Auren Da Nake Muradi

Auren Da Nake Muradi

Matasa wannan sashi ne na musamman da muka kirkiro muku domin bayyana irin auren da mutum yake da muradin yi. Za a iya aiko mana da bayana dalla-dalla kan irin auren da ake matukar son yi tun daga kan irin yarinyar da kake so ka aura ko irin saurayin da kike so ki aura har zuwa yanayin bikin da za a yi da kuma uwa-uba zamantakewar da mutum yake fatan yi da iyalansa daga lokacin da aka daura masa aure. A aiko ta adireshinmu na email. leadershipayaujumaa@gmail.com ko kuma a tuntube mu ta 08034980391 amma tes kawai banda kira.

Fitattun Sakonnin Matasa

Ina Muradin Auran Mace Fara

Assalamu Alaikum, nawa auren da nake muradi shi ne, farar mace mai gaba da baya da adalci a cikin lamuranta, sannan kuma ta kasance saliha, wacce ta san mutunci, mace mai tsafta, iya wanka da natsuwa. Wacca ko da yaushe za ta damu da ni, kulawa da ni da tarerayar junan mu. Za mu yi rayuwar aure mai daurewa da soyuwa da mutunta juna da aminci da kuma alkawari ba yaudara. Ni dai auren da nake muradi kenan.

Exit mobile version