Ba A Dauki Matakan Kare Lafiyarmu Ba – Likitoci

A makon da ya gabata ne shugaban Likitoci na Asibitin koyarwa na Jami’ar Legos, Farfesa Chris Bode, ya shelanta cewa sun horas da Likitoci da wasu masu bayar da gudummawa a kashin kansu har gida 120 a kan yanda za su shiga yakin fafatawa da annoar Koronabairus. Sai kuma ga wasu rahotanni daga Likitocin suna musanta wannan maganar.

Likitocin a Asibitin koyarwar na Jami’ar ta Legos sun yi zargin cewa an tilasta masu ne aka shigar da su a cikin yaki da cutar ta Korona a matsayin wai masu bayar da gudummawa ta kashin kansu. Kamar yanda wasu daga cikin Likitocin wadanda ba su so a bayyana sunansu a nan ba, suka nuna. Sun nuna kaduwa da mamakinsu a lokacin da suka ji sunayensu a matsayin wai wadanda suka amince su bayar da gudummawar a radin kansu Likitocin suka bayyana cewa, an yi hakan ne ba tare da an tuntube su ba.

“An dai kira mu ne domin wai a yi ma na wasu bayanai kawai, a hakan ne a hukumance aka tilasta ma na yin wannan aikin. Majiyar Likitocin ta bayyana cewa tsoron a yi masu bi-tada-kulli ne ya sanya su karban aikin da aka dora masu ala tilas, amma ba da son ransu ne ba.”

Wani likitan kuma cewa ya yi, an tilasta su shiga aikin ne alhalin ba wani abu da a ka yi na kokarin ganin an kare tasu lafiyar ballantana ma a yi maganar a kyautata masu.

“Ko da za mu gamu da hadarin mutuwa a cikin wannan aikin ko kuma na kamuwa da cutar, sam babu wani abu da aka tanadar ma na. Tabbas kamata ya yi Likitoci su kasance a sahun gaba wajen yaki da wannan annobar, amma ba wani abu da a ka tsara na kare tamu lafiyar daga kamuwa da annobar ta COVID-19.

“Kusan kullum sai na yi kuka tun daga lokacin da na ga sunana a matsayin wai wadanda suka sadaukar su bayar da gudummawarsu. Idan da a ce su hukumomin sun nuna damuwarsu a kan kare tamu lafiyar daga kamuwa da wannan annobar, sam ba wanda zai nuna wata damuwa a kan aikin.

“Abin ma da ake biyanka a kan aikin sam bai taka kara ya karya ba. misali a nan Asibitin koyarwan na Jami’ar Legos, a matsayinka na Likita in da za ka kwanta rashin lafiya ba wani abu da za a biyaka baccin albashinka.” Kamar yanda wani likitan ya yi zargi.

Likitan ya kuma ci gaba da bayyana cewa, yanda kuma za a kula da duk wani marar lafiya da ya zo daga waje, kai ma Likitan iyaka abin da za a yi maka kenan.

“A wannan annobar ba wani da ya fito ya ce in har da Likita zai kamu a dalilin aikinsa ga wani abu na musamman da za a yi masa, ba wanda ya yi wani bayani a kan hakan.

“Da irin haka muka yi rashin A ranar Alhamis da ta gabata Ministan lafiya, Dakta Likitoci masu yawa a zamanin cutar zazzabin Lassa. An yi wa daya daga cikin manyan Likitocinmu ma kisan gilla, amma ba na jin akwai wani abu na musamman da aka yi wa iyalansa.

Wata Likitar kuwa bayyana irin damuwar da mijinta yake da shi ta yi a kan wannan aikin nata. “Ba kuma ni kadai ba, yawancin ‘yan’uwana Likitoci mata duk suna tattare da wannan matsalar.

“A duk lokacin da na shirya zuwa wajen aiki, haka nake ganin alamun damuwa a fuskar mijina da ‘ya’yana. Suna masu cike da tsoron abin da ka iya samuna alhalin ba wani tanadi da aka yi a gareni,’’ In ji Likitar.

Wata kwararriyar Likita Asibitin koyarwar na Jami’ar Legos cewa ta yi, na taba kiran hukumomi a Jihar ta Legos a waya domin jin tanadin da aka yi mana a matsayinmu na masu bayar da gudummawa, amma na girgiza a lokacin da hukumomin suke shaida mani cewar babu wani tanadi a kanmu.

“An dai shaida mani cewar wai na dai yi ne domin Allah,” in da ta fadi hakan a fusace. Amma sai ga shi suna fitar da bilyoyin naira a kullum wai da suan yaki da wannan annobar.

“Sam ba su dauki Likitoci da sauran ma’aikatan lafiya a matsayin mutane ba. a matsayina na kwararriyar Likita a kullum ina jefa kaina a cikin hatsari kala-kala wanda sam ba domin shi ne aka dauke ni aiki ba, amma wai suna cewa wai na yi domin Allah.

Osagie Ehanire, ya girgiza Kakakin Majalisar wakilai ta tarayya, Femi Gbajabiamila, a lokacin da ya ce masa ba shi da masaniyar wani kyautatawa da aka tanadar wa Likitocin da ke cikin yaki da wannan annobar ta COVID-19.

A cewar Ministan, wai sadaukarwa a lokaci irin wannan shi ne daman aikin na Ma’aikatan lafiyan a kullum. Kakakin Majalisar, Gbajabiamila, sai ya nuna masa rashin amincewarsa a kan hakan, sannan ya yi masa nuni da cewa, “Na yi tsammanin ka ce mani Koronabairus annoba ce? To ta ya hakan kuma zai zama aikinsu na yau da kullum?”

Exit mobile version