hunk" />

Ba Da Halastattun Kuri’u Ganduje Ya Ci Zabe Ba – Abba Gida-gida

Dan takarar kujerar gwamnan Jihar Kano a karkashin tutar jam’iyyar PDP, Abba Kabiru Yusuf, wanda a ka fi sani da Abba Gida-gida, ya bayyana cewa, gwamnan jihar mai ci, Injiniya Abdullahi Umar Ganduje, ba da halastattun kuri’u ya ci zaben jihar ba.

Dan takarar ya bayyana haka ne lokacin da a ka dawo zaman kotun koli a jiya Talata, domin sauraron bayanan karsge kan daukaka karar da ya yi, wacce ya shigar ya ke mai kalubalantar halascin zaben Gandujen a zaben da a ka gudanar ranar 9 ga Maris, 2019, wanda hukumar zabe mai zaman kanata, INEC, ta ayyana Dr. Ganduje a matsayin wanda ya lashe shi.

Abba Kabiru Yusuf ya kuma yi ikirarin cewa, kasantuwar shi ya lashe kuri’u mafiya yawa a zaben, shi ne dan takarar da ya cika sharadin da sashe na 179 na dokar zabe ya shardanta.

Da ya ke bayyana hujjojin daukaka karar da ya yi ta bakin Lauyansa, Adegboyega Awomolo (SAN), ya nemi kotun ta koli da ta yi watsi da hukuncin da kananan kotunan da su ke a karkashinta (Kotun sauraron kararrakin zabe da kotun daukaka kara), su ka zartar, inda su ka tabbatar da nasarar zaben Gwamna Abdullahi Umar Ganduje a matsayin Gwamnan na Jihar ta Kano.

Awomolo ya kafa hujja da cewa, babban Jami’in zaben daga hukumar zabe mai zaman kanta ta kasa (INEC) a Jihar ta Kano ya shelanta sakamakon zaben na ranar 9 ga watan na Maris a dukkanin kananan hukumomi guda 44 na Jihar har ma ya bayar da takardar fom mai lamba EC8D, wacce ta ke kunshe da tabbataccen sakamakon zaben a dukkanin kananan hukumomin Jihar guda 44, har sai daga baya ne a ka ce an soke sakamakon zaben a mazabu guda 207.

Ya kara kafa hujja da cewa, a wasu kararrakin masu kama da wannan, kotun kolin ta yanke shawara a kan wani jami’in zaben da ya soke sakamakon zaben wata karamar hukuma da cewa ya wuce gona da iri ne, domin haka soke zaben da ya yi bai halasta ba.

“Shelanta cewa wai zabe bai kammala ba a sabili da soke mazabu 297 shi ma wannan wuce gona ne da iri da shi jami’in zaben ya yi,” in ji Awomolo.

Amma Lauyoyin wadanda a ke kara, Ahmed Raji (SAN), Aled Izinyon (SAN) da Offiong Offiong (SAN), wadanda suke wakiltar Hkumar zabe ta INEC, Jam’iyyra APC da Gwamna Ganduje, bi da bi, sun nemi kotun kolin ce da ta yi watsi da daukaka karar Abba Kabiru Yusuf da kuma Jam’iyyar ta PDP.

Raji ya ja daga da cewa, sam babu wata shaida ta cewa babban Jami’in zaben ne ya soke kuri’un, amma abin da yake a rubuce dai shi ne cewa babban Jami’in zaben ya gaza tattara sakamakon zaben a wannan ranar.

“Don haka, Ina neman mai girma alkalin wannan kotun ya yi watsi da wannan daukaka karar, ya kuma nemi kotun ta koli da tabbatar da hukuncin da kananan kotunan da suke a karkashinta suka yanke a baya.”

Exit mobile version