Connect with us

KASASHEN WAJE

Ba Abinda Trump Yake Sai Zubarda Mutumcin Amurka: Inji Iran

Published

on

Ministan harkokin wajen kasar Iran Muhammad Jawad Zarif ya ce a daidai lokacin da kasar Iran take ta kokarin samar wa da rikicin Syria mafita ta siyasa, shi kuwa shugaban kasar Amurka ba abinda ya sa a gaba sai zubar wa da kasar dan mutumcin ta da ya rage a idon duniya.

 

‘A daidai lokacin da kasashe Rasha, Turkiyya da Iran suke kokarin samun mafita ta siyasa ga rikicin na kasar Siriya, su kuma Amurkawa sun can suna ta wasa da hankalin kawayensu a duniya game da matsayar da za a cimma, shiyasa muka dau matakin daina tattaunawa da Amurka din.’ Inji Zarif

 

Kasashen uku sun cimma matsayar kawo karshen ‘yan ta’addan da suka samu mafaka a garin Idlib, Turkiyya kuwa ta bukaci a tsagaita wuta ne a garin na Idlib don a samu mafitar siyasa ga rikicin, amma Putin na Rasha da takwaranshi Rauhani na kasar Iran suna gani bai kamata a sassauta ma ‘yan ta’addan ba.

 

Garin na Idlib ne kadai ya yi saura a matsayin mafakar ‘yan ta’adda a duk fadin kasar Siriya sakamakon cin nasarar fatattakar ‘yan ta’addan da sojin kasar Siriya da taimakon kawayensu Rasha da Iran suka yi, duk da goyon bayan da kasashen yamma suke bai wa ‘yan ta’addan na Siriya.
Advertisement

labarai

%d bloggers like this: