CRI Hausa">
Leadership Hausa Newspapers
No Result
View All Result
  • LABARAI
  • WASANNI
  • RAHOTANNI
  • SIYASA
  • KASUWANCI
  • ADABI
  • RA’AYINMU
  • TATTAUNAWA
  • BIDIYO
  • MAKALAR YAU
  • LABARAI
  • WASANNI
  • RAHOTANNI
  • SIYASA
  • KASUWANCI
  • ADABI
  • RA’AYINMU
  • TATTAUNAWA
  • BIDIYO
  • MAKALAR YAU
No Result
View All Result
Leadership Hausa Newspapers
No Result
View All Result
Home DAGA BIRNIN SIN

Ba A Fafe Gora Ranar Tafiya…

by CRI Hausa
December 29, 2020
in DAGA BIRNIN SIN
2 min read
Ba A Fafe Gora Ranar Tafiya…
WhatsAppShare on FacebookShare on TwitterShare on Telegram

A baya bayan nan ne aka gudanar da ranar shiryawa tunkarar annoba ta duniya da majalsiar Dinkin Duniya ta ware. Manyan annoba kamar cututtuka masu yaduwa, irinsu COVID-19 da Ebola da sauransu, na mummunan tasiri ga harkokin rayuwa da ci gaban tattalin arziki cikin lokaci mai tsawo. Irin wadannan cututtuka kan kawo matsi kan tsarukan kiwon lafiya da tsaiko kan harkokin samar da kayayyakin bukatu da jefa rayuwar bil adama cikin mawuyacin hali, baya ga tsananta yanayi a kasashe da yankuna matalauta da kuma mutane masu rauni.

samndaads

Wannan rana a bana, ta zo a lokacin da ya dace na kara tunatar da cewa, akwai bukatar gaggauta samar da ingantattu tsarukan kiwon lafiya masu juriya, wadanda za su isa ga dukkanin mutane dake da rauni ko marasa rauni.
A yayin da aka rasa hadin gwiwa tsakanin kasa da kasa, illar da annoba za ta yi a nan gaba ka iya fin wadanda aka gani a baya ta fuskar tsanani da karfi. Akwai matukar bukatar kara wayar da kan al’umma da musayar bayanai da dabaru da ilimin kimiyya da ilimi mai inganci, tun daga matakan kananan hukumomi, zuwa jihohi da kasa da kasa da yankuna da ma duniya baki daya, a matsayin hanya mafi nagarta ta kandagarki da tunkarar annoba.
Hadin gwiwa tsakanin kasashen duniya zai taka muhimmiyar rawa wajen shiryawa tunkarar annoba. Ya kamata a fahimci karfin hadin gwiwa da taimakekeniya tsakanin daidaikun mutane da al’ummomi a dukkan matakan tunkarar annoba, tun kafin isowarta.
Har ila yau, ya kamata kowa da kowa daga kan daidaikun jama’a zuwa gwamnatoci da sauran masu ruwa da tsaki, su san hakkin da ya rataya a wuyansu da kuma rawar da su taka wajen kawar da aukuwar annoba, ko daukar matakan kandagarki da na dakile ta.
Barkewar annobar COVID-19 a bana, ya nunawa duniya cewa, babu wani wuri da zai tsira muddun wani bangare na fuskantar annoba ko kalubale, kana ya nuna cewa kowa yana da rawar takawa wajen kare ta’azzarar cutar. Sannan ya nunawa gwamnatocin da ba su mayar da hankali kan inganta rayuwar al’ummominsu ba, illar dake tattare da rashin yin haka. Don haka, akwai bukatar kara zage damtse da shirin ko ta kwana, don rage irin illolin da ake fuskanta a yanzu, maimakon ta’azararsu, idan duniya ta kuma fuskantar wata annobar mai kama da wadda take fuskanta a yanzu. (Fa’iza Mustapha)

SendShareTweetShare
Previous Post

Kawar Da Talauci Bisa Shirin Da Aka Tsara A Sin Ya Haskaka Yanayin Da Duniya Take Ciki

Next Post

Xi Jinping: Ya Kamata A Kara Dora Muhimmanci Kan Batutuwan Aikin gona, Kauyuka Da Manoma

RelatedPosts

Matasan Sin Da Afrika Sun Tattauna Da Nufin Inganta Kare Halittu

Matasan Sin Da Afrika Sun Tattauna Da Nufin Inganta Kare Halittu

by CRI Hausa
8 hours ago
0

Matasan Sin da Afrika, sun gudanar da wani taro ta...

Alluran Rigakafin Kasar Sin Sun Sanya Kwarin Gwiwa Kan Yaki Da Annobar COVID-19 A Kasashe Da Yankuna Masu Yawa

Alluran Rigakafin Kasar Sin Sun Sanya Kwarin Gwiwa Kan Yaki Da Annobar COVID-19 A Kasashe Da Yankuna Masu Yawa

by CRI Hausa
8 hours ago
0

Annobar numfashi ta COVID-19 na ci gaba da yaduwa a...

Alluran Rigakafin Cutar COVID-19 Na Kasar Sin Na Taimakawa Kasashe Da Dama Yaki Da Cutar

Alluran Rigakafin Cutar COVID-19 Na Kasar Sin Na Taimakawa Kasashe Da Dama Yaki Da Cutar

by CRI Hausa
8 hours ago
0

A baya-bayan nan, wasu kasashe da yankuna sun amince da...

Next Post
Xi Jinping: Ya Kamata A Kara Dora Muhimmanci Kan Batutuwan Aikin gona, Kauyuka Da Manoma

Xi Jinping: Ya Kamata A Kara Dora Muhimmanci Kan Batutuwan Aikin gona, Kauyuka Da Manoma

Domin sanya talla ko karin bayani a tuntube wannan numbar +2348126152609.

Leadership Epaper
ADVERTISEMENT
  • LABARAI
  • WASANNI
  • RAHOTANNI
  • SIYASA
  • KASUWANCI
  • ADABI
  • RA’AYINMU
  • TATTAUNAWA
  • BIDIYO
  • MAKALAR YAU
Advertise with us

© 2020 Leadership Group .

No Result
View All Result
  • LABARAI
  • WASANNI
  • RAHOTANNI
  • SIYASA
  • KASUWANCI
  • ADABI
  • RA’AYINMU
  • TATTAUNAWA
  • BIDIYO
  • MAKALAR YAU

© 2020 Leadership Group .

Go to mobile version