‘yellow’, gaskiya bana son wani shagalin biki, kawai a daura aure lafiua, Allah ya kai kowa gidansa lafiya bana son wata bidi’a,wayyo Allah na, Allah ka cika min burina akan mijin da zan aura, zama irin na larabawa zamu yi insha Allah.
Daga Fatima I. Umar Kaduna Nigeria to Saudi Arebia

Namiji mai sanin yakamata na zaba
Ina son Namiji mai hakuri da kuma kyautatawa iyalansa kuma wanda ya san darajar iyayensa da kuma nawa, sannan kuma ina son namiji da sanin ya kamata Allah dai ya bamu nagari, Ina son auren mu ya kasance babu wata bidi’a kuma ina son bikin mu kowa ya ji dadin zuwa ba tare da ya bata rai ba Allah ya sa mana albarka kan auren amin. Ina son rayuwar aurenmu ya kasance kamar a fim wato mu yi rayuwar turawa so simple babu wata hayaniya.
Daga Rabi’atu Yusif Usman Garin Adamawa

Ina son namiji mai sanin darajar mace
Ina matukar son na auri namiji mai wadatar zuciya me hakuri da sanin darajar mace wanda kuma yake daraja iyayensa da iyayena me kyaun zuciya ba kyan fuska ba, me addini da kamanta gaskiya da rikon amana, ina son ayi min aure tafarkin da ba zai sabawa addinina ba wanda kowa zai sawa auren albarka da yi mana fatan zuriya ta gari da zama lafiya a rayuwar mu, ina son rayuwar aurena mu samu fahimtar juna ni da mijina sannan mu zama masu tausayin junanmu da rikon amana da kyautawa junanmu ta ko wanne irin yanayin da muka tsinci kanmu a ciki za mu ji dadi.
Daga Maryam Muhd Mekwale Jos Fulatu namu

Bukatata na auri namiji mai rikon amana
Ina bukatar na auri namiji mai wadatar duci mai kyawan hali da addini da rikon gaskiya wanda kuma yake sona ba dan wani abun duniya ba wanda kuma ya san mutucin iyayena da ‘yan uwana. Ina son a yi min aure da mutane masu mutunci wanda zasu samin albarka a cikin shi, su kuma tayani farin cikin, ina son in yi zaman aure da kowa zai yi sha’awar sa.
Daga Ilham Sale Abdullahi Kano

Muradina namiji me addini da tsafta
Ina son miji Allah ya bani miji nagari mai addini maitsafta mai kyawawan halayaye wanda zai rinka tausaya min, wanda zai rikeni amana wanda zai girmama kowa da komai nawa ya kuma sadaukar da komai nasa saboda ni, wanda zai kula da bukatuna, ina son randa na yi aure ayi mun walimar hadi da saukar alkur’ani mai girma domiin samun zaman lafiya tare da kwanciyar hankali da zuriya dayyiba. Ina son zaman auranmu da mijina ya kasance muna zaman amana da hakuri da fahimtar junanmu da kuma yiwa dayanmu uzuri domin yau da gobe sai Allah, kuma ina son kyakkyawar fahimta a zamantakewar aurena da mijina da nunawa juna zallan kauna da kulawa.
Daga Ikilima Yunusa Jihar katsina karamar hukumar Jibiya1

Ina son Namiji mai tsafta dogo
Ina son namiji mai ilimi da hakuri da gaskiya da rukon amana, Ina son namiji mai tsabta kuma dogo shi ba mai jiki ba kuma shi ba siriri ba, Shagalin bikina ina son a tara malamai a yi wa’azi da rokon Allah ya bamu zaman lafiya da kuma zuriya ta gari.
Daga Amina Abubakar Sai’du kasar Saudiya

Zabina Namijin da ya iya soyayya
Ina son namiji wanda ya iya soyayya dumin nima zan nuna mai soyayya sosai don shi ne farin cikina abin alfaharina, tuni na fara mafarkin yadda zan shayar da shi madarar soyayya.
Daga Ilham Saleh Abdullahi Kano

Namiji mai ilimin addini da na boko na fi so
ina son na auri miji mai Hankali da nutsuwa, mai ilimi na addini dana boko, wanda ya san kima da darajar mutane, kuma mai hakuri da juriya. A ra’a yina ina son ayi min walima da ‘kanuri day’. Gaskiya ina son mu yi rayuwar aurenmu cikin yardar juna da aminci ta yadda ba wanda zai ji kanmu da ruyuwar jin dadi.
Daga Amina AAhmad garin maiduguri

Ina son namiji mai tawakkali
Ina son na aure namiji mai hakuri da tawakkali da wadatar zuci mai kuma girmama iyayena da kuma ‘yan uwana ko ba shida komai zan iya zama da shi indai yanada wannan halayen. Ni idan za a yi aurena ban son wata bidi’a ina son a tara min malamai suyi tunatarwa ga matar aure, har ma da ‘yan mata da dai sauransu wannan ma ya isa indai har za’a karu to wannan ma na yi shagalin bikina zan yi rayuwar aure da mijina yadda ya kamata yadda ba zai taba jin sha’awar kula wata ba balle ya yi tunanin kawota gidan.
Daga Fateemah Abdullahi (teemah beby) Jigawa, babura

Exit mobile version