Auren Da Nake Buri

Fili na musamman domin jin ta bakin matasa game da irin namijin da suke so ko kuma matar da suke son aura, tare da irin shagalin bikin da suke son yi, har ma da irin zaman auren da suke son yi da masoyan nasu, sai dai kuma akasarin matasan na jin kunya wajen fayyace irin shagulgulan bikin da suke son yi, ko me ya janyo hakan? Amsar na wajen matasa. Kadan daga cikin sakonnin matasa na wannan mako su ne:

 

Zabina Miji Mai Tsoron Allah

Burina na rayu a inuwa guda da namiji mai tsoron Allah; ilmi; mutumtawa, wanda ya iya soyayya, mai matukar jin kai. Ina matukar son na shaku da masoyina, kafin mu auri juna, watau auren so da kauna nake muradi. Burina mu yi rayuwar auren da za a rika kwatance da mu, watau rayuwa mai cike da fahimtar juna; mutumtawa; da soyayya mai tsayawa a rai ta bi jini da tsoka ta mamaye dukkan sassan jiki.

Real Nana Aisha

+22784506476

 

Kyau Na Samu Miji Mai Addini Da Boko

Ina so na auri namiji me addini, zurfin karatun boko da kuma matsakaitan shekaru. Ina son auren da bai sabawa shari’ar Muslunci ba da kuma al’adunmu na Hausawa. Ina son mu yi zaman aure  rayuwa me tsafta wacce za ta zama abun kwatance.

Fatima Jamila Usman

 

Mijin Da Ya San Mutuncin Kanda Da Darajar Mace Nake So

Ina son na auri miji na gari wanda ya san mutuncin kansa wanda ya san darajar ‘ya mace wanda yake wa iyayensa biyayya matuka. Auren da nake so irin wanda addinin musulunci ya yarda da shi ba tare da bidi’o’i ba. Rayuwar auren da nake son mu yi Irin tsaftatacciyar rayuwar da addininmu ya tsara mana da kuma irin tsaftatacciyar rayuwar da annabinmu (SAW) ya yi mana nuni da mu yi koyi da ita.

Hakima Muktar

 

 

Namji Mai Neman Nakansa Na Fi So

Ina son Namiji ya kasance mai neman na kansa! sannan uwa uba mai ilimin Arabi dana boko, haka nan ya kasance mai hakuri, da juriya, mai tsaffata, dan gaye, dan kwalisa ko da bai mallaki abin hawa ba. Ina son Auren na-gani-ina-so. Ina son mu yi rayuwa mai cike da walwala kana da farin ciki tare da dawwamamen zama na har abada cikin aminci da salama.

Hassana Yahaya Iyayi Maman Noor 08088615600

 

Mace Mai Ilimin Addini Da Zamani Nake Buri

Ina son matata ta kasance mai ilimin addini da na zamani, kuma mai tarbiya, da nutsuwa, mai sanin ya kamata, amma fa ba duka sai mai irin wannan halayyar ba ko da uku aka samu daga ciki zan so ta. Maganar kyau a ajiye shi gefe. Ina son na yi aure a cikin farin ciki da walwala. Ina son na yi rayuwar aure na a cikin farin ciki mai dorewa har karshen rayuwata.

Buhari Umar Assada +234 703 045 7903

 

 

Namijin Da Abin Hannunsa Bai Rufe Masa Ido Ba Na Zaba

Namijin da nake son aure mai addini da tsoron Allah, wanda ya san daraja da kima da mutuncin mace, wanda ya san girman na gaba da shi, mai neman na kansa, mai wadatar zuciya wanda abun hannun sa bai rufe masa ido ba. Aure cikin rufi asiri da wadata, ranar farko ayi kamu abisa al’ada, rana ta biyu kuma idan aka yi daurin aure ayi walima malamai su fadakar, Ina so kowa ya ci ya sha a biki na. Ina son na yi rayuwar aure cikin farin cikin d kaunar juna tare da miji na, Ina fatan samun kauna ta har abada tare da shi da fatan samun zuri’a ta gari.

Fatima Abdulrahman Abdu (Teema Dimple) 08123604443

 

 

Miji Mai Wadatar Zuci Nake Son Samu

Namijin da nake son sure, na farko mai addini da tsoron Allah a zuciya ba a fuska ba, wanda ya san mutunci da darajar mutane, mai wadatar zuci da sanin ya kamata, mai dogora da abun hannunsa wanda baya hangen abun hannun wani. Ina son Aure cikin rufin asiri, wanda addinin Musulunci ya yarda da shi. Rayuwa mai cike da kima da daraja, mai cike da zallar soyayya da yarda da kuma aminci a tsakanina da mijina, rayuwar da zata Daure a tsakanin mu har abada. Fatan Allah ya zaba mana abinda ya fi zama alkheri a rayuwar mu.

Maryam Ibrahim daga Sokoto 08136402046

 

 

Namiji Mai Kyan Zuciya Ba Fuska Ba Nake Muradin Aura

Ina matukar son na auri namiji mai wadatar zuciya, me hak’uri da sanin darajar mata, wanda kuma yake daraja iyayena, me kyaun zuciya ba kyan fuska ba, amman sai mugun hali. Ina son ayi min auren da mutane za su yi ta sakawa auren albarka, da yi mana addu’ar Allah ya bada zaman lafiya. Zaman auren da nake so Rayuwar jin dadi dan babu wanda zai bukaci ya yi rayuwar wahala.

Khadija Muhd Sha’aban (Mrs Breaker)

08122188717

 

 

Miji Mai Hakuri Da Tawakkali Nake Bukatar Na Aura

Ina Burin na auri Miji Mai hakuri, da tawakkali a rayuwa, Ina bukatar na auri Miji Mai ilimin addini dana zamani Ko yayane, Ina bukatar in auri Miji mai zuciyar neman halak dinsa duk rintsi duk wuya, Ina bukatar na auri mijin da ya san darajata, Ina bukatar na auri mijin da ke tsaida Ibadarsa akan lokaci ba masu rafkawaba, Ina bukatar mijin da zai girmama iyayena ya dauke su tamkar nasa duk da kasancewata Bazawara amma ina da burin auren mara Mata ina so ni dai a iskeni ko ba komai a lokacin na san na zama shi ya zama ni, a karshe kuma ina rokon Allah ya zaba mana mafi alkhairi albarkar Annabi Muhammad (s a w) masu aure Allah ya ba su zaman lafiya, marasa shi Allah ya kawo musu mazaje nagari masu matsala a gidan aurensu Allah ya kawo masu maslaha Allah ya kau da shaidan tsakaninsu.

Aisha Musa Yankara

Exit mobile version