Ayi Dokar Tilasta Wa Maza Auren Matan Da Suka Yaudara -Harirah

Daga El-Mansur Abubakar, Gombe

Hajiya Harirah Abdulsalam, Mace ce yar rajin kare yancin Mata ta koka kan yadda wasu Mazaje ke yaudarar da Mata suke hana su yin aure kuma su basa aurensu.

Harirah Abdulsalam, ta bayyana bakin cikin ta kan hakan a lokacin da take zantawa da jaridar Leadership A Yau inda tace yana da kyau a samar da wata doka a ƙasar nan ta tilastawa Mazaje auren Matan da suke yaudara.

Tace wasu Mazan sun mayar da Matan waje waɗanda ba Matan su na cikin gida ba tamkar ba Mata ba domin a kullum burin su shi ne su ga sun sami hanyar da za su keta musu ‘yanci su kuma ketare su barsu.

Harirah Abdulsalam, ta ƙara da cewa idan Namiji yaje wajen Mace suna nema kamar zai da gaske zai aure ta sai ya hure mata kunne ya hanata tsayawa da kowanne Namiji bayan ya san ba aurenta zai yi ba.

A cewar ta irin haka ne yake hana wasu Matan yin aure saboda sun sa rai sun sami Mijin aure ashe mayaudari ne kuma ko anyi auren baya jimawa saboda da tsakani da Allah ya aure ta ba.

Daga nan sai Hajiya Harirah Abdulsalam, ta yi kira ga gwamnatocin jihohi da hukumomin kare yancin ɗan adam da sauran jami’an tsaro da za su samar da doka wacce za ta tilasta Namiji auren Matar da ya yaudara kuma a sa doka na hana saki har sai da ƙwaƙwaran dalili.

Exit mobile version