An danganta ta’azzarar tsadar Albasa da aka samu a bana da cewa ya farune saboda yanayi da aka samu ta matsalar nomata da aka samu wasu wuraren basu kai ba. Shugaban kungiyar ‘yan Albasa na kasuwar karfi a Gundutse, Alhaji Musa Karfi ya bayyana hakan ga manema labarai.
Ya ce, su dai tunda suka harkar Albasa basu taba ganin lokacin da aka samu darajar tsadar Albasa Lamar wannan lokaci ba da takai ‘yan kwanakin baya sai da aka saida Buhun Albasa N60,000 wanda a yanzu nema da tayi saiki make samun buhunta a N40,000.A kudancin kasarnan kuwa said a aka rika saida Buhun Albasa akan N110,000 yanzu da tayi dan sauki make sayarwa N70,000. Albasa saida ta nemi tafi karfin masu dan saye na karamin bukatunsu.
Ya ce za’a iya samun kyakkyawan cigaba idan manoman Albasa basu samu taimako daga Gwamnati kamar yanda sukasa rai za a tallafa musu amma uwar kungiyar ‘yan Albasa ta kasa da akace an baiwa Kudi basu baiwa na kasa ba da zai yi noma.
Ya ce, akwai tallafi da akace za’a basu an bayar a hannun kungiyar ta kasa amma daga baya ba’a san India suka yi ba.
Ta yi nuni da cewa yanzu noman Albasa yana yin baya yana neman fin karfin talaka saboda tsadar taki.
Alhaji Musa ya ce, idan aka sami yin noman Albasa a ranin nan za ta yi sauki sai dai ya koka da cewa akwai sassa da make noman Albasa sosai a Kano da Gwamnati ta dakatar suna kira ga Gwamnati ta bada dama a cigaba da noma a wurin dan hakan zai taimaka sosai.
Alhaji Musa Karfi ya jaddada kira ga uwar kungiyar yan Albasa na kasa su rika kulada na kasa a kowane yanayi don bunkasa cigaban Albasa.