Abba Ibrahim Wada" />

Ba Ciwo Ronaldo Ya Ji Ba’

Mai koyar da yan wasan kungiyar kwallon kafa ta Real Madrid, Zinedine Zidane ya bayyana cewa dan wasan kungiyar, Cristiano Ronaldo ba ciwo yaji ba kuma zai ci gaba da buga wasanninsa a kungiyar.

A ranar Lahadi ne dai dan wasan ya zura kwallo a ragar kungiyar Barcelona a daidai minti 15 da wasan da suka buga na hamayya sai dai a lokacin daya zura kwallon dan wasan baya na kungiyar Barcelona, Gerard Pikue ya dokeshi a kafa.

Zidane ya ce Ronaldo ba ciwo yaji ba kawai ya dan buge ne kuma hakan bazai hana dan wasan buga wasan karshe ba nacin kofin zakarun turai da zasu fafata da kungiyar Liberpool a ranar 26 ga wannan watan.

Yaci gaba da cewa likitocin kungiyar zasu duba ciwon da dan wasan yasamu kuma zasu gayawa kungiyar abinda ya kamata ta dauka akan Ronaldo amma kuma tabbas ba wani babban abu bane ya sami dan wasan.

Barcelona da Real Madrid dai sun buga wasan hamayyar ne a filin wasa na Nou Camp dake yankin Cataloniya wasan da Luis Suares da Messi suka ciwa Barcelona yayinda Ronaldo da Bale suka ciwa Real Madrid kwallayenta guda biyu sai dai tun a minti 43 ne aka bawa dan wasan baya na Barcelona Sergi Roberto jan kati.

A yanzu dai haka kungiyar Barcelona ta lashe kofin laliga kuma har yanzu babu kungiyar data samu nasara akanta yayinda ya rage saura wasanni 2 a kammala gasar.

Exit mobile version