Shahararran mai maganin gargajiyar nan Dakta Alhaji Abubakar Gailo ya bayyana cewa cibiyarsa ta GAILO TRADO MEDICAL CLINIC dake Passo, daura da Babban Asibitin Specialist a Gwagwalada, FCT Abuja (08034535235) sun shirya tsaf, domin ganin sun bada gudunmawar samar da lafiyar al’umma. Sannan kuma ya ce ba kamar yadda wasu ke cewa Cutar Sida (Kanjamau) kawai yake bada maganinta ba, a’a. Haqiqa Allah Ya bani iko ina bayar da magungunan cutuka da daman gaske, wadanda wasu ke jin cewa ba su da magani.
“Bayani ne wanda kuka saba ji da kuma gane wa idanunku cewa hatta cututuka gagararu wadanda duniya ke kururutawa, kuma har yanzu sun gaza shawo kansu. Musamman cutukan dake halaka mata masu juna biyu da kuma yara kanana Allah Ya bamu iko akan su.”
Ya ci gaba da cewa, “Babar damuwar da ake samu ga mata masu juna biyu wadanda yawansu ke mutuwa wajen haihuwa ko bayan sun haihu ko kuma wadanda ke yawan samun tabuwar kwakwalwa bayan sun haihu. To ina farin cikin sanar da ku cewa a shirye muke mu bada tamu gudunmawar domin samar wa al’umma sauki kuma aga zahiri.” In ji shi.
Dakta Gailo wanda ya bayyana haka a yayin ganawarsa da manema labarai a ofishinsa dake Gwagwalada Abuja, ya ce, “Muna muku albishir cewa idan har an bamu hadin kai, zamu iya kawar da wannan cuta da ma wasu da dama cikin yardar Allah. Wasu sun dauka cewa muna warkar da cutar Sida ce kawai, a’a, muna bada magungunan cutuka ma su hatsari ga rayuwar bil-Adama dake barazana ga mata da maza da suka hada da Cutar Sikila mai yawan halaka yara kanana da ma manyan baki daya.”
Sannan ya karkare da cewa, “Haka nan da Cutar Asma, Ciwon Suga, Hawan Jini, CutarBarkewar Jini (Hipertitis) Cutar Kashin Baya (Spinal Cord) wanda ke haddasa lalacewar mazakutar da namiji da sauransu.”