Khalid Idris Doya" />

Ba Don Muradin Kanmu Muke Adawa Da Buhari Ba – Yakubu Dogara

Wakilinmu ya nakalto Kakakin Majalisar Tarayya, Honorabul Yakubu Dogara na fayyace asalin dalilansu da muradinsu da ya sanya suke adawa da shugaban kasa Muhammau Buhari, inda Dogara ke cewa, ba wai suna adawa da Buhari don basu sonshi a kashin kansu ba ne, illa kawai domin tabbatar da samar da Nijeriya makoma mai kyau.
LEADERSHIP Ayau ta jiyo wadannan kalaman na Dogara ne a wajen kaddamar da yakin neman zaben dan takarar gwamna a jam’iyyar PDP da aka gudanar a ranar Asabar din da ta gabata a garin Bununu da ke karamar hukumar Tafawa Balewa a cikin garin Bauchi.
Yakubu Dogara ya shaida cewar Nijeriya tana cikin wani mummunar yanayin da akwai gayar bukatar a tashi tsaye domin nema mata mafita, ya shaida cewar kashe-kashe sun kara hauhawa a gwamnatin Buhari, inda ya shaida cewar yanzu haka yunwa da fatara su ma dukka sun addabi Nijeriya don haka ne suka fito da Atiku Abubakar domin ya kawo gyara.
A ta bakin Kakakin Majalisar Tarayya; “Ina son na tabbatar wa illahin jama’an kasa cewar a cikinmu din nan gaba dayanmu da kuka gani, har shi Kauran Bauchi babu waninmu da yake gaba da shugaban kasa Muhammadu Buhari ko kuma ba mu sonshi, babu wani kuma da za a fada masa wannan.
“Mu bawai mun tsani Buhari ba ne; a’a, gaskiyar magana ita ce, muna ganin makomar da ‘yan uwanmu, al’ummarmu, talakan Nijeriya ke fuskanta ne, musamman ma mu a yankinmu na arewa maso gabas, mun ga yadda rikicin Boko Haram ya zama mana barazanar da muddin ba a tsayar da ita ba, yadda muke jin ana gudu a Borno, wata rana daga Bununu nan za a gudu, amma Allah ya kiyaye mana.
“Mune Allah ya bamu hukuncin kada kuri’a da za mu kashe wannan rikicin na Boko Haram din. Muna ji muna gani talauci ya yi mana kanta, muna ganin kashe-kashe da shekar da jini da ake zubarwa, wannan lamarin ya ishemu mun gani da shi,” Inji Yakubu Dogara
Dogaya ya ci gaba da jawabinsa da cewa, “akwai wasu daga arewa masu kaunar Buhari sosai, wajajen kwana hudu da suka wuce bayan sun ga wannan hirar da aka yi da shi a talabishin, duk da son da suke wa Buhari domin da baka isa ba ka ce wa Buhari cas ba, don ko da na koma cikin PDP sune suka tayar min da hankali sosai da gaske; amma bayan kallon wannan hirar da aka yi da Buhari a talabishin sai suka bugu min waya suka ce ‘Speaker amma da kun cucemu, amma yanzu Allah ya bude mana ido mun ga abun da ko kun boye mana ne domin ganin girma, amma yanzu an yi walkiya mun ga zahiri; mun maka alkawarin ba za mu zabi Buhari ba, abun da ya damemu shine makomar talaka’.
Kakakin ya shaida cewar, matsalarsu dai bai wuce ina dan Nijeriya zai samu kyakkyawar rayuwa a nan gaba ba; “Mu matsalar mu ita ce waye zai taimaki talakawa, waye zai dauki matasanmu aikin yi? Waye zai zo ya yaki jahilci? Waye zai zo yaki yunwa da fatara? Waye zai kawo mana karshen kisan da ake yi wa jama’a ko yaushe? Wannan dalilin ne ya sanya muka dauko muku Atiku Abubakar muka ce a zabeshi domin makomar Nijeriya ta yi kyau,” Inji Dogara
Honorabul ya kara da cewa; Nijeriya a halin yanzu tana neman hadin kai ne domin shawo kan matsalolin da suke akwai, don haka ne ya ma jinjina wa wadanda suka dawo daga jam’iyyar APC da wasu jam’iyyu zuwa cikin PDP.

Exit mobile version