CRI Hausa" />

Ba A Taba Tayar Da Rikici Tsakanin Addinai Daban-Daban Ko Sau Daya Ba A Tarihin Kasar Sin

Kwamitin kare hakkin Bil Adama na MDD yana gudanar da taronsa karo na 43 a birnin Geneva, inda a jiya Talata an yi muhawara da wakilan musamman kan ’yancin bin addini, inda wakiliyar musamman ta kasar Sin kan batun kare hakkin Bil Adama Liu Hua ta nuna cewa, addinai daban-daban na zama tare cikin lumana, har ma kawo yanzu ba a taba tayar da rikici ko sau daya tsakanin addinai daban daban a kasar Sin ba tukuna.
Liu Hua ta ce, bisa tanade-tanaden tsarin mulkin kasar Sin, duk hukuma ko kungiya ko daidaikun mutane, ba su da ikon tilastawa mutane bi ko magance bin wani addini, sannan kuma an haramta nuna bambanci kan mutanen da suke bin wani addini, ko kuma wadanda ba su bin addini ba. Ta kara da cewa, a kasar Sin ana samun masu bin addinin Budda da na Taoism da kuma na Musulunci da na Katolika da sauransu, sannan kuma a kasar akwai kungiyoyin addinai fiye da 5500, har da kwalejojin koyon ilmin addinai kusan dari, da wuraren ibada sama da dubu 140. Har ila yau, Sin na da wuraren ibada na mata mabiya musulunci fiye da dari. Tana mai cewa, wannan ya nuna cewa, addinai daban-daban na zama tare cikin lumana a kasar Sin, babu rikici tsakaninsu. Matakin kuma ya bayyana al’adun kasar Sin na yin hakuri da juna tsakanin bangarori daban-daban, da kuma bayyana cewa, manufofin da gwamnatin Sin ke dauka kan addinai sun dace da yanayin da kasar ke ciki. (Mai Fassarawa: Amina Xu)

Exit mobile version