Daga Khalid Idris Doya
Antoni Janar (AGF) kuma Ministan Shari’a a Nijeriya, Justice Abubakar Malami, ya yi fatali da ikirarin Babbar Alkalin jihar Ondo (CJ), Alkali Oluwatoyin Akeredole, da ta ce yana aikin hadaka da gwamnan jihar Rotimi Akeredolu da wasu domin ganin an cireta daga ofishinta.
Mai Shari’a Akeredolu ta yi zargin ne a wani karar da ta shigar a wani Babban kotun tarayya da ke Abuja inda ta shigar da gwamnan da wasu cikin kararta mai lamba FHC/ABJ/CS/2016/2021.
Wadanda take kara sun hada da Ministan Shari’a, gwamnan Ondo, Antoni Janar na jihar Ondo, Majalisar Dokokin jihar Ondo da Shugaban ‘yan sandan kasa (IGP).
Mai Shari’a Akeredole ta yi zargin cewa da gwamnan jihar, Kwamishinan Shari’a na jihar Ondo da Majalisar jihar sun sha alwashin aiwatar da shiryensu na tsigeta ne bisa dogaro da zargi da wani makusancinta Olupelumi Fagboyegun da ke zarginta (CJ) a wani bidiyon da aka yada a kafafen Sadarwar zamani da ke cewa an tsareshi shekaru uku bisa rashin jituwar da ya shafi kadarorin zuri’arsu.
Har-ila-yau, CJ din ta kuma zargi Ministan Shari’a da shiga cikin lamarin domin ganin an tsigeta duk kuwa da cewa ba haka doka ya tanadar a yi na bincikenta ba.
Ta na mai cewa dukkanin wadanda shigar kotun suna kokarin cireta daga ofishinta a matsayin Babbar Alkalin jihar Ondo ta haramtacciyar hanya, don haka ne ta zo kotu domin dakatar da su daga daukan kowace irin mataki har sai an kammala sauran Shari’ar da ta shigar.
Sai dai a martanin da ofishin Ministan Shari’a ya fitar, ya sanya kafa ya shure zarge-zargen CJ din Ondo bisa cewa babu kamshin gaskiya kan batun.
A bisa haka ne ofishin nasa ya roki kotun da ta yi matsi da bukatar mai shigar da karar.
Alkaleri kotun tarayyar Justice Inyang Ekwo ya umarci gwamnan Ondo da sauran wadanda ake kara da su dakatar da daukan kowace irin mataki har zuwa sauraran kowace bangare.