Al-Amin Ciroma 08033225331 (TES Kawai ) ciroma14@yahoo.com
Zancen da ya fi ɗaukar hankula tun bayan dawowar Shugaba Muhammadu Buhari daga taro a ƙasar Turkiyya shi ne zancen maido da Tsohon Shugaban Yi Wa Harkar Fansho garambawul A Nijeriya Malam Abdulrasheed Maina. Mamakin day a fib a ‘yan Nijeriya shi ne a lokacin da Shugaba Buhari ya furta cewa bai ma san zancen dawowa da Mainan kan aikinsa ba.
Irin wannan na ɗaya daga cikin manyan rafkannuwan da maso adawa da gwamnati mai ci ke kallo a matsayin rashin ƙwarewa da tuntuɓe mai wuyar warkewa. Idan dai ba a manta ba, jim kaɗan kafin Shugaban na Nijeriya ya taka ya tafi ƙasar ta Turkiyya, sai da aka tafka wata ‘yar dirama tsakanin Ministan Man Fetur Emmanuel Ibe Kwachikwu da Babban Manajan Daraktan Ma’aikatar, wato Dakta Maikanti Kachalla Baru. Duk da cewa wasu da dama sun goyi bayan ƙorafe-ƙorafen da ministan ya yi a kan daraktansa, wasu kuma na kallon hakan a matsayin wani giɓi da gwamnatin Buhari ke da shi.
Tun ba a ko’ina ba, ‘yan Nijeriya na shaidar manyan tufka da warwara a tsakanin jami’an gwamnati mai ci. Tambayoyin da ke cikin zukatan ‘yan Nijeriya a kullum sun haɗa da; Shin yaushe za a daina kai-komo a tsakanin jami’an gwamnati, har su kwantar da hankali su yi wa talakawa aikin da ya kamata, duba da cewa dududu bai fi ‘yan watanni suka rage mu su a kan zangonsu na farko ba? Har ila yau, wanne mataki Shugaba Buhari zai ɗauka don tabbatar da yi wa jami’an gwamnatinsa garambawul? Me ya sa har yanzu gwamnatin ba ta daidaita a kan kyakkyawar siraɗi ba?
Bari mu dawo kan zancen Malam Abdulrasheed Maina. Shin wace irin gwamnati ake yi a Nijeriya a yanzu? Ina dokokin tsari na ɗauka da korar ma’aikata? Ta yaya har babban darakta kamar Maina, ya dawo bakin aiki, ba tare da an tabbatar da dokokin ɗaukar aiki a kansa ba? Ko kuwa har yanzu ba mu da manyan ƙwararru ma su sa idanu kan dokokin ƙasa? Har ila yau, zancen na Maina ya haɗo da Ministan Shari’ah Abubakar Malami, ta yaya abin ya faru?
Idan ba haka ba, ta yaya za a wayi gari Ministan Cikin Gida Abdulrahman Bello Dambazau da Shugabar Ma’aikatan Gwamnatin Tarayya Winifred Oyo-Ita, su riƙa sukar juna, tare da ƙaryata junansu a kan zancen wane ne ya maido da Maina bakin aiki? Har ila yau, wasu masu ƙorafin sun ayyana sunan ministan Shari’ah a ciki, da yamaɗiɗin cewa wasu ne daga fadar shugaban ƙasa suka nemi a dawo da Mainan. A sani cewa ‘yan Nijeriya sam ba sa kallon wannan musayar yawun da waɗannan manyan jami’an ke yi a matsayin ci gaba, illa kawai ci baya ne ga ƙasar baki ɗaya.
Ƙwarai Maina ya koma bakin aikinsa tun ba yau ba. Idan har ta tabbata Oyo-Ita a matsayinta na shugabar ma’aikatan gwamnatin tarayya, za ta fito bainar jama’a ta bayyana cewar ba ta san Maina ya komo bakin aiki ba, tabbas da lauje a cikin naɗin! Haka shi kansa Minista Dambazau, shin idan har Malam Abdulrasheed Maina, ya koma bakin aikinsa a ma’aikatar harkokin cikin gida, inda Alhaji Dambazau yake jagoranta, sannan bai san hawa ba, kuma bai sauka ba, kamar yadda ya furta, to sai mu ce; ina gizo ta yi saƙar?
Rahotanni dai tuni sun bayyana cewa Shugaba Muhammadu Buhari ya harari wannan lamari tare da nuna rashin jin daɗinsa kan lamarin na Maina, har ma ya kafa kwamitin bincike a kai. Ba wannan kaɗai ba, har ma ya bayar da umarnin gaggauta korar tsohon shugaban kwamitin yi wa harkar Fansho garambawul ɗin.
Idan ma ba a manta, Maina ya gamu da fushin hukumomi a yayin da aka zarge shi da almundahanar zunzurutun kuɗi har naira bilyan 100 na daga cikin kuɗaɗen ‘yan fansho, ya kuma bar aikinsa ya, har aka daina jin ɗuriyarsa, sai kwanan nan kwatsam aka ji ya dawo bakin aikinsa. Hukumar da ke yaki da masu yi wa tattalin arzikin Nijeriya zagon ƙasa (EFCC) ta fara neman Abdulrasheed Maina ruwa-a-jallo ne a shekarar 2015 kan zargin yin sama da fadi da naira bliyan biyu cikin kudin yin garambawul wa tsarin fanshon Nijeriya.
Sai dai kuma duk mai bibiyar lamarin na Maina zai tabbatar da cewa a shirye tsohon shugaban kwamitin yake ya fasa ƙwan da ake zarginsa a kai. Saboda bincike ya nuna a lokacin da yake bisa aikinsa na kwamitin, Maina yana aiki ne tare da wasu jami’ai daban daban na gwamnati, waɗanda suka haɗa da jami’an hukumar EFCC guda 16, jami’an hukumar binciken ICPC 16, haka kuma jami’a guda huɗu daga hukumar bincike ta SSS da jami’an hukumar binciken NIA guda biyu, da kuma jami’a 15 daga ma’aikatar kula da harkokin ma’aikata, a yayin da shi kuma Abdulrasheed Maina ya kasance shugaban kwamitin. Kenan dukkanin abin da zai wakana a kwamitin sai ya bi kan teburin dukkanin jami’an nan da muka lissafa kafin shi shugaban ya sa hannu a kan kowane irin ƙuduri.
Har wa yau, Maina ya ce ba a taɓa ware wa kwamitinsa ƙwandala ɗaya don gudanar da ayyukansa ba, kuma ya ce ba a taɓa keɓe wa kwamitinsa naira goma na kasafin kuɗin Nijeriya ba, amma duk da haka ya ci nasarar ƙwato wa ƙasar nan zunzurutun kuɗi har naira Bilyan 282, waɗanda aka sace, kuma ya mayar da su a lalitar gwamnati. Sannan ya bayyana cewa ba ya daga cikin waɗanda ke da haƙƙin sa hannu wajen fitar da kuɗi daga wancan asusun ajiyar da aka sanya kuɗin.
A gefe guda kuma, bayan Shugaba Buhari ya bayar da umarnin tabbatar da bincike na musamman a kan harkar Maina da badaƙalar da ake tuhumarsa da aikatawa, akwai kuma buƙatar yi wa rashin ƙwarewar da jami’an gwamnati ke nunawa a yanzu.
Ba daidai ne a kawar da kai daga zancen neman bahasin wanda ya maido da Maina bakin aiki ba. Tuni dama ministan na harkokin cikin gida ya nesanta kansa da zancen, a yayin da ita ma shugabar ma’aikatan Nijeriya ta yi tsalle zuwa gefe guda, tare da nuna wa Dambazau yatsar cewa ya sharara ma ta zuƙi-ta-malle!
Tabbas, akwai abubuwan da ‘yan Nijeriya ke da haƙƙin sani a kan waɗannan lamura na kwan-gaba-kwan baya da wasu manyan jami’an gwamnatin Buhari ke yi. Shin a tsakanin Dambazau da Oyo-Ita, da kuma Ministan Shari’ah Malami, wane ne ke mai gaskiya?