Leadership News Hausa
No Result
View All Result
  • LABARAI
  • WASANNI
  • RAHOTANNI
  • SIYASA
  • KASUWANCI
  • ADABI
  • RA’AYINMU
  • TATTAUNAWA
  • BIDIYO
  • MAKALAR YAU
  • LABARAI
  • WASANNI
  • RAHOTANNI
  • SIYASA
  • KASUWANCI
  • ADABI
  • RA’AYINMU
  • TATTAUNAWA
  • BIDIYO
  • MAKALAR YAU
No Result
View All Result
Leadership News Hausa
No Result
View All Result

Ba Hari A Ka Kai Fadar Shugaban Kasa Ba – Garba Shehu

by
2 years ago
in LABARAI
2 min read
Kashe-Kashe A Katsina: Gwamnatin Tarayya Tana Zargin Sarakuna Da Sa Hannu
WhatsAppShare on FacebookShare on TwitterShare on Telegram
ADVERTISEMENT

Fadar shugaban kasa ta yi magana a kan harbe-harben bindigar da wani jami’in tsaro da ke gadin uwargidan shugaban kasa, Aisha Buhari, ya yi a Billa. A ranar Juma’a ne rahotanni suka bayyana cewa wasu jami’an tsaro, a karkashin umarnin Aisha Buhari, sun tunkari Sabiu Yusuf, hadimin shugaban kasa, Muhammadu Buhari.

Rundunar ‘yan sanda ta kama wasu hadiman Aisha Buhari sakamakon harbe – harben da aka yi a fadar shugaban kasar. Sai dai, Aisha Buhari ta bukaci babban sifeton rundunar ‘yan sanda (IGP), Mohammed Adamu, ya saki jami’an tsaron da ke bata kariya. Da farko dai fadar shugaban kasa ta yi gum a kan faruwar lamarin tare da kin bayyana takamaiman halin da ake ciki dangane da wannan batu.

Amma, a cikin wani jawabi da kakakin shugaban kasa, Garba Shehu, ya fitar a jiya Lahadi, ya ce shugaba Buhari ya bayar da umarni a gudanar da bincike a kan lamarin. “Fadar shugaban kasa ta yaba da yadda jama’a suka nuna damuwarsu a kan hatsaniyar da ta kai ga ‘yan sanda sun kama wasu mazauna fadar shugaban kasa.

Labarai Masu Nasaba

Mai Yuwa A Gaza Kawo Karshen Yaki Da Yunwa A Nijeriya Har Zuwa 2025 —Mata Manoma

Sojoji Sun Kashe 2 Tare Da Tarwatsa Sansanin Bayar Da Horo Na IPOB A Jihar Imo

“Mu na ba wa jama’a tabbacin cewa shugaban kasa, Muhammadu Buhari, ba ya fuskantar wata barazana daga cututtuka ko kuma daga jami’in tsaron da ake gudanar da bicike a kansa.

ADVERTISEMENT

“Lamarin ya faru ne a wajen gidan da shugaba kasa ya ke zaune. Ma su tsaron lafiyar shugaban kasa kwararru ne da aka bawa horo a kan sarrafa makamai da kuma bayar da kariya a yayin da basa dauke da makamai. “Shugaban kasa ya yi aiki da tsarin doka ta hanyar bayar da umarnin gudanar da cikakken bincike a kan faruwar lamarin. “Bai kamata saboda samun karamin sabani ‘yan adawa suke kafa hujja a kan cewa an kai wa shugaban kasa hari ba. “A wannan karo, kamar ko da yaushe, shugaban kasa ya ce a bari doka ta yi aikinta,” a cewar Garba Shehu.

Like this:

Like Loading...
SendShareTweetShare
Previous Post

Edo 2020: Gwamnonin APC Za Su Gana Da Buhari

Next Post

’Yan Bindiga Sun Halaka ‘Yan Sanda Biyu A Neja

Labarai Masu Nasaba

Mai Yuwa A Gaza Kawo Karshen Yaki Da Yunwa A Nijeriya Har Zuwa 2025 —Mata Manoma

Mai Yuwa A Gaza Kawo Karshen Yaki Da Yunwa A Nijeriya Har Zuwa 2025 —Mata Manoma

by Abubakar Abba
6 hours ago
0

...

Sojoji Sun Kashe 2 Tare Da Tarwatsa Sansanin Bayar Da Horo Na IPOB A Jihar Imo

Sojoji Sun Kashe 2 Tare Da Tarwatsa Sansanin Bayar Da Horo Na IPOB A Jihar Imo

by Abubakar Abba
7 hours ago
0

...

CAN Ta Shirya Zanga-Zangar Yin Allah Wadai Da Kisan Deborah A Duk Jihohin Nijeriya

Batanci: CAN Ta Janye Gabatar Da Zanga-Zangar Da Ta Shirya Kan Kisan Deborah

by Leadership Hausa
11 hours ago
0

...

‘Yan Bindiga Sun Fille Kan Wani Dan Majalisa A Jihar Anambra

‘Yan Bindiga Sun Fille Kan Wani Dan Majalisa A Jihar Anambra

by Abubakar Abba
12 hours ago
0

...

Next Post
Masu Garkuwa Da Sarkin Ikulu Sun Nemi Fansar Milyan 100

’Yan Bindiga Sun Halaka 'Yan Sanda Biyu A Neja

Domin bayar da talla ko neman ƙarin bayani a tuntuɓe mu a: +2348039216372

  • LABARAI
  • WASANNI
  • RAHOTANNI
  • SIYASA
  • KASUWANCI
  • ADABI
  • RA’AYINMU
  • TATTAUNAWA
  • BIDIYO
  • MAKALAR YAU
Advertise with us | English Edition | Fashion Magazine | Business News

© 2022 Leadership Media Group .

No Result
View All Result
  • LABARAI
  • WASANNI
  • RAHOTANNI
  • SIYASA
  • KASUWANCI
  • ADABI
  • RA’AYINMU
  • TATTAUNAWA
  • BIDIYO
  • MAKALAR YAU

© 2022 Leadership Media Group .

%d bloggers like this: