Leadership Hausa Newspapers
No Result
View All Result
  • LABARAI
  • WASANNI
  • RAHOTANNI
  • SIYASA
  • KASUWANCI
  • ADABI
  • RA’AYINMU
  • TATTAUNAWA
  • BIDIYO
  • MAKALAR YAU
  • LABARAI
  • WASANNI
  • RAHOTANNI
  • SIYASA
  • KASUWANCI
  • ADABI
  • RA’AYINMU
  • TATTAUNAWA
  • BIDIYO
  • MAKALAR YAU
No Result
View All Result
Leadership Hausa Newspapers
No Result
View All Result
Home MAKALAR YAU

BAƘON MARUBUCI: Gwamnatin Ganduje: Ko Kwalliya Na Biyan Kuɗin Sabulu?

by Tayo Adelaja
October 21, 2017
in MAKALAR YAU
4 min read
WhatsAppShare on FacebookShare on TwitterShare on Telegram

Abdullahi Muhammad Sheka

Tun bayan da mai girma Dakta Abdullahi Umar Ganduje ya samu ikon dafe madafun ikon mulkin Jihar Kano, gwamnatin tasa ta shirya samar da abubuwan da ake zaton za su kawo ƙarshen matsalolin da Kanawa suka jima suna fama da su. Duk da tulin basukan da Gwamna Ganduje ya tarar da kuma ma’aikatan da ya gada waɗanda ba a fara biyan su ba, sannan kuma ga abubuwan da ba gaira ba dalili ke zuƙe lalitar Gwamnati, amma Gwamna Ganduje ya yi rawar gani musamman yadda ya zaƙulu haziƙan mutune waɗanda aka ɗora akan muƙamai daban daban.

samndaads

Misali idan aka ɗauki Kwamishinan yaɗa labarai Malam Muhammad Garba wanda saboda kishin Kano da Kanawa ya sa yana riƙe da muƙamin shugaban ƙungiyar ‘yan Jaridu na Afrika, sannan kuma shugaban  ƙungiyar ‘yan Jarida a Nijeriya, amma ya ajiye duk waɗannan ayyuka ya komo gida ya karɓi muƙamin kwamishina don ya bautawa al’ummarsa.

Ɗarewarsa kan wannan muƙami ya samar da dandamalin da aka samu ikon warware matsalolin isar da saƙonni zuwa ga al’ummar, waɗanda suka yi uwa suka kuma yi makarɓiya wajen sahallewa Gwaman Ganduje jagorantar Dimukaraɗiyyar Kanawa.

Kwamishinan Yaɗa labarai na Jihar Kano Malam Muhammad Garba a lokacin da yake yiwa Jaridar LEADERSHIP Hausa ƙarin haske, ya bayyana cewar mai girma Gwamna Ganduje bai fiya son yawaita surutu ba, musamman kasancewar ayyukan da gwamnatinsa ke aiwatarwa ko makaho ya san ta ciri tuta, ya ce dubi aikin gadar ƙasa dake kan titin zuwa Madobi, haka kuma ga aikin gadar da ake a titin Katsina wanda aikin zai sauƙaƙawa matafiya  a cikin birni da masu fita waje wanda wata hanya ta bunƙasar harkokin tattalin arziƙin Kano da Ƙasa bakiɗaya.

Haka lamarin yake batun samawa matasa ayyukan yi, akwai batun matasa 100 da aka tura koyon gyaran mota irin na zamni tuni sun kammala samun  horo wanda yanzu haka rayuwarsu ta samu canji a fagen dogaro da kai, ga kuma  wani kason na mutane 150, maza 100 mata 50 suna kan hanyar tafiya Kaduna domin samun irin wannan horo.

Idan kuma aka dawo ɓangaren ma’aikata, jihar Kano na daga cikin jihohi bakwai da suka yiwa sauran fitinkau wajen iya sauke nauyin da hau kansu, musamman batun biyan haƙƙi ma’aikata, watau albashi wanda ake cewa ba su ka huta. Yanzu haka batun samar da ƙarin gidaje masu rangwamin farashi domin amfanin masu ƙaramin ƙarfi na nan gwamnatin Gaduje ta mayar da hankali a kansu.

Su ma mata gwamnatin Ganduje ba ta manta da su ba domin an koyawa mata sana’ar tuƙin mota a tsarin gwamnatin Kano mai taken Kano Ƙalƙal, wannan shiri shi ne irinsa na farko a tarihin Jihar Kano har da ƙasa bakiɗaya. Akwai abubuwa masu yawa da gwamnatin Ganduje ta yiwa iyaye mata ta ƙarƙashin ma’aikatar mata ta Jihar Kano.

Harkar lafiya, Gwamnatin Ganduje ta himmatu wajen ci gaba da shirin inganta kiwon lafiya ta hanyar aiwatar da shirin nan na saɓar ta juye ta, wanda ke bada dama ga marasa lafiya su samu magunguna masu kyau kuma cikin farashi mai sauƙi a asibitoci mallakar gwamanti da ke cikin birni da karkara.  Sai kuma aiwatar da allurar rigakafin cutar shan-inna da makamantansu, domin samun al’umma mai cike da ƙoshin lafiya.

Domin ganin an dawo da kima da mutuncin jam’iyya da shugabancin ta, gwamna Ganduje ya jagoranci taron ɗaukacin masu ruwa da tsaki da duk masu riƙe da madaffun iko musamman masu kishin ci gaban Kano da Jam’iyyar APC, taron da aka gudanar a Sokoto an tattauna muhimman batutuwa kuma laya ta yi kyan rufi. Kusan ƙananan hukumomin jihar Kano 44 na rige-rigen yin mubaya’a da sabon shugabancin jam’iyya, wanda a halin yanzu ke tsare-tsaren ɗora jam’iyyar a sirdi domin tunkarar zaɓen shekara 2019. Hakan ce ma tasa ake ganin kullun jam’iyyar APC a Kano na yin ɗauki ɗaiɗai a wasu jam’iyyun adawa a Kano, inda  a wannan satin aka karɓi ruwa Baba watau tsohon mataimakin Gwamnna Injiniya Tijjani Muhammad Gwarzo, inda ya ce tafiyarsa da Ganduje ta yi daidai, a cewarsa sun zama takalmin kaza.

Haka ma Lawan Shehu Bichi tsohon shugaban ƙaramar hukumar Bichi sannan kuma tsohon wakilin majalisar wakilai ta tarayya ya ce shi ma yabi.

Kamar yadda aka sani kowace gwamnti na da irin nata salon mulkin don haka shima Gwamna Ganduje haka yake, kuma alhamdulillahi Kanawa tuni suka fara kwankwaɗar irin wannan romon dimukraɗiyya a tsarin shugabancinsa duk kuwa da irin ƙalubalen da yake fuskanta musamman na matsin tattalin arziƙi da kuma ɗinbin basukan da ya gada, amma hakan bai hana shi samar da ci gaban da ake buƙata cikin gaggawa a ɓangarorin da suka haɗar da harkar tsaro, Ilimi da kuma samar da abubuwan more rayuwa a birni da karkara, Gwamna Ganduje ya tabbatar da rubuta sunansa a tarihi bisa  ta fuskar ci gaba da ayyukan da gwamnatocin baya suka bari.

Akwai halayen gwamna Ganduje wanda abin koyi ne kuma abin yaba wa ne, shi ne gwamna ɗaya tilo da ke halartar duk wani bikin da aka gayyace shi wannan kuwa ya haɗar bikin talaka ko mai kuɗi.

SendShareTweetShare
Previous Post

‘Ya Kamata Nijeriya Ta Kai Matakin Kusa Da Ƙarshe A Gasar Kofin Duniya

Next Post

Muna Son Kafa Masana’antar Dogaro Da Kai Amma Ana Neman Hana Mu —Shugaban Naƙasassu

RelatedPosts

Sulhu Da ‘Yan Bindiga: Me Ya Sa Sheikh Gumi Na Tufka Wasu Na Warwara?

Sulhu Da ‘Yan Bindiga: Me Ya Sa Sheikh Gumi Na Tufka Wasu Na Warwara?

by Sulaiman Ibrahim
7 hours ago
0

Ni da ma tun da farko ban taba tunani ko...

Rance

Kura-kuren Da Hukumomi Ke Yi Wajen Bayar Da Rance

by Muhammad
2 days ago
0

Daga Aliyu M. Kurfi (PhD), Ya kamata mu sani cewa...

Ilimi

Satar Dalibai Ko  Kassara Ilimi A Arewa?

by Muhammad
4 days ago
0

alimailafiyasunusi@gmail.com - 08036064695: A yanzu babu abinda ya fi jan...

Next Post

Muna Son Kafa Masana’antar Dogaro Da Kai Amma Ana Neman Hana Mu —Shugaban Naƙasassu

Leave a Reply Cancel reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Domin sanya talla ko karin bayani a tuntube wannan numbar +2348126152609.

ADVERTISEMENT
  • LABARAI
  • WASANNI
  • RAHOTANNI
  • SIYASA
  • KASUWANCI
  • ADABI
  • RA’AYINMU
  • TATTAUNAWA
  • BIDIYO
  • MAKALAR YAU
Advertise with us

© 2020 Leadership Group .

No Result
View All Result
  • LABARAI
  • WASANNI
  • RAHOTANNI
  • SIYASA
  • KASUWANCI
  • ADABI
  • RA’AYINMU
  • TATTAUNAWA
  • BIDIYO
  • MAKALAR YAU

© 2020 Leadership Group .

Go to mobile version