Ba Dimukradiyya Ake Yi Ba Yanzu A Nijeriya -Ghali Na’Abba

Dimukradiyya

Daga Abdullahi Muhammad Sheka,

Tsohon kakakin majalisar wakilan Nijeriya Ghali Umar Na’Abba, ya zargi gwamnoni da cewa su ne matsalar Nijeriya da ke kassara dimukradiyya a kasar nan.

A hirarsa da BBC ya ce gwamnoni ne suka haddasa duk wani halin da yanzu Nijeriya ta tsinci kanta a ciki.

 

Duk da ana ganin dimokradiyya a Nijeriya wuyanta ya isa yanka, amma yana ganin da sauran aiki idan aka yi la’akari da manyan matsalolin da suka dabaibaye dimokradiyyar Nijeriya, a cewarsa saboda rashin dimukradiyyar cikin jam’iyya da siyasar uban gida da kuma siyasar bangaranci.

 

Na’Abba wanda aka zaba dan majalisar tarayya a jam’iyyar PDP kafin ya koma APC, ya ce yanzu dukkanin manyan jam’iyyun babu wadda take bin tsarin dimokradiyya.

 

“Yanzu ba ni da jam’iyya saboda ba dimokradiyya ake ba, kuma ba a yin zabe. “Na janye daga takarar sanata saboda an bukaci dole sai na bayar da kudi a tsayar da ni,” in ji shi.

 

Ya shaida wa BBC cewa suna shirin kafa sabuwar jam’iyyarsu kuma zai nemi takarar kujerar sanata.

 

Exit mobile version