Connect with us

TATTALIN ARZIKI

Ba Gudu Ba Ja Da Baya Wajen kayyade Farashin Mai, Cewar PPPRA 

Published

on

Hukumar da ke kula da farashin mai a Nijeriya (PPPRA) ta dage a kan za ta ci gaba da kayyade farashin mai duk da ‘yan kasuwan mai sun bukaci ta cire hannunta daga cikin farashin mai. Haka kuma ta bayyana cewa, a yanzu za ta dunga tuntubar ma’aikatar albarkatun mai da ofishin alkalin-alkalai na tarayya kafin da kayyade farashin mai.

Shugaban hukumar PPPRA, Abdulkadir Saidu, shi ya bayyana hakan lokacin yake amsa tambayoyi a kan farashin mai wanda hukumar ta rage a ranar 19 ga water Maris ta shekarar 2020.

Tun lokacin da aka bayyana sabon farashin mai, ‘yan kasuwan mai suka bukaci hukumar ta cire hannunta daga cikin kayyade farashin mai.

Da yake mayar da martani a kan wannan bukata, Saidu ya bukaci mabambantar fannonin tattalin arziki su fahimci ka’idojin rage farashin mai a cikin wannan kasa.

Ya ce, “babban bankin Nijeriya shi ke kulawa da harkokin bankuna da sauran hukumomin da ke gudanar da harkokin kudade, haka ma hukumar sadarwa ta Nijeriya ita ce mai alhakkin kulawa da harkokin sadarwa, haka ma lamarin yake a bangaren albarkatun man fetur.

“Daga karshe, hukumar kula da farashin mai ba wai tana gabatar da ka’idojin saka farashin mai ba ne kawai da nufin kare maradun masu amfani da mai ba ne.

“Yana da matukar mahimmanci mu bayyana cewa, babu wani abu da ake kayyadewa a Duniya ba tare da kulawa ba ko kuma saka ido a kan shi.”

Saidu ya ci gaba da bayyana cewa, tsarin kasuwa ita ke kayyade farashin kowani irin abu, kai mu saka rashin yadda ga bangaren gwamnati da ke kare ‘yan kasanta.

A kan bukatar gyara tsarin kayyade farashin man a hukumarce, ya bayyana cewa, doka ce ta bayyawa hukumar damar gudanar da tsarin kayyade farashin man.

“Bisa wannan lamari, ka’idojin sake tsarin kayyade farashin mai an riga an kammala shi a cikin dokokin gudanar da harkokin mai, ya rage ga masu gudanar da harkan su bi dola sau-da-kafa,” in ji Saidu.

Shugaban hukumar PPPRA ya kara da cewa, canjin kayyade farashin man yana karkashin doka. Ya ce, babban matsalar da ake samu wajen canja farashin man ya hada da rake kasuwan man wanda zai iya sa farashin man ya karu.
Advertisement

labarai