Ayyukan Da Ganduje Ke Yi Na Da Alaka Da Nasarar Da Aka Samu A Zaben Kananan Hukumomi —Garo

An Gwamnan Kano Dokta Abdullahi Umar Ganduje da cewa ya yi rawar gani wajen gudanar da zaben kananan hukumomi a jihar Kano.Kwamishinan ma’aikatar kananan hukumomi Alhaji Murtala Sule Garo ya bayyana hakan.

Yayi nunu da cewa duba da yanda a wasu jahohin anma shafe shekaru shida wasu 9 ba a gudanarda zaben kananan hukumomi ba, amma anan kano wa’adin zababbun daya kare ba a dauki wani tsawon lokaci ba, aka sanya ranar zabe akayi, duk kuwa da yanayi na karancin kudi da ake fama dashi a kasarnan.

Ya ce “Mun godewa Allah da al’ummar jihar Kano suka fito suka kada kuri’arsu akayi zaben.Cikin kwanciyar hankali da lumana ba tareda wata matsala ba”

Alhaji Mutala Sule Garo ya ce zabe ya tafi daidai  duk da cewa an dan sami tsaiko na raba kayan zabe sakamakon sunzo hukumar zabe a makare, ba a gudanarda zaben a lokacin da ake bukata ba, amma  isowar kayan aka raba a kananan hukumomi 44 jama’a sun tsaya sun yi zabe.

Ya yi kira da cewa a ci gaba da baiwa Gwamnatin Kano goyon baya, zabe ya nuna jama’a sun zabi abinda zai taimakesu, sunji dadin yanda jama’a suka fito sukayi zaben nan, ayyukanda

Gwamnatin Kano take yanada alaka da nasarar da sukayi a zaben da ba a taba ganin irinsa ba wajen nagarta.

Alhaji Murtala Sule Garo yayi kira a wadanda ba su yi nasara ba su zo a hada kai da su domin ci gaban jihar Kano domin idan akayi zabe an gama maganar banbancin jam’iyya al’ummar Kano gaba daya za a sa a gaba dan dorawa akan ayyukan alkhairi da Gwamna Ganduje yake aiwatarwa.

Kwamishinan na kananan hukumomin Alhaji Murtala Sule Garo yayi kira ga dukkan zababbun shugabaninn kananan hukumomin su bada hadin kai ga gwamnati wajen aiwatarda ayyuka tukuru domin bada gudummuwansu ga ci gaban al’ummar jihar Kano.

Exit mobile version