Connect with us

KASUWANCI

Ba Da Mugun Nufi Shugaba Buhari Ya Garkame Iyakoki Ba – Ministar Kudi

Published

on

Ministar kudi da tsaretsare, Uwargida Zainab Ahmed Shamsuna, ta sanar da cewa, Shugaban kasa Muhammadu Buhari ya nuna kun aincewa da rufe iyakokin Nijeriya da makwabtanta saboda ya na sane da matsanancin halin da tattalin arzikin kasashen zai shiga, inda ta kara da cewa, tunda farko bai amince da matakin ba, don haka ba da mugun a karshe ya amince da hakan ba.
Zainab Ahmad ta sanar da hakan a ranar Lahadin da ta wuce a yayin da ta ke ganawa da manema labarai a babban birnin Washington DC da ke kasar Amurka, inda ministar ta ce an dauki matakin ne don gyara alakar Nijeriya da makwabtanta. A cewar Hajiya Zainab, bankin bayar da lamuni na duniya, IMF na goyon bayan wannan mataki, saboda ya na sane da cewa ba wai an dauki matakin ba ne da nufin kuntata wa kasashen, sai dai kawai domin yin gyara ne ga tsarin alakar kasuwanci tsakanin kasashen.
Ta bayyana cewa, an yi ta kokarin daidaitawa da sauran qasashen, amma hakan ya faskara.
“Mun san akwai matsi ga tattalin arzikin qasashensu, saboda wannan  mataki, amma abinda mu ke so qasashen nan su gane shi ne cewa za su iya turo ma na kayayyaki, amma fa sai ta tashoshin jiragen ruwanmu,” in ji ta.
Ta jaddada cewa, dole ne kayan su shigo Nijeriya cikin sunduqai domin bai wa hukumar kwastom ta qasar damar bincikar su, sa’annan kuma su dinga biyan duk harajin da ya kamata, amma ba abinda su ke yi ba kenan, inda ta qara da cewa, “sai su bari a buxe sunduqai a qasashensu, sa’annan a shigo da kayan zuwa qasar nan ta varauniyar hanya.”
Ministar ta ce, Nijeriya ba za ta buxe iyakokinta ba har sai qasashen sun amince da bin tsarin cinikayya da kasuwanci na qungiyar qasashen yammacin Afirka, sa’annan ta qara da cewa har yanzu a na cigaba da tattaunawa a kan hakan.
Advertisement

labarai