Connect with us

LABARAI

Azal Ta Fada Wa Malamai 5 Bayan Sun Yi Wa Dalibarsu Ciki

Published

on

A jiya ne dai rahotanin ke fito wa daga jama’a da dama da kuma wasu daga cikin makarantar kwalejin Waziri Umaru ta tarayya da ke garin Birnin-kebbi cewa, wasu malamai biyar na makarantar sun dirka wa dalibarsu ‘yar aji shida watau ss3 ciki a makarantar wadda aka bukaci a sakaya sunanta.

Wannan matsalar ta yi wa dalibar ciki  dai ta sanya tashin hankali da kuma tsoro ga jama’ar cikin garin na Birnin-kebbi inda iyayen yara suka fara tunanin makomar ‘ya’yansu da ke makarantar. Haka kuma wakilinmu ya yi tataki zuwa makarantar don bincike kan aukuwar wannan matsala da ta shafi shafi malamai biyar da kuma dalibi daya.

A yayin da wakilinmu ya isa makarantar ya samu labarin cewa shugaban makarantar watau” Principal “ Mallam Muhammad Musa Mahuta shi da lafiya lokacin da matsalar ta auku, kuma kawo yanzu yana asibiti domin kula da lafiyarsa. Amma ya samu ganawa da mataimakinsa “Bice Pirncipal” Mallam Oumar Bankano Wouland koye domin jin ta bakin hukumar makarantar kan matsalar yi wa  wannan daliba ciki. Mataimakin shugaban makarantar ya tabbatarwa wakilinmu cewa” Gaskiya ne abin ya auku da dalibarsu kancewar wasu malamai biyar da kuma dalibi daya ana zarginsu da kwanciya da ita har ya zama sanadiyyar hakan ciki ya shiga “. Haka kuma ya ce” hukumar makarantar tuni ta nada kwamitin bincike kan aukuwar lamarin kuma yanzu haka kwamitin ya dakatar da malaman guda biyar da kuma dalibin da ake zargi tare da malaman”.

Daga karshe mataimakin shugaban makarantar ya ce“ ‘yan jarida kudawo wani sati domin samun cikaken rahoton kana bin da ya faru a makarantar ’.

Ya kara da cewa “mutumin da ka ga ya fita ofishina a yanzun nan da ka shigo shi ne sakataren babban kwamitin hukumar kwalejin ta waziri Umaru wanda takarda ce ya kawo min domin hade da rahoton karamin kwamitin da hukumar makarantar ta kafa. Bugu da kari ya ce“ Babban kwamitin zai yi zama ranar Alhamis zuwa juma’a domin fito wa da sakamakon hukuncin da suka zartar kan malaman”. Saboda haka ina rokonku ‘yan jarida cewa ku yi hakuri har zuwa kamala zaman  kwamitin hukumar kwalejin.

A zantarwa da wakilinmu ya yi da mataimakin shugaban makarantar ya ki bayyana sunayen malaman da ake zargi.

 
Advertisement

labarai

%d bloggers like this: