Ayyukan Jami’an Ilimi Da Muhimmancinsu (2)
  • English
  • Business News
Wednesday, October 8, 2025
Leadership Hausa
Read English News
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Ra’ayi Riga
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Ra’ayi Riga
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
Leadership Hausa
No Result
View All Result

Ayyukan Jami’an Ilimi Da Muhimmancinsu (2)

byIdris Aliyu Daudawa
9 months ago
Ilimi

Maida hankali sosai yana da amfani saboda kuwa dole ne su tabbatar da cewar ana gudanar da ayyuka kamar yadda ya dace wato yadda doka ta ayyana ko ta tanadar.Jami’an ilimi akwai bukatar suna  fahimta da ganewa kan al’amuran ilimin fasaha da yadda ake tafiyar da su.

Dole ne su yi kokari wajen koyon amfani da hanyoyi daban- daban nak afar sadarwa ta zamani saboda kuwa hakan zai taimakawa wajen bunkasa tafiyar da ayyukansu na jami’an ilimi ta hanyoyi da yawa.Daga karshe jami’an ilimi su tilastawa kansu son  bunkasa ilimi da kuma ganin sai dalibai sun fara samun ci gaba kan sakamakon abinda suke koyo.Dole ne su kasance misali da karfafawa wasu da basu kwarin gwiwa su ma su kasance sai sun zama gwarzaye a vanagaren ilimi, duk da hakan kuma su kasance suna kokarin ganin sai an samar da tsare- tsare ko manufofi da za su taimakawa dalibai cimma nasara.

  • Ayyukan Jami’an Ilimi Da Muhimmancinsu
  • Hukumar Ilimin Bai Daya Za Ta Gina Dakunan Karatun Zamani A Makarantun Nijeriya

Kacokan, irin ilimin da ake bukatar jami’in / jami’an ilimi su kasance ya kasance sun san fannoni ko vangarori na ilimi,gogewa ko kwarewa, dabaru da kuma son lamarin aikin nasu har ga zuciya. Irin aiki ko gudunmawa da jami’an ilimi suke badawa bata wuce su tabbatar da cewa dalibai suna samun nagartaccen ingantaccen ilimi,su kuma hukumomin ilimi da al’umma su rika bada tasu gudunmawar bayan suma an taimaka masu domin a cimma muradan ci gaba da ingancin ilimi.

Ci Gaba Kan Ayyukan Jami’in Ilimi

Shi/su jami’an ilimi wadansu mutane ne da yakamata su da lamarin gudanar da ilimi har da tsare- tsare da manufofi a wata makaranta ko hukuma ana tafiyar da su kamar yadda ya dace. Hakanan ma ya dace su tabbatar da cewa  cigaban tsarin manhajar koyarwa, koyon yadda ake koyarwa, irin sakamakon yadda dalibai suke koyo yana tafiya daidai da muradu, manufofin ita hukumar.Jami’an ilimi suna aiki da Malamai, masu tafiyar da lamarin ilimi,da sauran masu fada aji wajen samar da tsare- tsare da manufofi wadanda za su taimaka wajen bunkasa samuwar ingantaccen iulimi ga dalibai.daya daga cikin ayyukan jami’/ jamai’an ilimi shi ne na samar da aiwatar da tsare- tsaren ilimi, wadanda suke taimakawa muradan ko manufofin hukumar.

Wannan ya hada da yadda zai rika yin aiki yana tuntuvar Malamai da sauran  kwararru ta  fannin ilimi domin tabbatar muradan koyarwa, abubuwan ko daraussan da ake koyarwa, da yadda ake auna fahimtar daliban kan abinda aka koya masu, hakan ya yi daidai da abubuwan da su daliban suke son ko, ya kamata  a koya masu da kuma ita hukumar makarantar.Hakanan ma jami’an iimin suna bibyar yadda ake aiwatar da tasare- tsare da manufofi,su kuma  bada shawarwari yadda za a kara bunkasa lamarin, wannan kuma ya dogara ne kan irin bayanan da suka samu daga Malamai, dalibai, da sauran masu ruwa da tsaki .Akwai ma wani babban aikin jami’an ilimi wanda shi ne su bada dama yadda za a samu ci gaban Malamai, da sauaran kwararru ta vangaren ilimi.

Wannan ya kunshi shirya tarurrukan karawa juna ilimi,zuwa wasu muhimman taro, da horarwa lokaci zuwa lokaci wanda hakan zai sa a maida hankali ga sababbin hanyoyin koyarwa, bunkasa manhajojin da za a koyar, da irin dabarar da za ayi amfani da ita  wajen  lura da irin ci gaban da aka samu  sanadiyar hakan.Jami’an ilimi suna bada tsarin koyarwa domin taimakawa Malamai wadanda watakila su kan fuskanci matsala wajen aikinsu na koyarwa, kamar yadda za su iya tafiyar da aji da  kuma sa dalibai su kasance cikin koyarwar.Duk da hakan jami’an ilimi s uke da alhakin lura da yadda ko tsare- tsaren ilimin da manufofin sun dace da yadda ake so ko bukata.

Irin hakan ya hada da sanin yadda fahimtar ko kokarin daliban yake da kuma yin wani abu kan hakan, mai da hankalin Malami kan aikin shin a koyarwa, da sauran abubuwan da suke da alaka da samun nasarar ilimin da ake koyarwa. La’akari da hakan, suna iya bada shawarwari saboda a samar da sauye- sauye kan tsare tsare da manufofi, ko kuma su samar da sabbin hanyoyin da aka san ko tabbatar da za su bunkasa ganewar abinda ake koyawa dalibai wanda hakan zai sa a samu sakamakon da ake so. A takaice, ayyukan jami’in/jami’an ilimi suna da yawa sun kuma bambanta.Wadannan kwararrun suna bada muhimmiyar gudunmawa wajen tabbatar da cewa su tsare – tsare da manufofin ilimi suna tafiya kafada- kafada da bukatar dalibai da hukuma, su ma  kwararrun fannonin ilimi suna samun irin gudunmawar da suke bukata domin su ma su zama suna gudanar da ayyukansu kamar yadda ya dace.

ShareTweetSendShare

MASU ALAKA

Minista Nnaji Ya Yi Ƙarar Jami’ar UNN Kan Rikicin Takardun Kammala Makaranta
Ilimi

Minista Nnaji Ya Yi Ƙarar Jami’ar UNN Kan Rikicin Takardun Kammala Makaranta

October 6, 2025
Uwargidan Shugaban Ƙasa, Remi Tinubu, Ta Nuna Damuwa Kan Ƙarancin Malamai A Duniya
Ilimi

Uwargidan Shugaban Ƙasa, Remi Tinubu, Ta Nuna Damuwa Kan Ƙarancin Malamai A Duniya

October 5, 2025
Jami’ar Ibadan Ta Bude Sashen Karatu A Gida Ta Intanet
Ilimi

Jami’ar Ibadan Ta Bude Sashen Karatu A Gida Ta Intanet

October 4, 2025
Next Post
Za Mu Tabbatar Da Samun Kyakkyawar Alaka Da Gwamnati Don Ci Gaban Kasuwar Kofar Ruwa – ‘Yanleman

Za Mu Tabbatar Da Samun Kyakkyawar Alaka Da Gwamnati Don Ci Gaban Kasuwar Kofar Ruwa – ‘Yanleman

LABARAI MASU NASABA

Babban Yankin Sin Ya Soki Lamirin Kalaman Aware Na Jagoran Yankin Taiwan

Babban Yankin Sin Ya Soki Lamirin Kalaman Aware Na Jagoran Yankin Taiwan

October 8, 2025
Yawan Zirga-Zirgar Jiragen Kasa Tsakanin Sin Da Turai Kan Layin Dogo Na Tsakiya Ya Zarce 3,000 A Bana

Yawan Zirga-Zirgar Jiragen Kasa Tsakanin Sin Da Turai Kan Layin Dogo Na Tsakiya Ya Zarce 3,000 A Bana

October 8, 2025
Majalisa Ta Nemi Jami’an Tsaro Su Ceto Daliban Jami’ar Gusau 30 Da Aka Sace

Kafa ‘Yansandan Jihohi Na Da Matuƙar Muhimmanci Wajen Magance Matsalar Rashin Tsaro

October 8, 2025
Adadin Kudaden Da Gidajen Sinima Na Sin Suka Tara Yayin Hutun Bikin Ranar Kasa Ya Haura Yuan Biliyan 1.7

Adadin Kudaden Da Gidajen Sinima Na Sin Suka Tara Yayin Hutun Bikin Ranar Kasa Ya Haura Yuan Biliyan 1.7

October 8, 2025
Tinubu

Tinubu Na Son A Saka Hannun Jari Da Kuɗaɗen Fansho A Ɓangaren Mai Da Iskar Gas

October 8, 2025
Gwamnatin Nasarawa Za Ta Hukunta Duk Masu Amfani Da Sinadiran Kamun Kifi Acikin Ruwa

Gwamnatin Nasarawa Za Ta Hukunta Duk Masu Amfani Da Sinadiran Kamun Kifi Acikin Ruwa

October 8, 2025
Sin: Ana Sa Ran Jigilar Fasinjoji Fiye Da Miliyan 21 A Yau Ta Jiragen Kasa

Sin: Ana Sa Ran Jigilar Fasinjoji Fiye Da Miliyan 21 A Yau Ta Jiragen Kasa

October 8, 2025
Kwastam Ta Kama Lita 35,000 Na Man Fetur, Tabar Wiwi Da Sauran Kayayyaki A Kebbi

Kwastam Ta Kama Lita 35,000 Na Man Fetur, Tabar Wiwi Da Sauran Kayayyaki A Kebbi

October 8, 2025
Sin Ta Yi Kira Ga Mambobin WTO Da Su Tinkari Yanayin Tangal-Tangal Tare

Sin Ta Yi Kira Ga Mambobin WTO Da Su Tinkari Yanayin Tangal-Tangal Tare

October 8, 2025
ABU Na Kashe Sama Da Naira Biliyan 4 Duk Shekara A Wutar Lantarki

ABU Na Kashe Sama Da Naira Biliyan 4 Duk Shekara A Wutar Lantarki

October 8, 2025

© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.

No Result
View All Result
  • Gida
  • Labarai
    • Manyan Labarai
    • Kananan Labarai
    • Masarautu
    • Bakon Marubuci
    • Dausayin Musulunci
    • Daga Kasar Sin
    • Nishadi
    • Noma Da Kiwo
    • Sana’a Sa’a
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Taskira
    • Daga Birnin Sin
    • Ado Da Kwalliya
  • Siyasa
  • Wasanni
  • Al’adu
  • Al’ajabi
  • Labaran Kasuwanci
  • Karanta cikin Turanci

© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.

Exit mobile version