Gwamnatin jihar Bauchi ta karyata labaran da ke cewa gwamnan jihar Bauchi, Sanata Bala Muhammad Abdulkadir na can kasar London kwance shame-shame a asibiti inda ke neman lafiyarsa biyo bayan wata rashin lafiyar da ta rufke shi.
A cikin wata kwafin sanarwar manema labaru da Kakakinsa, Alhaji Muktar Gidado ya fitar, ya bayyana cewar labaran da suka bazu na cewar gwamnan jihar na kwance a asibiti ba gaskiya ba ne, yana mai fadin cewar wasu da suka yi ta amfani da kafafen sadarwar zamani sun yi ta yada cewar gwamnan ba zai dawo jihar da wuri ba sakamakon rashin lafiyar da take damunsa, inda ya ce ‘yan adawarsu ne kawai ke yada hakan.
Sai dai Gidado ya tabbatar da cewar gwamnan ya bar jihar ne zuwa London a bisa ganawar sa’o’i da yake da shi da Likitan shi wanda tunin suka gana kan dalilin hakan.
Idan za ku iya tunawa dai, an yada cewar gwamnan na kwance a wata asibiti a kasar London kan wata rashin lafiyar da ba a bayyana ta ba, lamarin da ya bazu a daren da za a je kotun Koli domin yanke shari’ar da ke tsakaninsa da tsohon gwamnan jihar Muhammad Abubakar kan kujerar na gwamnan Bauchi, lamarin da wasu suka jingina da fargabar hukuncin da zai biyo ba, sai dai gwamnatin jihar ta yi watsi da zancen.
Sanarwar tana cewa; “Hankulan gwamnatin jihar Bauchi ya karkata kan wasu labaran kanzun kurege da wasu bata gari ke yadawa da ke cewa gwamna Bala Abdulkadir Muhammad yana kwance a gadon asibiti wai ba zai iya dawowa a kwanan nan domin ci gaba da aikin shugabanci da ke gabansa ba,”
Sanarwar ta ce, wasu mambobin jam’iyyar adawa sun fake da cewar gwamnan ya tafi kasar London da kwanciya a asibiti ne kawai don fargabar yanke hukuncin da ke gabansu, wanda ya ce sam zuki ta malli ce hakan ma.
SSA na Media na gwamnan ya daura da cewa; “Ina son in shaida muku cewar wadannan bayanai suna zuwa ne kawai ta hanyar jita-jita da shaci-fadi,”
“Gwamna ya tafi ne a bisa ganawar da yake da shi da Likitansa, a bisa wani karamin dalili, bayan da ya gana da likitansa a wannan ranar ma ya koma masaukinsa.
“Ma’abota kafafen sadarwar zamani sun gani an tura gwamnan yana hutawa cikin farin ciki da annashuwa.
“Ina tabbatar wa illahirin al’umman jihar Bauchi cewar gwamnanmu zai dawo jihar nan ba da jimawa ba, kamar ma yadda shi da kanshi ya nuna hakan a soshal midiya a safiyar yau,”
Sanarwar ta Muktar Gidado ta kuma shaida cewar gwamnan ya aike da sakon jinjina a bisa du’a da jama’a da makusanta da suka yi ta kiransa a waya gami da masu aike masa da sakon karta kwana domin gaisheshi da tattaunawa da shi musamman masoyansa da suke jihar Bauchi da masu masa fatan alkairi a kasar nan, ya yaba musu dukka kan hakan.
Daga nan sai Gidado ya nemi jama’a da su yi watsi da wancan batun na farko