Daga Sagir Abubukar,
Alhaji Mustapha Saulawa daya daga cikin na hannun damar Gwamna Aminu Bello Masari kuma Shugaban Kungiyar “Masari Youth Vanguard” ya bayyana cewa jam’iyyar APC alheri ce ga daukacin al’ummar Jihar Katsina da ma kasa bakidaya. Saboda a cewarsa ba a taba yin jam’iyyar siyasa wadda talakkan da ke kasa-kasa ya san ana mulki irin APC ba.
Mustapha Wada ya bayyana haka ne a sakatariyar karamar hukumar Daura, a lokacin da yake wani rangadi da wayar da kan membobin kungiyar na su fito su amshi katin zama yan jam’iyyar da ake shirin yi nan gaba kadan.
Wada ya ci gaba da cewa a jihar Katsina ta ciri tuta, saboda a nan ne Shugaban Kasa Muhammadu Buhari ya fito kuma aka samu zunzurutun kuri’u na halak malak ba tare da yin magudi ba ko wata tarzoma ba. Kuma gwamnati na wani shiri na sama wa dimbin matasan jihar Katsina, domin za ta kirkiro hukumar KATROTA nan gaba kadan. Duk da ana ba matasan wani alawus, kuma bai taba tsinkewa ba kari ma za a yi nan gaba, wanda kuma ba su samu damar shiga kungiyar Masari Youth Banguard ba, su kara hakuri saura kiris su ma a shigar da su.
Darakta janar din ya kara da cewa “tun daga yau, ku fara shiga lungu da sakon domin ci gaba da wayar da kan al’umma muhimmancin yin katin zama dan jam’iyyar APC, domin nan jihar Shugaban Kasa Muhammadu Buhari ce, ana so ta mu tafi ta kowacce jiha yawa, ta hanyar wayar da kai ne kadai hakar mu za ta cinma ruwa. Mu zama tsintsiya madauri daya kar wani ya shigo ya ba mu gurguwar shawara.”