Connect with us

MANYAN LABARAI

Ba Gudu Ba Ja Da Baya Kan Ikon Shugaban Kasa – Malami

Published

on

A ranar Talatar nan ne Gwamnatin Tarayya ta nanata cewa, sam ba gudu ba ja da baya a kan dokar nan mai lamba 10, wacce ta tabbatar da ikon Shugaban Kasa Muhammadu Buhari na ’yancin cin gashin kai ga ’yan majalisun jihohi da sashen shari’a na Tarayyar Nijeriya.

A maimakon sabanin hakan, babban Lauyan Gwamnatin Tarayya kuma Ministan Shari’a, Malam  Abubakar Malami (SAN), ya ce, kan hakan wannan gwamnatin za ta yi aiki tare da gwamnonin jihohi wajen tsara yadda za a tafiyar da wannan dokar. Ya ce, kwamitin da za a kafa, domin tsara yadda za a aiwatar da dokar, zai amshi shawarwari masu amfani daga kungiyar gwamnonin kasar da sauran masu ruwa da tsaki.

Ya ce, Gwamnatin Tarayya ta ji dadin yadda su kansu gwamnonin jihohin su ka aminta da halascin da tsarin mulki ya bai wa ’yan majalisun jihohi da kuma sashen na shari’a. Ya ce, gwamnonin sun aminta da cewa wannan dokar mai lamba 10 ne, domin karfafa tafarkin dimukuradiyya tun daga tushensa da kuma tabbatar da aiwatar da rabe-raben iko a kasar.

Malami ya yi wannan karin hasken ne a cikin wata sanarwa da ya fitar a Abuja ta hannun mai taimaka ma sa na musamman a kan harkokin manema labarai da hulda da jama’a, Dakta Umar Jibrilu Gwandu.

Da kama fayyacewar ya zama wajibi ne, domin kore ikirarin da gwamnonin ke yi na cewa wai Shugaban Kasa Muhammadu Buhari ya dakatar da yin aiki da wannan dokar ta aiwatar da ‘yancin cin gashin kan. Amma sai Malami ya ce, “Gwamnatin Tarayya ta na dai sauraron shawarwari ne daga gwamnonin jihohin da kuma masu ruwa da tsaki.

Ministan Shari’ar ya ce, bayar da ’yancin cin gashin kai ga majalisun jihohin da kuma sashen na shari’a wani abu ne da sassauci a kansa.

Ya ce, “kara tabbatar da dalilai na tsarin mulki a kan dokar bayar da ‘yancin cin gashin kan ga majalisun jihohi da kuma sashen na shari’a ya na nan a cikin sashe na 121 (3) na tsarin mulkin Nijeriya na shekarar 1999, wanda shi ne ya wajabta kafa ita wannan dokar mai lamba 0010.”

Ya ce, “Babban dalilin kafa wannan dokar shi ne tabbatar da ana aiwatar da bayar da ‘yancin gashin kan.”

Jim kadan bayan ganawarsu da shugaban kasa a ranar Litinin, shugaban kungiyar gwamnonin, Dakta Kayode Fayemi, ya fada cewa: “A bayan da shugaban kasan ya saurari duk damuwar da gwamnonin suke da ita a kan halascin da tsarin mulkin ya bayar a kan ikon kafa ita wannan dokar ta shugaban kasa, sai shugaban kasa Muhammadu Buhari, ya amince da a jinkirta aiwatar da abin da dokar ta tanada.

“Mun turo wakilanmu ne daga kungiyar gwamnonin zuwa fadar ta shugaban kasa domin su tattauna a kan wasu mahimman batutuwa da suka shafi kasa, sai shugaban kasan ya ce mu je mu tattauna da Ministan shari’a, shugaban ma’aikata na fadarsa da kuma Ministar kudi da tsare-tsare da kasafin kudi a kan batutuwan.

“Wannan magana ce wacce ta dauki hankulan da yawanku manema labarai da ma mutane da yawa a sassan kasar nan, magana ce a kan bayar da ‘yancin cin gashin kai ga majalisun Jihohi da kuma sashen shari’a, mun kuma zauna da shugaban kasa a kan batun kafin yanzun, shugaban kasan kuma ya yi farin ciki sosai da ganin cewa a matsayinmu na gwamnonin kasar nan 36 duk kanmu a hade yake wajen amincewa da halascin bayar da ‘yancin cin gashin kan a tsarin mulkin kasar nan, dukkanmu gwamnonin kasar nan 36 muna goyan bayan bayar da ‘yancin cin gashin kan ga majalisun Jihohi da sashen shari’a, wannan kuma shi ne matsayarmu.

“To a ina matsalar take? Matsalar tana kan hanyar da tsarin mulkin ya shimfida ce wajen aiwatar da dokar shugaban kasan, shugaban kasan kuma yana da halin kirkin fahimtar cewa, shikenan, a bisa damuwar da kuke nunawa a kan hakan, za mu jinkirta aiwatar da abin da dokar ta tanada mu ba ku lokaci domin ku zauna da babban Lauyan gwamnatin tarayya da Ministar kudi domin tsara hanyar da ya kamata a bi wajen aiwatar da dokar.

Ya ce gwamnonin kuma suna kan tattauanwa da shugabannin majalisun Jihohin kasar nan domin tsara hanya mafi sauki wajen warware matsalar.

Ya kara da cewa, “to maganar dai ita ce, mu na ta tattaunawa da shugabannin majalisun kasar nan. Mataimakin shugaban kungiyar gwamnonin kasar, an kuma nada Gwamna Tambuwal na Jihar Sakkwato, domin ya jagoranci tawagar musamman na wasu gwamnonin Jihohi wadanda suke da kwarewa a kan sha’anin ayyukan majalisa ta Jiha ko dai sun taba zama a majalisar wakilai ta kasa, ko kuma sun taba shugabantar wata majalisar Jiha, ko kuma sun taba zama a majalisar Dattawa, to wannan tawagar kwamitin ne yake ta yin zama da shugabannin majalisun Jihohin domin tsara hanyar da ya kamata a bi wajen aiwatar da ita wannan dokar, muna kuma da tabbacin wannan zaman na su zai samar da hanya mafi sauki wajen warware matsalar ba tare da an shiga kotu ba.”
Advertisement

labarai