Connect with us

DAGA BIRNIN SIN

Ba Da Hidima Da Kuma Dogaro Da Jama’a Su Ne Dabarun Da Sin Ta Dauka Wajen Yakar COVID-19

Published

on

A wani lokaci a baya an tabbatar da mutane dubu 13 da suka kamu da cutar COVID-19 a wata rana guda, amma a halin yanzu, babu sabon mutum da ya kamu da wannan cuta, kuma babu wanda yake cikin halin rai kwakwai mutu kwakwai a birnin Wuhan, abin da ke da babbar ma’ana sosai. Abin da ya bayyana cewa, bayan gwagwarmaya da duk al’ummar Sinawa suka yi, sun samu nasarar shawo kan wannan mummunar annoba.

Da wuya ne kasar Sin ta samu wannan ci gaba, al’ummar duniya na kokarin gano wane irin dabaru kasar Sin ta dauka, don cimma nasarar shawo kan wannan mummunar cutar cikin gajeren lokaci? A hakika dai, bada hidima ga jama’a da dogaro da jama’a su ne dabarun da Sin ta dauka wajen yakar COVID-19.

Saboda jam’iyyar JKS ta mayar da muradun jama’a a matsayin kolin, Sinawa da yawansa ya kai biliyan 1.4 sun hada kansu sun tinkari wannan kalubale tare. A wayar da ya yi da shugabannin kasashen waje, shugaban kasar Sin Xi Jinping sau da dama ne ya nanata cewa, jama’a suna bada karfi da kwarin gwiwa wajen yakar COVID-19, dukkansu jarumai ne. A karkashin jagorancin shugaba Xi Jinping, Sinawa sun kafa wani tsari mai inganci a duk kasar domin yaki da wannan cutar.

Hadin kai don tinkarar kalubale tare, ta wannan hanya kasar Sin ta cimma nasarar shawo kan cutar, kuma tana kokarin farfado da zaman rayuwa da gaggauta bunkasuwar tattalin arzikinta, Sin tana kuma da imanin cimma burinta na kafa al’umma mai matsakaicin wadata a wannan shekara. Bada hidima ga jama’a da kuma dogaro da jama’a, karfi ne mai inganci wajen ingiza bunkasuwar kasar Sin da kuma cimma muradunta. (Mai Fassarawa: Amina Xu)
Advertisement

labarai

%d bloggers like this: