Dr. Jamilu Yusuf Zarewa" />

Ba Da Kudin Kashewa, Ba Wajibi Ba Ne A Kan Miji!

Tambaya
Assalamualaikum malam, Dan Allah ga wata tambaya a taimaka mana da amsar ta, wata aminiyata ce take so a taimaka mata, ita dai ta kasance mijinta yana da hali sosai kuma kullum yana ma ta duk laluranta wadanda Allah ya daura mishi a kanshi, to amma ba ya daukan kudi haka kawai ya ba ta, to shi ne ita kuma sai ta yi ma mijin karyan cewa wasu masu neman taimako sun zo da lalura sun ce dan Allah ya taimaka musu, to idan ya bayar sai ta rike, ko kuma idan masu neman taimakon na gaskiya suka zo in ta fada mishi in ya ba ta se ta cire wani abu aciki ta ba su sauran, shi ne ta keso ta ji wannan kudin da ta ke ci, mene ne matsayin hakan?
Amsa
Wa’alaikumus Salam, In ta yi haka ta ci haramun, ta kuma yi Algus, Annabi S.A.W. yana cewa “Wanda ya yi Algus ba ya cikinmu” kamar yadda Muslim ya rawaito.
Allah da Manzonsa ba su wajabtawa miji ya bawa matarsa kudin kashewa ba, abin da aka wajabta masa shi ne Ci da ita da Shayar da ita, yi mata Sutura, da yi mata duk abin da rayuwarta ba za ta ta fi ba sai da shi gwargwadon halinsa, kamar yadda ayar suratu Addalak da hadisai ingantattu suka tabbatar.
Bada EDtra kudi ba wajibi ba ne, tare da cewa kyautatawa iyali abu ne mai kyau, Annabi (S.A.W) yana cewa “Mafi alkairinku shi ne Wanda ya fi kyautatawa iyalansa”, wannan sai yake nuna cewa: Mijin da yake bada kudin kashewa ya fi wanda ba ya bayarwa.
Babu bukatar ta bi ta hanyar Algus, idan ta lallabi mijinta, ta yi masa biyayya, za ta same shi a hannunta.
Allah ne mafi sani

Idan Masabuki Ya Riski Liman A Raka’a Ta Biyar, Ya Samu Jam’i?
Tambaya:
Assalamu alaikum, Akramakallahu idan liman ya yi kuskuren kara raka’a daya, masbukin da aka tsere ma da raka’a daya za ta ishe shi idan Anyi ba’adiyya tare da shi?
Amsa:
Wa’alaikum assalam, Allah ya taimaki shehinmu, malamai sun yi sabani akan wannan mas’alar zuwa zantuka biyu:
Akwai wadanda suke ganin za ta isar masa. Sai dai abin da na fi nutsuwa da shi a raina shi ne ba za ta isar masa, saboda mamu sallarsa tana like da ta liman ne, shi kuma liman ya zo da raka’ar a kuskure, wannan ya sa kamar yadda ba za ta amfani liman ba, haka ba za ta amfani mamu ba, wannan ita ce fatawar Sheik Ibnu Bazz da Sheik Abdulmuhsin Al-abbad.
Yana daga cikin ka’idojin sharia: Mabiyi ba ya kebanta da hukunci.
Allah ne mafi sani.

Hukuncin Tsotson Farjin Mace Yayin Saduwa
Tambaya:
Assalamu alaikum, M. Na kasance ina tsotsan azzakarin mijina, shi kuma yana wasa da gabana da harshensa kafin mu sadu, ina matsayin haka a addinin musulunci.
Amsa:
To ‘yar’uwa hakan ya halatta, ba matsala a sharian ce, saboda an rawaito halaccin haka, daga magabata, daga cikinsu akwai Imamu Malik, saidai ya wajaba a tabbatar an tsaftace wurin musamman farjin mata, saboda a bude yake, sannan kuma wuri ne da ake yin haila, ake kuma zuba maniyyi, ga shi kuma yana kusa da wajan yin bahaya, wasu masana likitanci suna bada shawarar cewa: a dinga wanke wurin da gishiri kafin a tsotsa, saboda neman kariya.
Allah madaukakin sarki a cikin suratul Bakara aya ta: 223, ya kwatanta mace ga mijinta da gona, wannan sai ya nuna dukkan bangarorin jikinta ya halatta a ji dadi da su, in ban da cikin dubura wacce nassi ya togace.
Duba: Mawahibul-jalil sharhin Muktasarul Khalil 3\406.
Allah ne mafi sani.

Matata Ta Haihu, Bayan Mun Yi Aure Da Wata Biyar!
Tambaya:
Assalamu alaikum, Malam don Allah ina hukuncin macen da ta yi aure bayan wata biyar (5) ta haihu, shi kuma mijin yace ‘yar ba nashi ba ne, yarinyan matsayin me za’a sanya ta? kuma ya mastayin wannan aure nasu?
Amsa:
Wa’alaikumus salam, Idan mutum ya auri mace ta haihu a wata biyar, to ba dansa ba ne, saboda ciki ba a haihuwarsa a kasa da wata shida, kamar yadda Sayyadina Ali, Allah ya kara yarda a gare shi, ya fahimta a aya ta: 14 a suratul Lukman da aya ta: 15 a suratul Ahkaf, kuma Sahabbai suka yi masa muwafaka akan haka.
Don haka wannan yarinyar dole a nemo babanta na asali, wanda ya fara saduwa da mahaifiyarta tun kafin ta yi aure. Auransu ya inganta, a wajan Malaman Hanafiyya, sannan ba shi da laifin saduwar da ya yi da ita tana da ciki, in har bai sani ba.
Allah ne mafi Sani.

Ya Yaga Takardar Sakin Kafin Matarsa Ta Gani…
Tambaya:
Assalamu alaikum. Malam shin idan mutum ya rubuta takardar saki ya aje, sai wani ya gani shin matar ta shi tasaku?
Amsa:
Wa alaikum assalam To malam matukar ya rubuta da niyya kuma yana cikin hayyacinsa ba takura masa aka yi ba, to ta saku, saboda fadin Annabi tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi : “Allah ya yafewa al’umata abin da ta riya a zuciyarta, mutukar bata fada ba, ko ta aikata” ka ga kuma rubutu aiki ne.
Kuma Annabi tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi ya kasance yana zartar da abubuwa da yawa ta hanyar rubutu, ka ga ya zama hujja kenan.
Wannan shi ne mazahar Abu-hanifa da Malik kuma shi ne zancen Shafi’i mafi inganci. Duba Al-mugni : 7\486
Allah ne mafi sani.

Hukuncin Hulda Da Yahudu Da Nasara
Tambaya:
Assalaamu alaikum. Allah ya karawa Dakta lafiya, don Allah ina son amsar tambayoyin nan tare da hujja don gamsar da abokan karatuna.
1. Minene matsayin amsa gayyatar Kiristoci zuwa cikin coci don wani taro da suke yi na graduation (bikin yaye dalibai) ko makamancin haka amma a cikin coci?
2. Minene matsayin shiga coci din karan-kansa?
3. Menene matsayin fara yiwa wanda ba musulmi ba sallama ?
Allah ya karawa mallam ikhlasi da ilimi mai amfani
Amsa:
Wa alaikum assalam, Annabi (SAW) ya hana fara yiwa Kirista sallama kamar yadda ya zo a hadisin Tirmizi. Ya halatta Musulmi ya yi hulda da Kirista ya kuma kyautata masa in har ana zaune lafiya , kamar yadda aya ta (8) a suratul Mumtahanah ta tabbatar da hakan, sannan zai iya cin yankansa kamar yadda aya ta (5) a suratul Ma’idah ta yi bayanin hakan.
Annabi (SAW) ya rasu silkensa na yaki yana wajan Bayahude, saboda ya amshi abincin da za’a ci a gidansa, sannan da aka bude Khaibar ya bar gonakin musulmai a wajan Yadudawa sun rinka nomawa suna bawa musulmai wani kaso kamar yadda Bukhari ya rawaito a Sahihinsa Nasaran Najran sun zo wajan Annabi (SAW) ya sauke su a Masallaci, sannan ya zo a Musannaf a lamba ta: (4871) cewa: “Sahabin manzon Allah Abu-Musa Al’ash’ary ya taba yin sallah a wata coci da ake cewa NAHYA a Damshk lokacin da bai samu masallacin ba. Tarurrukan Kristoci ba sa rabuwa da kade-kade da raye-raye da cakuduwa tsakanin maza da mata, ga kuma manyan hotuna a like a bango, wannan yasa rashin halartar taronsu shi ne daidai, saboda gujewa keta iyakokin Allah.
Allah ne mafi sani.

Idan Na Kusanci Mijina, Yana Kyamata Ta, Mece Ce Mafita?
Tambaya:
Assalamu alaikum Malam ni ce ina da miji a duk lokacin da zan zo kusa da shi sai ya ce min barci yake ji, ai shari’a ta hana na dame shi, a haka za mu yi kusan wata ba abin da ya shiga tsakanina da shi, Allah taimaki Malam mece ce mafita?
Amsa
Wa’alaikum assalam, ki tambaye shi dalılin da yasa yake yin hakan, zai iya yiwuwa kin bata masa rai ko kuma akwai Wata matsalar, amma ta hanyar tambaya ko shigar magabata lamura za su iya fitowa fili.
Sharia ba ta halattawa namiji ya ki saduwa da matarsa ba da gangan, saboda nau’i ne na cutarwa, yana daga cikin manufofin aure katange ma’aurata daga kallon haram.
Allah ne mafi sani.

Exit mobile version