Daga Hussaini Yero, Zamfara,
Wakilinmu ya ruwaito mana cewa, yanzu haka wani lauyan bogi mai suna Chukwuka, ya fada hannun rundunar ‘yansanda ta jihar Zamfara. Lauyan bohin ya fada hannun ‘yansandan ne, sakamakon korafin da kungiyar lauyoyi ta kai wa ‘yansanda, ta hannun shugabanta, Barista Junaidu Abubakar.
Rahoton ya ce, wanda ake zargin ya bayyana a matsayin lauya, a babbar kotun shari’ar Musulinci da ke Tudun Wada, a garin Gusau.
Lokacin da ya shiga hannu aka bayyana masa laifin da ya yi, lauyan bogin sai ya roki kotun ta yi masa afuwa, lokacin da za ta yankr masa hukunci wajen ba shi zabin biyan tara. Ya ce, daure shi, zai jefa iyalinsa cikin tashin hankali, saboda shi kadai ne ke daukar dawainiyar iyalin nasa, ba shi da wani mataimaki.
Lauyan bogin mai kimanin shekara 46 ya ce, dalilin da ya sa ya fada cikin wannan hali shi ne, ya rasa komai nasa, shagunansa guda biyu sun kone, ga shi kuma ya nemi aiki ya rasa, don haka ya yanke shawarar ya yi shiga, irin ta lauyoyi, ya fito a matsayin lauya, ya dinga neman jama’a su ba shi kudi domin ya kare su, da haka kuma yake samun kudin da yake tafiyar da rayuwarsa ta yau da kullum, sai bayan da asirinsa ya tonu.
Da yake yanke hukunci Mai shari’a, Sa’adu Garba Gurbin Bore, ya daure wanda ake tuhumar tsawon wata shida, a tuhuma ta farko ko zabin tara ta naira dubu hamsin, da kuma daurin shekara daya, ba tare da zabin tara ba, a tuhumar da ake masa ta bata suna.