Sulaiman Bala Idris0703 666 6850
Kuma matuƙar a ka ci gaba da zuba ido, wannan gagarumar matsala ta na hauhauwa tamkar farashi, za a sha mamaki. Gwamma ma tun da wuri, mu farka, mu daina yaudarar kawunanmu, da iyalanmu, da danginmu, da ƙabilarmu, da al’adarmu, da yankinmu, da ƙasar mu. Idan kuma kunnuwanmu ba a shirye suke da jin gargaɗi ba, ga fili nan ga mai doki, jiki magayi.
Na tsimu sosai, a ƙarshen makon da ya gabata. Hankalina ya tashi yadda ya kamata. Har sai da ta kai zuciyata ta bar komi, ta koma saƙe-saƙe da sawwale-sawwale. A wani tunani da na yi nisa cikinsa kuwa, ƙwaƙwalwata cewa ta ke yi; ‘An mayar da hankali wurin yaƙin Shekau da ƙungiyarsa ta Boko Haram, amma kuma a aikace, a hankalce, yanayin da ƙasar ke ciki, tamkar wani sharar fage ne ga duk wani nau’in aikin Shekau ko ta’asa da ɓarna su zo su zauna daram!’
Wata jarabawa ko in ce gwaji na halarta, bayan na samu nasarar tsallake matakin farko na tantance wa. Tun farko an bi matakan tantance wa ne, ta hanyar matakin digiri na farko. Tun a nan, ana tsammanin za a samu rangwamen adadin waɗanda za su halarta. Aka tsallake wannan. Aka yi jarabawa kashi na biyu.
A wannan wurin gwaji ne na ga abin mamaki. Matasa majiya ƙarfi, da ‘yan mata sun yi cincirindo. Mafi yawa ’ya’yan manya ne. saboda basu yi kama da waɗanda ke jin yunwa ba. Saboda tsabar yawan da muke da shi, sai da ta kai an rarraba gwajin gida biyu. Kason farko suka fara yi da safe. Mu kuma kaso na biyu, muka yi da rana.
Waɗanda idanuwa na suka iya gani, sun fi mutum 200. Wannan banda waɗanda suka zauna a gwajin kaso na farko fa kenan. Su ma Allah kaɗai ya san adadinsu.
Babban abin da ya tada min hankali shi ne, a duk fa waɗannan adadin, mutum biyar kacal ake buƙata. Amma sama da 200 sun halarta, kuma duk sun cancanta a matakin kwalin karatunsu na jami’a. kowa da ka gani a wurin kwalin digiri mai daraja ta biyu zuwa sama yake da ita.
Lokacin da muka shiga ciki. Sai wani a kusa dani yake ce min, wannan ai da sun nemi wata hanyar tantance wa ba sai duk mutanen nan sun halarci gwajin ba. Na yi shiru, ina saurarensa. Ni dai mamaki da takaicin irin matsalar da ke fuskantarmu nake yi. Yayin da wannan bawan Allah ya cika ni da surutu, sai na ce mishi, ai haka ma, don mutane ba su samu sanarwar wannan lamari yadda ya kamata bane. Kuma an ɗan taƙaita sanarwar a tsakankanin ‘yan uwa da abokan arziki, sai kuma waɗanda suka ci sa’ar cin karo da sanarwar a kafafen sada zumunta bisa tsautsayi. Idan da an sani sosai, adadin waɗanda zasu tsallake matakan farko da na biyu sai sun fi 5,000.
Ko da na lura wannan bawan Allah ya samu natsuwa da kalamai na, sai na ci gaba da jawabi a salo irin na masana kimiyyar zamantakewa da halayyar jama’a. na tambaye shi, me ya fahimta da wannan dandazo na matasa, waɗanda kuma suna sane cewa mutum biyar kacal ake nema? Sai ya ce, kowa na son samun gurbin karatu ne zuwa Turai.
Amsarsa ba ta gamsar da ni ba. Don haka na kaɗa kai, alamun ba haka bane. Sai ya ce, to mene ne? na ce, wannan kaɗai ya ishi ya yi wa mutum bayanin halin da Nijeriya ke ciki. Irin matsalar da ke fuskantar wannan ƙasa, irin barazanar da za a iya tsinta kai a ciki, matuƙar ba a farka an yi mai yiwu wa ba.
Nijeriya, wata ƙasa ce da ake wasa da ƙarfin matasa, ta hanyar wasa da rayuwarsu da nuna musu halin ko-in-kula. Wanda kuma duk wata ta’asa da za a so ɗorewarta a cikin al’umma, ana shigar da ita ne, ta samu muhalli a zukatan matasa.
A lokacin da ya zama, matasa da iyayensu na ƙaunar yin karatun. Maimakon gwamnati da masu mulki su ƙarfafa musu gwiwa su ilimanta, ko don a rage yawan jahilai da daƙiƙai a tsakankanin al’umma, sai ya zama abin ba haka bane. Sai ma aka yi ta ƙirƙiro wasu munafukan matakai da suke kasance wa Katanga tsakanin ‘ya’yan talakawa da karatu.
Tsaurin da matakan shiga jami’a ke da ita ya sa ’ya’yan talakawa da yawa suke tuƙe wa a matakin karatu na Sakandare. Sai su ɓuge da leburanci, kabu-kabu ko jagaliyar siyasa, da satar Agwagwa.
A na yi wa matasa irin wannan wulaƙanci da cin mutunci, me zai hana ba za a ci gaba da samun majiya ƙarfi suna sace-sace da sunan garkuwa ba. Saboda ai matashi na da buƙatu na rayuwa, sha’awarsa a zabure take, haka ma shauƙinsa. Yana kallon irin rayuwar jin daɗi da wasu ke yi, shi ma yana son irinta. Idan an hana mishi kai wa wannan mataki ta halastacciyar hanya, zai lalubo mafita ta haramtacciya.
Kuma da zaran an bari matashi ya gano haramtattun hanyoyi, kowa sai ya ɗanɗana kuɗarsa. Babu wanda zai tsira, talakawa da masu kuɗin kaf ɗinsu sun shiga uku. A ɓangaren talakawa, ƙatti ne (matasa masu zaman banza) za su yi ta yi wa ‘ya’yansu fyaɗe saboda basu da kuɗin yin aure. Masu kuɗi kuma a yi ta sace su, ana sace ‘ya’yansu (garkuwa). Gwamnati kuma a dagula mata lissafi, ta rasa alƙibla, wannan ita ce gagarumar matsalar.