Ayyana ‘Yan Bindiga Matsayin ‘Yan Ta’adda: Ko Zai Yi Tasiri?

Masana Sun Rabe Zare Da Abawa

Kashe-kashen

Daga Sharfaddeen Sidi Umar,

 

Ayyana ‘yan Bindiga da Kotu ta yi a matsayin ‘yan ta’adda lamari ne da aka jima ana ta kiraye- kiraye a kai musamman a bisa tunanin kwakkwaran matakin zai yi tasiri wajen kawo karshen ayyukan ‘yan bindigar da suka hana wa al’umma bacci da ido biyu.

 

Hukuncin da alkalin Babban Kotun Tarayya da ke Abuja, Mai Shari’a Taiwo Taiwo ya yanke a ranar Juma’ar makon jiya ya biyo bayan bukatar da Gwamnatin Tarayya ta shigar gaban kotun a bisa ga yadda suke kisan gilla, garkuwa da mutane da hana al’umma kwanciyar hankali.

 

Tuni dai shugabanni, kungiyoyi da al’ummar kasa suka bukaci Gwamnatin Tarayya da ta ayyana ayyukan ‘yan bindigar da suka addabi yankunan Arewa- Maso- Yamma da Arewa- Ta- Tsakiya a matsayin ‘yan ta’adda kamar yadda aka yi wa kungiyar IPOB amma bukatar ba ta samu karbuwa ba sai a yanzu.

 

Rahotanni da dama sun tabbatar da cewar ‘yan ta’addar a 2021 kadai sun kashe dubban mutane sama da mayakan Boko- Haram ta yadda a watan Satumba sun kashe mutane akalla 600 a Arewa. Jihohin Zamfara, Katsina, Kaduna, Sakkwato, Benue da Neja ne ‘yan ta’addan ke cin karensu ba babbaka wanda har ya zama silar datse layukan sadarwa a wasu Jihohin.

 

A yayin da yake gabatar da kudurin bukatar a gaban kotun, Daraktan Shigar da Kara na Tarayya, Muhammad Abubakar ya bayyana wa kotun cewar Shugaban Kasa Muhammadu Buhari ya aminta da ayyana ‘yan bindigar a matsayin ‘yan ta’adda.

 

A hukuncinsa, Mai Shari’a Taiwo Taiwo musamman ya bayyana cewar ayyukan kungiyoyin ‘yan bindiga da ‘yan ta’adda ayyuka ne na ta’addanci wadanda suka haramta tare da saba wa doka.

 

Kamar yadda takardun da aka shigar a gaban kotun suka nuna, Gwamnatin Tarayya a bisa ga bayanan tsaro ta tabbatar da cewar ‘yan bindigar su ne ke da alhakin kashe- kashe, garkuwa da mutane da fyade a Arewacin Nijeriya.

 

Gwamnatin Tarayya ta samu kungiyoyin ‘yan bindigar da laifukan “ta’addanci, yawaitar garkuwa domin karbar kudin fansa, garkuwa da daliban makarantu masu yawan gaske, satar shanu, fyade, mayar da jama’a bayi, cin zarafin mata, tursasa wa mata yin ciki, kai farmaki da kisan al’umma da yawaitar tarwatsa dukiyar jama’a da sauransu da dama a Nijeriya musamman a Arewa- Maso- Yamma da Arewa- ta Tsakiya wadanda wadannan kungiyoyin na ‘yan ta’adda da ‘yan bindiga da sauran makamantansu da ke ayyuka iri daya ke aiwatarwa ba kakkautawa.”

 

“Ayyukan kungiyoyin ‘yan bindiga da ‘yan ta’adda da ire-irensu ayyukan ta’addanci ne da ke haifar da rashin kwanciyar hankali da tsaron al’umma wanda barazana ne ga tsaron kasa da hadin kan jama’a a matsayin kasa daya.” In ji Gwamnatin Tarayya.

 

A hukuncin, kotun ta bayyana duk wani nau’in ayyukan kungiyoyin ‘yan bindiga da ‘yan ta’adda da ire- irensu a kungiyance ko a daidaiku a ko’ina suke a fadin kasar nan a matsayin ta’addancin da aka haramta.”

 

Tasirin Ayyana ‘Yan Bindiga A Matsayin ‘Yan Ta’adda

 

Masu rike da madafun iko a Nijeriya kama daga Gwamnoni, ‘Yan Majalisun Tarayya da na Jihohi, kungiyoyi da masana sha’anin tsaro duka sun dauki matsayar cewar ayyana ayyukan ‘yan bindiga a matsayin ta’addanci zai taimaka kwarai ainun wajen shawo kan bahaguwar matsalar ayyukan ‘yan bindiga a sassa da lungunan Arewacin Nijeriya da ma duk wani wajen da ake yaki da su.

 

A bayaninsa kan wannan matakin, Ministan Shari’a, Abubakar Malami ya bayyana cewar hukuncin da kotun ta yi ya nuna irin kokarin da Gwamnatin Tarayya ke yi wajen kawo karshen yaki da ta’addanci.

 

Babban Lauyan na Gwamnatin Tarayya wanda ya yi magana ta hannun Kakakinsa, Umar Gwandu ya bayyana cewar daukar wannan matakin ya nuna Gwamnati Tarayya tana aiki da doka da oda tare da yin amfani da tsarin da duniya ta aminta da shi wajen yaki da ta’addanci.

 

A bayaninsa Gwamnan Jihar Kaduna, Malam Nasir El- Rufa’i na da ra’ayin babu wata hanyar yaki da ‘yan bindiga da ta wuce yi masu barin wuta wanda ya ce shi ne dalilin da ya sa yake son a ayyana su a matsayin ‘yan ta’adda ta yadda za a yake su ba kakkautawa.

 

Gwamnan wanda jiharsa ke gaba- gaba wajen fama da bahaguwar matsalar ya bayyana cewar tun a 2017 Gwamnatin Kaduna ta mika bukatar ayyana ‘yan bindiga a matsayin ‘yan ta’adda a rubuce ga Gwamnatin Tarayya domin a ra’ayinsa ayyana su ne kadai zai bai wa sojoji ikon kashe su ba tare da wani abu ya biyo baya ba daga kasashen duniya kamar yadda ya bayyana jim kadan bayan karbar rahoton tsaro a Kaduna.

 

Da yake bayyana jin dadinsa kan ayyana ‘yan bindiga a matsayin ‘yan ta’adda masani harkokin tsaro kana tsohon Mataimakin Sufeto- Janar na ‘Yan Sanda Taiwo Frederick Lakanu ya bayyana cewar ba a makara ba wajen daukar wannan matakin wanda ya ce ya zo dai-dai da lokaci.

 

“A yanzu yanayin yaki da ‘yan bindigar zai zo daya da irin farmakin da ake kai wa mayakan Boko- Haram da duk wasu kungiyoyin ta’addanci har a samu galaba a kansu. Fargaba ta ita ce ayyana su a matsayin ‘yan ta’adda zai iya sa su kara daukar matakin canza salo har su hade da wasu manyan kungiyoyin ta’addanci.” Ya bayyana.

 

A bisa lura da muhimmancin ayyana ‘yan bindigar a matsayin ‘yan ta’adda Majalisar Dattawa da Majalisar Wakilai a watan Satumba suka yi kira ga Shugaba Buhari da ya ayyana su a matsayin ‘yan ta’adda.

 

A cewar majalisun biyu a zamansu mabambanta idan aka ayyana ‘yan bindiga a matsayin ‘yan ta’adda a Dokar Yaki da Ta’addanci ta 2011 za a yake su da hukunta su tare da ayyana su a matsayin masu laifi kuma wadanda ake nema ruwa jallo a kuma kama su a duk inda aka gan su domin gurfanar da su, haka ma wadanda ke daukar nauyinsu da wadanda ke hulda da su duk za su fuskanci hukunci.

 

A yanzu haka dai wasu bayanai daga jami’an soji sun nuna cewar bayan ayyana ‘yan bindigar a matsayin ‘yan ta’adda, Rundunar Soji ta shirya tsaf domin fara amfani da sababbin jiragen yaki na Super Tucano domin yakar ‘yan ta’addan ta hanyar yi masu luguden wuta.

 

Bayanan sun nuna sojoji sun kasa fita da jiragen Tucano daga Arewa- Maso- Gabas zuwa Arewa-Maso-Yamma da Arewa ta- Tsakiya saboda sharuddan da aka shata wajen sayar da su da suka shafi ‘yancin Dan- Adam amma yanzu wannan dokar ta kawar da komai.

 

Wani babban Janar na soja ya bayyana wa Saturday Punch cewar a yanzu bayan wannan dokar suna jiran umarni daga Gwamnati kan mataki na gaba da za a dauka. Ya ce hakan na daya daga cikin abubuwan da Shugabannin Hukumomin Tsaro suka tattauna da Shugaban Kasa a ranar Alhamis. Don haka “Umarni muke jira.” Ya bayyana.

 

Ayyana Su Ba Zai Canza Komai Ba- Gumi

Dakta Ahmad Gumi

A ra’ayinsa fitaccen Malamin Addini, mai bibiyar sha’anin tsaro Dakta Ahmad Gumi ya bayyana cewar ayyana ‘yan bindiga a matsayin ‘yan ta’adda ba zai canza komai ba a yaki da su da ake yi.

 

Gumi wanda ke da ra’ayin sulhu ne mafita da ‘yan ta’addar ya jaddada cewar siyasa ce kawai kashin bayan ayyana ‘yan fashin dajin a matsayin ‘yan ta’adda domin a ta bakinsa “Wannan canza sunan ba zai yi wani tasiri ba domin tun kafin a ayyana su ake yaki da su a matsayin ‘yan ta’adda.”

 

Gumi wanda ya yi magana ta bakin jami’in tuntubarsa kan yada labarai, Malam Tukur Mamu ya ce “Idan za a tuna, an ayyana IPOB a matsayin kungiyar ta’addanci wanda akwai odar kotu kan hakan amma hatta kasashen duniya ba su aminta da ayyanawar da Gwamnatin Tarayya ta yi masu ba don haka bukatar yin hakan ba ta yi tasiri ba.”

 

Gumi ya ce yana fatan ‘yan Nijeriya ba za su dauki makiyaya a matsayin ‘yan ta’adda ba maimakon hakan su dauki laifin da wasu tsiraru daga cikinsu ke yi a kan mutanen da ba su ji ba ba su gani ba kamar yadda ake kallon IPOB da hare- haren da suke kai wa jami’in tsaro da sauran ‘yan arewa a matsayin ta’addanci.”

 

Malamin ya kuma yi fatan wannan dokar ba za ta bai wa jama’a lasisin daukar makiyaya a matsayin ‘yan ta’adda ba wanda a cewarsa yin hakan zai haifar da karin tashin hankali maimakon samar da zaman lafiya.

 

Shi kuwa a nasa bangaren, masanin tsaro, Kyaftin Sadik Garba (Mai ritaya) ya ce babu tabbacin samun nasara bayan bayyana ‘yan bindiga a matsayin ‘yan ta’adda musamman saboda a yanzu ma yakin a ke yi da su. Sai dai ya ce amsa kiran jama’a da Gwamnati ta yi na ayyana su a matsayin ‘yan ta’adda abu ne da ya dace.

 

… Abu Ne Mai Kyau, Ya Rage A Ga Rawar Da Jami’an Tsaro Za Su Taka, In Ji Barista Jibrin

Barista Jibrin S. Jibrin

 

Daga Khalid Idris Doya

 

Shi kuma Barista Jibirn S. Jibrin shugaban kungiyar Lauyayoyi ta kasa reshen jihar Bauchi (NBA) ya bayyana wa LEADERSHIP Hausa cewa ayyana ‘yan bindiga a matsayin ‘yan ta’adda mataki ne mai kyau da yake kallon hakan zai iya bai wa jami’an tsaro da gwamnati cikakken ikon tunkararsu yadda ya dace domin kawo karshen matsalar a fadin Nijeriya.

 

Yake cewa: “To na farko dai a kan wannan batu na ayyana ‘yan bindiga a matsayin ‘yan ta’adda, akwai abubuwan da ya kamata a lura da su, na farko, shi ayyana wani gungun mutane a matsayin ‘yan ta’adda hurumi ne na shari’a wanda kotu take yi bisa hujjoji da dalilai da ta gamsu da su. Na biyu ayyana ta’addanci a kan wasu mutane yana bai wa gwamnati da jami’an tsaro damar amfani da duk wani karfi na soji da makami don yakar wadannan mutane kamar yadda dokar da take da alaka da wannan batu na 2011 na Nijeriya da sauran dokoki masu alaka da su suka tanada.”

 

Barista Jibrin S. Jibrin ya kara da bayyana cewar wannan matakin da aka dauka zai taimaka matuka wajen dakile ‘yan bindiga, “Don haka wannan matsayi da gwamnatin Nijeriya ta dauka a kan ‘yan bindiga yana iya tasiri idan aka yi la’akari da cewa sabanin a baya, yanzu jami’an tsaro sun samu lasisin fuskantar su ‘yan bindigar da duk karfi da kaimin da suke da shi.”

 

Sai dai ya ce a yanzu za a sanya ido ne a ga irin rawar da jami’an tsaron za su iya takawa a kan ‘yan bindigan, ta haka ne za a iya ganin tasirin matakin ko akasin shi, “Abun da za a tsaya a kalla shi ne tasirin damar da su jami’an tsaro da gwamnati suka samu yanzu ko za a ga amfanin haka a kasa wato a zahiri ko kuma a’a,” In ji shi.

Exit mobile version