Ayyana ‘Yan Bindiga Matsayin ‘Yan Ta’adda: An Kashe Maciji Ne Ba A Sare Kansa Ba – Barista Aminu

Barista Aminu

Wakilinmu na Kaduna ABUBAKAR ABBA, ya tattauna da kwarrre kuma sanannen LAUYA ABDULRASHEED AMINU kan ayyanawar da Kotun ta yi, inda ya yi nuni da cewa, an bari ne dan Zaki ya girma, an bar Jaki ne ana bugunTaiki, rashin hobbasan daukar matakai.

Me zaka ce kan ayyana ‘yan bindiga a matsayin yan ta’adda da Kotun Tarayya ta yi?

Na farko, Babban Lauyan Nijeriya kuma Atoni Janar Abubakar Malami shi ya gabatar da roko na wucin gadi a gaban wannan kotun da ta gaggauta ayyana su wadanan nan ‘yan bindiga da ake fama da su a matsayin kungiyar ‘yan ta’adda wadanda za a sanya su a cikin ‘yan ta’adda a duniya kamar irin su ISWAP, Al-Shabab, Al-ka’ida da sauransu.

Wannan shi ne rokon da ya gabatar wa da Kotun, wanda tun da ba a ba da dama wani ya kalubalanci wannan rokon ba, kotun ta amsa wannan rokon ta kuma ayyana su a matsayin ‘yan ta’adda. Abin da hakan yake nufi shi ne, daga yanzu, Gwamnatin Tarayya da kuma kasashen duniya za su iya yakar duk wadanda suke yin aikin fashin daji da garkuwa da mutane da kuma wannan ta’addancin a matsayin ‘yan ta’adda.  A bisa abin da duniya ta yarda da shi ne a taron duniya da aka yi kan ta’adanci. In ba ka manta ba, Gwamnatin Tarayya kwanan baya ta sawo wasu Jiragen yaki daga kasar Amurka kuma yarjejeniyar da Nijeriya ta yi da Amurka shi ne, ba za ta yi aiki da wadanan Jiragen yakin ba sai wajen yaki tsakanin kasa da kasa da yakin ta’adanci. To shi ya sa kilan wannan zai zama wata dama ga Gwamnatin Tarayya ta yi amfani da karfin da ya wuce a kan wadanan mutane da suke aikata ayyukan fashin daji.

Sa’annan kuma Nijeriya za ta iya yin amfani da kudi wajen yakar ta’adanci ba tare da sai ta je neman sahalewar ‘yan majalisu ba, za ta iya daukar kudi a ko da yaushe saboda kudin za a yi amfani da su ne wajen yakar ta’adanci. Wannan shi ne wannan ayyanawar take nufi. Sa’annan, ba wanda zai zo ya ce an yi amfani da karfi (fiye da kima) kan wadannan mutanen.

Wasu na gamin kamar an makara wajen ayyanawar, musamman ganin yadda suka jima suna kashe mutane, ka yarda da hakan?

Wato maganar ba wai makara aka yi ba. Ni, yadda nake ganin abin ba matakin da ya kamata a dauka aka dauka ba bakidaya, kamar an bar jaki ne ana dukan taiki. Sa’annan abubuwan da ke faruwa a Nijeriya cewa wadansuda suke aikata wannan kashe -kashen, fashin daji da garkuwa da mutane ba kungiyoyin ‘yan ta’adda ba ne, yanzu kamar yadda ake da kungiyoyin ‘yan ta’adda na Al-ka’ida, Al-Shabab, su ‘yan bindiga, masu laifi ne da suke aikata laifukka. Sa’annan ba su da hadaka da biyayya ga gungiyoyin  ta’addanci a duniya,  a’a, su mabarnata ne da suke neman kudin fansa ko kuma wata ramuwar gaiyya ko kuma a samar masu da wani sarari. Idan ka dauki kungiyar Boko Haram kungiya ce da ta shafe sama da shekaru goma tana yin ta’adanci, zan iya cewa, ‘yan bindigar daji an bari ne dan zaki ya girma, domin wadannan mutanen ba yau suka fara ba.

Misali, in ka dauki kungiyar Boko Haram, kungiya ce ta akida wacce ke da alaka da addininsu,  duk da haka suka fito suna aikata barna kuma lokacin da suka kafa akidarsu, suka ce wanda bai bi ba, ya zama wanda za su yaka. To amma su wadanan a’a, laifuka suke aiwatarwa, in aka zauna da su, irin wadanda ke bibiyarsu, kamar su Dakta Sheikh Ahmad Gumi kamar yadda maganganun da ke fitowa daga bakunansu suka nuna, sun ce jami’an ‘yan sanda sun tozarta su, an ci amanarsu, an kwace masu kudadensu, jami’an soji sun masu, Hakimai da Daggatai sun masu, Alkalai, Lauyoyi, Sarakuna, ‘yan kasuwa, manoma, mutanen gari sun masu, an yi watsi da su abin da suka dogara na sana’arsu yanzu babu an cinye masu wajen kiwo, burtalai da sauransu, shi ya sa suka dauki makami, bayanan da ke fitowa daga bakunansu ke nan, to ka ga, babu wani alamun ta’adanci.

Sa’annan za ka ga a wani lokaci sun ce in suka kai harin suna cewa sun kai ne don fansa domin an kashe masu wani. Abu ne da Gwamnati ta  bar shi zuwa tsawon lokaci ba wai wannan Gwamnatin kadai ba, Gwamnatocin baya, da ita wannan Gwamnatin da abin ya fi yawa a lokacinta da kuma rashin ganin hobbasar matakan da take dauka domin misali. An sha gani a wurare daban daban, Gwamnonin Zamfara da Katsina sun zauna da mutanen nan, an maida jawabai na sulhu da sauransu kuma za ka ga duk bayanan da suka yi bai da nasaba da akida da suke son sai sun tursasa wa mutane sun bi akidarsu, a’a, sai dai aikata laifukka da sauransu, don haka, ni a gani na riga Malam Masallaci ne ayyana su a matsayin ‘yan ta’adda domin ba su ba ne.

Sa’annan yin hakan kamar bude wata kafa ce su wadanan gungiyoyin ta’addancin suna nan a wurare daban-daban a nan Nijeriya ma muna fama da su. To idan aka ayyana su kamar irinsu Al-ka’ida Al-Shabab cewa daya ne to ka ga idan suka hada karfi da karfe, sai a zo abin ya yi girma fiye da yadda za a iya abin.

Sa’annan kowa ya ga babu wani shiri da aka yi a tun can baya, na yakar mutanen nan yadda ya kamata. Bambancin kawai shi ne ayyanawar da kuma yadda za a yi a yanzu saboda an ayyana su, amma ba a matakai ba, tun da misali, babu wani cikakken tsari da yake a kasa gamsasashe cewa akwai wani shiri da aka yi na ayyana su a matsayin kungiyar ta’adanci don a kawo karshen wannan abin.

Sa’annan in ka duba lamarin nan, akwai abubuwa da dama wanda ba ma yaki ne zai warware shi ba domin shi irin wannan yakin ba ya karewa. Kasar Etofiya misali irin wannan kananan yakin da yaki ci yaki cinyewa na nema ya ci Gwamnati.

Abubuwa ne sai an tattauna, kamar yadda kowa yake dan kasa su ma ‘yan kasa ne duk da cewa, idan ka ce abi matakai na sulhu sai wasu su ce kamar kana goyon bayan abin ne, babu wanda yake goyon bayan abin da suke yi domin mutanen nan, babu wanda suka raga wa, ba su raga wa ‘yan uwansu Fulani ba. Sa’annan, idan ka duba wata hadaka ce ta aikata laifi, ba wai Fulani kadai suke fashin daji ba akwai sauran wasu kabilu daban-daban.

Ganin irin rawar da masu bai wa ‘yan bindigar da kuma masu daukar nauyinsu ke takawa, ko ayyanawar za ta iya zama kamar an kashe maciji ne amma ba a sare kansa ba?

Kwarai da gaske, ka ga ko su masu bai wa ‘yan bindigan daji bayanai din ma, ana zargin cewa, wasu jami’an tsaro ne, wasu Sarakuna, wasu Limamai ne, wasu mata ne, saboda haka wannan ayyanawar ba shi ba ne mafita ga yakin da ake yi da su. A yi abin da ya kamata a fafare su, inda misali ya kamata a tattauna domin yau kana gani yadda kungiyar Boko Haram ta shafe sama da shekaru goma suna aikata ta’adanci, wasu sun zo sun mika wuya sun nuna cewa, bisa tursasawa suka yi.

Sa’annan, idan yakin nan da ake son a yi ana ganin kullum jami’an tsaro suna kama wadanda ake zargin cewa suna cikin wadanan kungiyoyin na fashin daji da sauransu, amma ba ka ganin cewa, ana gurfanar da su a gaban Kotuna ana yanke masu hukunci bisa dokokin kasa, sai dai ka ga kawai in aka ce an kama su an nuna su ne su ka yi laifi ka za, shi kenan daga nan labarin ya kare. Za ka ga ku ‘yan jarida ne kuna yawo ai na san cewa, da ana yin shari’oin a kotuna da za ku bai wa ‘yan kasa bayanai, to iyakar bayanina kullum, yana nan tsaye. Wannan kullum za ka dinga jin zargi da ake yi na hukimomin tsaro sun karbo kudade an nuna kudaden da sauransu, amma ba zaka kara jin labarin wadanan kudaden ba. To duk wasu irin abubuwa ne da suke matakan da aka dauka, ba a dauki kwararan matakai yadda ya kamata ba.

Wasu na danganta ayyanawar da nasaba da siyasa ganin cewa zaben 2023 na kara karatowa, me za ka ce kan wannan?

Wato ni ban ma alakanta shi da harkar zabe da sauransu, kawai dai ni ina ganin dabara ce ta kwace wa ita Gwamnati domin kamar yadda na yi bayani a baya, ba maganar wai a ayyana su da akwai jinkirin ayyana su yanzu, wato mataki wanda aka dauka in dai mataki ne sahihi kwakkwara, ko wanne lokaci aka dauka komin lattin da aka yi ba a cewa ya yi latti. Sai dai, gwanda da a yanzu aka farga, abin da ake nema sauki, ni na fi ganin sa a gyara samun sa’a.

Me ‘yan Nijeriya za su gani kan wannan tsarin?

Wato ni a hasashena, ban ganin cewa ‘yan Nijeriya za su ga wani banbanci da muke gani a yanzu domin an dade, ana gafara sa ba mu ga kaho ba. Muddin shugaban kasa bai dauki aikin a matsayinsa na  Babban Kwamandan Askarawan Nijeriya, ya dauki yakin nan da hannun shi da gaske ya kuma dauki matakai ya saka masu ruwa da tsaki kuma a daina kushe wadanda suke bayar dagudunmawarsu ba… har kullum ina jinjina wa yunkurin Dakta Ahmad Gumi domin a matsayinshi na ba wanda yake da mukami ba, a matsayinsa na Malami wanda yake ganin wasu za su saurare shi daga cikin mutanen ya jawo hankalinsu ba tare Gwamnati ta ba shi kudi ba, to kila da an ba da goyon baya da an samu ire-iren shi da dama,  za su ba da wannan gudunmawar  kuma a samu masalaha, domin wani lokacin ba sai an je a gwamnatance ba, tun da mutanen nan sun ce ba su gasgata ‘yan siyasa ba domin sun ce suna yaudararsu.

To amma suna mutunta Malamai, yau in ka dauki Malamai misali, daga kungiyoyin da ake da su daban- daban, Gwamnati ta sa su cikin al’amarin nan,  aka kuma dauki manyan shugabannin  misali tunda ana alakanta Fulani da  abin nan, akwai  kungiyoyin Fulani  manya da wadanda akan yi amfani da su wani lokaci, Ina ganin da za a kawo sulhu, inda Gwamnati ta ce ai mana makaranta, dama aikin Gwamnati ne, yi mana hanya, yi mana mashayar ruwa da Burtalai na inda za a iya a dawo da su, a dawo da su, misali,  yadda Gwamnati ta kawo maganar shirin Rugar nan, zai kawo saukin al’amarin, zai rage aikata barna  domin abin bakin ciki ne, za ka ga kananan yaran nan sun taso suka ga ana yi shi za su yi.  Wanda ba ka ba shi ilimi ba to ka ga, ba za ka hana shi zamowa dan ta’adda ba, to shi ne daukar kwararan matakai daga gun Gwamnati ya zama kamar busa ne.

 

 

Exit mobile version